Sashe 22
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
matattakalar bene na biyu ta hango Zayn ta cikin wani mudubi da akayi kwalliya da shi . Fasa hawan tayi ta koma wajen sa da sauri tana dariya. "Zayn Adams...." "Na'am Ahlam... Ya kike?" "Lapia kalau ... Shine baka mun magana ba? Ba dan na hangoka ba da shikenan ba zaka mun magana ba... Uhm?" Ta dora hannunta akan nasa tana murzawa. Ya janye da sauri yana goge hannun nasa da tissue paper. Murmushi tayi me hade da fari. "Baka ce komai ba ... Zayn." "Ahlaam. Nagaji ne. I'm exhausted beyond your expectation... Please." "Nayi lefi ne? Nace nayi lefi saboda nazo wajen ka?" Ya girgiza kai ahankali . Hade da sauke nannauyar ajiyar zuciya. Waheedah na jiyo dik abubuwan da suke cewa. Da sauri ta mike zata haye dakin da akace yana hanyar bene. "Zo nan Waheedah...." "Wa...Heee.. Dah. ! " Ya furta kasan maqoshi yadda shi kadai ya jiyo abunda ya fada. Ya na mai satar kallonta ta gefen idanu. "Ga ni Aunty....." "Ahh ... Kicemun Yaya dai. Sis Ahlam ko Yaya Ahlam, Kinji yar kanwata ? " Waheedah ta daga mata kai alamun toh. Kafin tace, "Tohm Insha Allah.." "Yauwa! Good girl... Kalle mu muna kama da shi ko bama yi?" Waheedah ta daga idanunta a hankali. Hade da gyara zaman gilashin idanunta. Ta sauke kallonta akan Ahlam kafin ta sake juyawa ta kallo Zayn. Da sauri tace, "Kuna yi..." "Jayyid.. Kaji ko itama tace muna kama. ?" Bai ce komai ba. Sai ma janyo tissue da yayi ya goge bakin sa. "Hubba bubba. Tace muna kama... Say something pls " "Muna yi..." Ya fada badan ya so ba. Waheedah dai na tsaye a akansu. Tana lankwasa yatsun hannuwan ta. "Shikenan dear sis .. . Mungode, Hubby na ne." Ahlam ta fada wa Waheedah tana murmushi. Waheedan ta gyada kai kawai itama tana dan murmushin. Ashe ma miji da matane amman yake shareta? Lalle bashida mutunci. Kuma da alama yana cikin maza marasa darajta matayen su. "Kije sis .." "Tohm." Daman ta gajin da tsaiwar da tayi akan su. Ta haye ta shige dakin da Maa tace ta shiga. Bandaki ta shige ta watsa ruwa. Sai da tayi da gasken gaske kafin ta gano yadda ake bude famfon. Ta dauro alwala jin ana kiraye kirayen sallar azahar na daya saura. Sallaya da hijabi gasunan an shimfida da carbi akai. Don haka tayi sallah da adduoi. Ta dan zauna tana zikiri kafin ta miqe ta koma kasa wajen Maa. Already Maa din ta kammala gashin da take. Har ta zuzzuba komai a food flask . Maaikatan na dauka suna kai wa Ummimi a sashen Haj. Barr Aisha. "Sannu da aiki Maa." "Yauwa sannun mu Waheedah. Ga naki abincin can a cikin plate. Na food flask din kuma na Hadiza ne. Idan zaki tafi seki tafar mata dashi " "Tohm Maa. Angode Allah ya saka da alkhairi." "Allahumma Aamin Waheedah, Bara nayo wanka na sakko " "Tohm sai kin dawo " Da sauri ta karasa wajen plate din. Fried rice ce lafiyayyiya da taji hanta sai sauce din nama da gasasshiyar kaza a gefe. Sai wani kwano karami daga kasan da aka dora plate akan sa. Soup din catfish ne daya gaji da haduwa. Ta wanko hannunta da sauri a sink ta shiga cin abincin bayan tayi basmala. Kunnuwanta har wani motsawa suke saboda tsananin dadin da abincin yayi mata . Kasa boye farin cikin data samu kanta akai tayi. Hawaye suka shiga reto a cikin