← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 82

Sashe 52

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ma hakan take kamar ko da yaushe bayan ta dawo ranar lahadi daga ziyarar da ta kai gidan su. Ranar litinin da safe ta shirya ta tafi titi ta hau dan sahu ya biya da ita gidan su Basira da fannah ta dauke su suka wuce makaranta. Zayn ya kuma samun kansa da bin su a baya turyan tiryan har zuwa makarantar. Bayan yaga shigewar su ajin karatu ya samu wani dalibi ya dan ji cikin sa yasanar masa komai har da gudunmuwar tura wa Zayn time table dinsu ta waya. Ya koma mota ya zauna na ya na mai nazarin jadawalin karatun na su. Wajen aiki ya wuce. Lokacin da zai kasance free period din su kuma a lokacin Zayn ya koma ciki ya faka motar sa nesa da wajen su Waheedah. Yaga fitowar ta itada kawayen ta. Ragowar pure water din da ke hannun ta ta shiga wanke fuskar tadashi. Zayn ya zuba mata idanu yana kallon ta. Tayi kyau kwarai matuka ba glasses dinma. Sannan idan ta saka kara wani kyawun ta keyi. Ya samu kansa da sake janyo wayar sa yayi zooming din fuskar ta. Ya dau hotunanta ta camera yana murmushi. Sai da lokaci ya cika suka koma class. Sannan ya samu damar komawa wajen aiki shi ma. Bayan an tashi ya biya gidan su wajen mahaifiyar sa.. Inda take sheda masa tayi magana da Abiey din su. professor Adams Nasser . Ta karkare da cewar, "So Abiey din na ku ya yi wa Ummimi tuni akan abubuwan da suke faruwa tsakanin ka da matar ka Ahlam .. Kuma Ummimi ta amince da dukkanin matakin da Abiey dinku yaga ya dace. So Abiey dinku yace na maka maganar. Ko ka duba acikin dangi idan akwai wadda kake da bukata ka aura... Kar a tauye maka hakki. Ka cigaba da zama da Ahlam din. Amman ka kara aure .... Don kaga yarinyar mutane tunda na ga abubuwan naku gaba suke sake yi. Zan mayar ma iyayen su ita. Tunda ni ba yar aiki na baku ba. Ba zeyiwu ba ta cigaba da zama a karkashin ku ba. . So kaji yadda maganar ta kasance." Zayn ya sauke numfashi kawai kafin cikin ladabi yace, "Maa.... Wallahi banason auren zumuncin nan.. Dan Allah kada sanadiyyar hakan ya kara bata zumunci Maa. Ba zan iya kara aure da wata daga cikin family ba Maa. Na hakura." Haj Hameedah ta daga kai ta dube shi shaqeqe can tace "Ka taba ganin tsatson ku sun auro bare da ba na gidah ba?" "No..., Amma dai bana so Maa. " "To kai a naka ganin ya kake so ayi? Kai din da ba mata kake kulawa ba? Tunda can din Ahlam din ce dai. Duk kuwa da hadaku akayi amman kun dede ta tsakanin ku ai." Shiru yayi bai ce komai ba. Yanata jujjuya yadda zai fadi zancen Waheedah. "Kayi shiru.... Ba kace komai ba?" "Maaa... Ni da Abiey zai amince na auro wata daban... Ya kamata a soke auren dangin nan Maa. Kinga nawa beyi dadi ba kar a maimaita. Ni zan sakewa Ummimi magana..." Haj Hameedah ta daga kai ta dube shi shaqeqe kafin tace, "Kanata kawo maganar wata daban. Yar gidan wacece? A'ina take?" Zayn ya taune kasan leben sa ya saki kafin cikin sosa keyar sa yace, "Waheedah..... Itace wadda ta mai da ranakun baqin ciki na zuwa FARIN CIKIN ZUCIYAH ta maa.... Maa na waheedah itace FARHATAL QALB dina... Na fara kaunar ta tun farkon gani na da ita. Tun kafin na auri Ahlam... Tun bata kai haka shekaru ba Maa.... * Baki da kunne Maa ta saki. Tamkar gaula. Dimbin mamaki ya hadu ya tokare makoshin ta. Ta ma kasa magana. Ji