Sashe 50
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
musu girkuna ko?" "Eh..." "To me da me kike bukata na girkin? Abunda babu sai mu sayo " "Bari na duba." Ta mike ta shiga kitchen ta dudduba. Biro da paper data ke rubuta abunda babu a kitchen din ta dakko tayi list. Ta koma parlorn ta mikawa Ahlam "Gashi aunty." "Okay... Ga shi babe." Ahlam ta mikawa Zayn Ya karba ya karantawa kafin ya ce da Ahlam din, "Ki shirya mu sissiyo abubuwan." "Kai gaskia babe agajiye na ke." "Me kikayi da kika gaji?" "Kuje da ita mana .. Tunda ta fini sanin kan abubuwan." Ya kada kai kawai yana danne leben sa na kasa. "Mu je..... Wa... Hee.... Dah.." Ya rarraba sunan nata tamkar dan koyo. Ta daga kai ta kalle shi tana mamakin dama ya san sunanta? Kafin ta bai wa kanta amsar tambayar ta tuni ya fice wajen bayan ya dauki mukullin motar sa. Ta juya ta dubi Ahlam da ta tattara tunanin ta da nutsuwar ta akan tv da ke nuna shirin keeping of with the Kardashians. "Aunty mun tafi." "Okay Waheedah.... Dan Allah kice masa wai yayi mun renewing data plans dina. " "Tohm." Ta juya ta shiga dakinta da ke a matsayin na ta. Ta zura takalmanta ta fita zuwa wajen motocin. Yana cikin motar ya tasheta already. Tana zuwa ta shiga ya fita daga cikin gidan. Tanata jujjuya yadda zata yi masa maganar datar. Can dai ta ce. "Aunty tace.... Wai." "Wai me ?" Ya tambaye ta kansa akan titi... "Wai ka mata renewing data plan..." Cikin zuciyar sa abun ya bata masa rai. Amman baya so ta gane kwarai akwai matsala a tsakanin su. Don haka ya gyade kai kawai kafin yace, "Okay ...." Yankaba suka je. Waheedah na zaba yana saya. Suka siyo komai daya danganci fannin abubuwan da zatayi amfani da su a girkin. Daga nan suka biya Sufi mart suka cigaba da siyayya. Shi ke rike da kwandon siyayyar. Yayin da Waheedah ke dauka tana saka wa aciki. Idan ka kalle su zaka rantse da Allah mata da miji ne irin farkon auren nan. Saboda tsananin yadda suka da ce da juna Ta dauki wani corn flour tana karanta bayan sa. Zayn ya rankwafa. Tururin numfashin sa na dukan jikin ta. Ji yake inama ace halaliyar sa ce. "Kina bukatar wani abun? Na ki bana gidah ba.... Uhm?" Zillewa tayi ta na girgiza kai. "A'ah..." Suka wuce wurin biyan kudi aka lissafa kaya ya biya suka fita. Ya bude booth ya saka kayan. Yaja suka dauki hanyar gidah. Kan ta akan carbin data ke ja. Sai ya juya kamar zai mata magana sai kuma ya fasa a haka suka karasa gidah. Ko da suka je. Nan da nan Waheedah ta shiga yin aiyukan iya karfin ta. Ya yinda Ahlam ke kame a kujera. "Baka samun data din ba...." "Ahlam... Bakya gajiya da danna waya ne? Idan ni ba ki da lokaci na. Ke kan ki ba zaki bawa kanki lokaci ba? Uhm? Har abada kan ki na kan waya? Yanzu da yarinyar nan bata nan wa zeyi girkin eh?" "Yanzu danna wayar ma matsala ne babe? Danna waya rage kadaici yake. Kuma de favorite hobby na ne.... Sannan batun abinci. Ko ba Waheedah dole zaa kawo me yi. To me ya rage?" Ya girgiza kai yana tabe baki. "Ba komai..." Sai bayan laasar Waheedah ta kammala komai. Daki ta koma ta yo wanka saboda kaurin girki da take. Ta cire kayanta ta dauraye ta shanya. Ta zura wata riga fara me karamun hannu da Nadra ta bata. Lapiar gado ta bi ta kwanta bayan tayi sallah. Sai sauke numfashi take. Saboda gajiyar da ta yi. Har ta fara bacci tajiyo budewar kofa. Ahlam ce ta shiga dakin. "Waheedah..." "Naam.." "Kizo kiyi serving dinsu. Akwai drinks a freezer ki hada." "Toh.." Bayan fitar Ahlam daga dakin. Waheedah ta mike tana rufe bakinta sakamakon hammar data taho mata. Hijabin ta ta zura. Ko glass bata saka ba tafita. Kitchen ta shiga daya bayan daya ta shiga kai abincin kan dinning. Dai dai shigowar Zayn da abokan na sa. Useey, Lameen da Awais. Baki daya suka tsaya kallon ta banda Zayn daya wuce ya zauna. Ta dakko tray din karshe dake dauke da cups ta ajiye. "Ina wunin ku....?" Ta fada tana jera komai. Don taga shigowar su. Amman ba zata iya cewa ga kamar su ba. Tunda bata ganin su sosai. Amsawa sukai baki a sake. Sun zuba idanu suna kalleta daga sama har kasa. Har sai data kurewa kallon su ta koma daki A tare suka shiga zubawa Zayn ruwan tambayoyi akan Waheedah. Tun yana daurewa yana amsa su har ya dena. Don wasu tambayoyin na saka zuciyar sa radadi. Du bada shi dinma a nasa bangaren yafu kowanne cikin su kwadaituwa da son kasancewa ko mallakar Waheedan ta zama ta sa. Suka shiga cin abincin suna zuba santin lalle madam Ahlam ta iya girki. Basu gano dawar garin ba. Sai murmushin yake kawai Zayn ya ke. Ya biye musu akan cewar Ahlam din ce ta girka girkin da suke santi. Yanata doka mata message ta Whatsapp kan ta sakko su gaysa da abokanan sa. Sai data mula ta sha iska tukun sannan ta sakko tana kukkumbura a yatsine ta gayda su ta juya ta koma sama. Zayn ya harhada zancen bata jin dadi ne da sauran su. Suka yita mata adduar samun lapia mai dorewa "Har zamu tafi baka kira mana yarinyar nan ba mun gaysa." "Ba kun gaysa ba...?" Zayn ya basu amsa yana sakatar hakoran sa da toothpick. "Maza dan Allah ta shi ka kira ta." "Itama ba dadin take ji ba. " "To Allah ya basu lapia baki daya.." "Amin.." Play station (ps) suka fara bugawa ta tv. Sun jima suna hirar tasu ta abokai har aka kira sallar magrib suka fita sukayi a masallaci suka dawo . Sai bayan da akayi ishai suka cinye sauran abincin sunata santin daya ki karewa. Daga fita sallar ishain da suka yi daga nan suka wuce joint dinsu sai kuma kowanne ya tafi gidah. Awais nata kulaficin naci kan lalle a dole Zayn ya samo masa number Waheedah. Shi da gaske yake yana kaunar ta. So yake ya mallaketa a matsayin matar aure. Wadda zata zamo uwar yaran sa. Zayn ya dube shi kawai ya watsar. Domin ba shi amsa ma bata lokaci ne. Don ba zai taba hada shi da waheedan sa ba. Don kuwa shidinma kullum cikin adduoin sa sai ya kamo sunan Waheedah ya roki Allah da ya mallaka masa ita a matsayin matar sa ta sunnah idan har alkhairi ne hakan agare su baki daya ..