← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 82

Sashe 53

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fanna ta tambaya tana leke. Waheedah na daga kai ta hango shi. Gabanta ya ja yayi turus. Ta kasa gane sabon lamarin da ya tsira. "Ko dai ko dai ...." Fannah ta fada tana dariya. "Ai kuwa dai .. Na ga ya fara folawa yasin." Basira ta bata amsa itama tana mai shekewa da dariya. Waheedah wani tuqwiqwin takaici ga taso ya tokare mata a wuya. Ta dube su tana yamutsa fuska, "Ku fa banzaye ne wallahi. Abun shirme zaku fara ko dai ko dai. Kaffa ku manta a gidan fa na ke. Maybe Maa ce tasa ya dinga kawo ni yana dakko ni. Yau ne fa kawai ya kawo mu sai wani dashare hakora kuke yi kafin ya ganku ma ya zata farin ciki mu ke dan zai dauke mu." "Yo ai gaskia abune na farin ciki. Sisi na kudin motar mu yau bai yi ciwo ba. Allah ya saka masa da alheri. Yau fa har dan party zan hadawa kai na. Da kudin motar yau da banyi amfani dashi ba. Zan sayo gurji da kifin salihu. Gefe daya kuma zobon baba larai." Fannah ta fada tana dariya. Tana direwa Basira ta dora da cewar, "Kamar kin shiga can cikin zuciya ta fannen mu. Sai dai ni ba zobo a budget dina. Kankarar ruwa zan siya ta foster Clark din shagon ma'aruf. Na korawa makogaro na. Ya kukaji wannan hadin?" "Superb kawalli. Lamarin zai bada color. " Duk bikin zancen nan da su ke Waheedah bata cewa komai. Ta shiga tafiya ahankali tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki. Ita dai inde har Maa ce ta sa Zayn ya dinga kawota ya na kuma mayar da ita gidah idan an tashi gaskia bata so. Da da hali da an soke umarnin. Haka suka karasa har wajen motar sa. Yan faculty duk sai suka tsaya suna bin su da kallo. Musanman Zayn din da ke da madaukakin kyau . "Sannun ku da karatu.." ya fada. Hadi da shigewa cikin motar. Basira da fannah ma suka bude suka shiga . Waheedah ce kadai bata shiga ba. Tana ta raba idanu. Can dai ta bude murfin gaba ta shiga . Ya tada motar suka fita daga cikin makarantar. Motar shiru ba mai magana. Sai sanyin ac da ke dukan su. A haka suka karasa unguwar ta su fannah . Ya kai su har kofar gidajen su. Sai kuma ya juya kan mota suka dauki hanyar gidah su ma. Yana driving yana satar kallon ta. "Kina bukatar wani abun....?" Ya tambayeta cikin muryar lallashi. Sam bata ji ba. Don gaba daya ta lula duniyar tunani. "Waheedah...." Ya sa ke kiran sunan ta. "Na'am." Ta amsa shi kanta na kallon waje. "Kina bukatar wani abun?" "A'ah....." "Kin tabbata?" Nanma tayi biris bata ce masa komai ba. Kasan zuciyar ta take kunkunin ina ruwan sa da abunda take bukata? Uban yan kanzagin shisshigi da fadi baa tambaye ka ba. Bai sake cewa komai ba. Domin shi kansa mamakin yadda ya ke susucewa akan Waheedah ya ke. Itace mace ta farko da yake bi yana kuma kwadaituwa da son kasancewa da ita ta hanyar halal. Gashi sam baya gaban ta. Shi kadai ya ke shirmen sa. A haka ya karasa gidah. Tun daga nesa baba mai gadi ya hango motar . Don haka da wuri ya bude gate din. Zayn na zuwa shiga kawai ya yi da motar sa ciki. Yana mai yabawa baba mai gadin shi kuma baban na saka masa albarka. Knocking tayi. Kafin ta danna door bell. Sai da Ahlam ta mula ta sha iska tukun sannan ta mike ta bude kofar. Gidan nan tamkar ba dazu da safe Waheedah tayi gyaren sa ba yanata kamshin turare. Yanzun kuwa yadda kasan yara ne sukayi dabdalar damben su a parlorn. Ga ledoji nan na chocolates Ahlam ta sha ta zubar su. Waheedah ta karewa ko'ina kallo tana kakalo