kyawawan idanunta. Tunda mahaifiyar ta ta haifo ta duniya bata taba haduwa da cima kawacacciya mai madaukakin dadi da gardin dandano irin wannan ba. Maa ce ta bude kofar kitchen din ta shiga tana sallama. "Wa'alaykm Salam..." Waheedah ta amsa tana goge hawayenta "SubhanAllah! Waheedah...kuka? Kukan me kike yi? Fadamun wani abun akai miki? Eh Waheedah? Menene.?" Waheedah ta kasa cewa komai saboda farin cikin dake dankare a harshenta ya mata nauyin furtawa. "Menene . Eh?" Maa ta sake tambaya hankalin ta baki daya ya tashi . "Ba... Bakomi wallahi." "To kukan me kike yi? Ko ni ce? Kinga wayata na manta nasan kuma zaa neme ni kinganta akan microwave na barta. Sai Kuma zan ce miki soup din kifin ma nakine na manta nace iya abincin plate. Dan Allah menene Waheedah?" Waheedah kulawar Haj Hameedah tasa ta kara kaunarta a ranta. Da sauri ta goge hawayen dake tsiyaya tace "Allah maa ba komai. Kawai abincin ne yamun dadi. Gashi kala kala. Bantaba ci haka ba. Shine nake hawayen farin ciki. Allah ya saka muku da madaukakin alkhairi ya kara muku arziki mai albarka Amin. .." Haj Hameedah ta janyo ta jikinta da sauri ta rungumota . Hawayen itama suka shiga kwarara a nata idanun. "Ssssh! Kukan ya isa haka nan Waheedah. Nan ai gidan ku ne. Ya zama na ku. Kema din yar gidah ce Waheedah. Allah ya miki albarka ya baki miji nagari inda zaki je ki huta. Yan uwan ki su huta, Na kusa da ke ma su huta. Gidan jin dadi da kwanciyar hankali. Amin, kinji ko?" "Eh Maaa " "Yauwa yi sauri ki cinye abincin. Kinji ko?" "Tam..." Daukar wayarta tayi. Ta janyo tissue ta goge nata hawayen sannan ta fice. Waheedah ta sake daurayo hannunta ta zauna ta shiga cin abincin tana korawa da ruwa mai sanyi.... *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:24_ Tana karasawa ta yi hamdala . Ta nufi wajen sink ta wanko hannunta da hand wash din da Maa ta nuna mata dazu. Dusters din da suka baci ta diba. Bayan ta mayar da komai mazaunin sa. Ta tattare kitchen din ta yi mopping. Sannan ta fita da moper din da bokitin zuwa famfon baya. Ta wanko su tas ta shanya. Ta koma kitchen din. Wani spray ta gani na saka kamshin gidah na kamfanin da ta gani a rubuce na (yerwa incense and more) Faffesa shi tayi. Baki dayan kitchen din ya gauraye da kamshi. Ta dakko food flask din abincin ta riqe a hannun ta. Maa ta shiryo cikin doguwar riga ta rufe jikinta da mayafin rigar. Tana hango Waheedah ta dashare hakora. "Sakkowa ta kenan ni ma...Sannu da kokari." "Na dauraye su duster din nayi mopping kitchen. Akwai wani abun da za'ayi?" "Sannu da kokari yar albarka. A'a babu komai kin gama. Mungode kwaarai. Dan Allah kiyi wa Hadizan sannu. Yauwa ungo ki bata wannan maganin tasha. Har na tsawon sati daya. " Ta miqa mata wata leda mai dauke da magunguna. Ta cigaba da cewa, "Na zana yadda zata sha kowanne." "Tohm. Allah ya saka da alkhairi." "Aamin. Amin. Nima fitar zanyi ai. Yaran duk suna wajen su Ummimi. " Sai a sannan Waheedah ta daga kai ba kowa a parlorn da dinning area sai Haj Hameedan kawai. "Tohm sai da safe. " "Yauwa Waheedah." A tare suka fita daga cikin sashen. Waheedah tayi hanyar gate don fita. Ita kuma Haj Hameedah ta nufi sashen abokiyar zamanta inda Ummimi suka sauka.