take tamkar kunnuwanta karya suke mata na maganganun da Zayn ke fadi. Domin tunda take a fadin duniya bata taba gani ko jin Zayn ko a kawo maganar Zayn akan yammata ba. Bata taba ji ya buda baki yace yana kaunar mace fyace yanzu .Kuma ya kamo sunan wadda ko a mafarki bata taba zato ko tsammani ba. Wai yau Zayn. Mai madaukakin zurfin ciki da adana magana.shi ne ya buda baki yana magana akan kaunar mace. Macen ma Waheedah da yake kiran da ita din ce FARIN CIKIN ZUCIYAr sa... "Ka ce me?" Ta tambaye shi cikin dimbin mamaki. "Waheedah dai maa.. Dan Allah kar ki ce a'a.... Ina kaunar Waheedah...Kauna irin wadda gangar jiki ke wa zuciya. Zuciya ke aika sako zuwa ga rai. I loved her, with every fiber of my being.... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWA I *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:54_ *SCHOOL OF NURSING AND MIDWIFERY* *Waheedah* ta cika da mamakin yadda ya san ina ne faculty din su kai tsaye ba tare da ya tambaye su ba, Yaje har kofar ya faka motar. Basira da fanna na fita ya sakawa motar lock. Waheedah ta saka hannu zata bude ta jita a datse. Hakan yasa su Basira shigewa ciki su bar ta. "Mungode.... Zan sauka." Shiru bai tanka ta ba. Niimataccen kamshin jikin su daya cakudi waje daya sai kamsasa motar yake yi. Ganin tamkar hankalin sa baya jikin sa yasa Waheedah sa ke cewa, "Ya Zayn.... Zan fita. " Juyawa ya yi ya sauke manyan idanun sa akan ta. Ta kasa jure kallon sa tana mai mayarda kan ta gefe, "Waye wancen yaron da na gan ku tare?" Ya tambayeta cikin isa da iyawa. Tambayar tasa ta daure mata kai ainun. Ina ruwan sa da wanda suke tare? "Magana na ke miki..." Ya sake fada hadi da juyawa ya fuskan ce ta sosai. Da kamar ba zata ce komai ba. Sai ta tuna da yanzun a karkashin kulawar su ta ke. Yana da ikon tambaya tunda yanzun sune tamkar marikanta Ba tare da kawo komai ba ta ce, "Ya Ibrahim..... " "Meye alakar ku da shi? U in particular. Uhm?" Ta danyi jim. Can kuma tace, "Abokin Yaya nane da ya rasu...." "Allah ya jikan sa ya gafarta masa " "Amin.. Nagode." "Ba wani abunda zaki ce bayan haka? Ba wata alaqa ta daban?" Ta saka hannu ta tura glasses din ta ciki kafin ta bashi amsa da, "Yace ya na...." "Uhm ya ki kayi shiru. Yace yana me?" "Dan Allah zan fita. Na yi latti wallahi." "Eh ki gayamun gaskia.." "Gaskiyar kenan." Ya kada kai kawai. Ya danna button ya cire mata lock. Ta fice da sauri bata waiwaya ba har ta shige ciki. Zayn ya samu kan sa da sakin tattausan murmushi. Kafin ya ja motar ya bar cikin makarantar zuwa ofishin aikin sa. Da sauri ya rufe laptop din gaban sa yana kallon lokaci a agogon da ke daure a wutsiyar hannun sa. Yana kammala komai ya dauki wayar sa da mukullin motar sa ya fice daga wajen aikin na su. Kai tsaye ya shige mota ya nufi makarantar su Waheedah yana mai sharara gudu. In dai ba an canza musu tsarin lectures din ba. Saura minti 20 a tashe su. Don haka yana karasawa ya samu waje yayi parking. Ya fito daga cikin motar ya jingina bayan sa. Yayin da hannuwan sa biyu ke zube acikin aljihunan gaban wandon sa. Ba jimawa sosai kuwa students suka fara fitowa daga cikin faculty. Ya gyara tsayuwar sa yana jiran fitowar ta. Ita da Basira ne suka fara fitowa sai fannah da ke bayan su. Basira ta bude baki tana, "Laa kinga ya dawo daukar mu.." "Yana ina?"
Chapter 52 · 0% Book details