murmushi. "Sannu da hutawa aunty..." "Yauwa my dear sis.... Cikina kamar yasan ke ce dawo. Yunwa nake ji wallahi." "Bara na cire kaya sai na dora abincin." "Yauwa pls .." Zayn da ke sauraron komai yayi Allah wadai da banzar dabi'ar Ahlam abincin da zata zuba acikin ta ma ba zata iya dafawa ba sai Waheedah ta dawo. Komai kaca kaca taki gyarawa. Takaici yasa ya durkusa ya kwashe ledojin ya zuba su a dustbin. Ya dauki air_freshener ta kamfanin turaren yerwa incense and more. Me kamshin oud oudi ya faffesa a parlorn. Zama yayi akan kujera. Ita kuma gogar taku ta cigaba da kallon da take. Tana kara volume. "Ba ni ruwa...." Ya fada yana kallon ta. "Waheedah.... Kawo ruwa. " "Waheedah ce zata ban ruwan?" "Eh to menene aciki? Tana kitchen. Hakama ruwan a kitchen ya ke. " "Ok." Kawai ya fada. Ya mike ya haye sama kansa na matukar sara masa. Tunane tunane ne dankare cikin zuciyar sa. Ya rasa ta inda zai kamo bakin zaren. Bandaki ya shige bayan ya murzawa kofar dakin na sa key. Saboda yadda kansa ke sarawa. Tamkar zai fado kasa saboda tsananin yadda yake masa ciwo ne. Yasa yana fitowa ya kwanta . Ba tare da bata lokaci ba kuwa bacci ya dauke shi Bai farka ba sai gab da magriba. Yayi sauri ya shiga bandaki yayi tsarki hade da dauro alwala. Ya sauka kasa don tafiya masallaci Ahlam bata kasan. Sai Waheedah da ke cikin kitchen tana wanke wanke. Da ke kofar a bude take. Tana tsaye agaban sink tana wanke wanken sanye cikin wata doguwar riga marar nauyi. Masallaci ya fice yaje yayi magriba. Ya zauna yana lazimi har aka kira ishai. Bayan sunyi ishai a jam'i ne ya karasa yan adduuoin sa sai kuma ya mike ya koma gidah A parlorn kasa ya zauna yana kallon news a CNN . Waheedah ta kammala aiyukan ta ta shige daki ta saka key. Har ta shige ciki bai dai na waiwayon kofar dakin ba. Yarinyar na tafiya da nutsuwar sa, Tunanin sa dama gangar jikin sa gaba daya. Ya yinda itace FARIN CIKIN ZUCIYAr sa. Kallonta kawai idan yayi sai ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Ta yaya zai gaya mata abunda ke cikin zuciyar sa akan ta? Taya zai sanar da ita ce FARHATAL QALB din sa? Ta ya ya zai gaya mata itace macen da yake ta dakon soyayyar ta tsawon lokaci? Ya sauke ajiyar zuciya kawai So ya ke ya samu ko da number wayar ta ne.... "Anya tana da waya ne ma?" Ya tambayi kansa cikin gasgatawa. Ya cigaba da kallon news har wajen 12 saura na dare. Daga bisani ya haura sama don yin bacci. Ya nufi dakin Ahlam ya murda yaji a kulle. "Ki gayawa malamar aji.....Da hausa room) Kunnuwan sa suka jiyo masa maganar aminiyar Waheedah . Da alama waya suke yi. Kuma a handsfree ta sa ka. Ya girgiza kai kawai ya wuce dakin sa. Ko da ya shiga bandaki ya wuce ya dauro alwala da wanka. Ya zura kayan bacci. Wayar sa ya janyo ya shiga Whatsapp yaci sa'a kuwa Awais yana online. "Aboki na...." Ya aika wa Awais ta Whatsapp. "Ah maza ya ne?" "Steady kawai.... " "Yauwa, Na ce wacece malamar aji a bloggers dinnan ne?" Awais ya aika masa da emojis na dariya da hawaye kafin ya amsa shi da, "Aisha falke mana. Northern hibiscus. Itace suke kira da malmar aji. " "Alright... Thanks" Dai-daita kwanciyar sa yayi akan gado. Ya shiga Instagram yayi searching page din northern hibiscus. Yana shiga kuwa yaga sabon post da ruwan comments a kasan sa. "Assalamu alaikum Malama.... Ya kamla da dan mutum? Pls keep me anonymous, Ni amarya ce. Malama miji na ne ko shekara bamu yi da aure ba ya canza. Dama can kafin auren baya kauna ta. Na dauka idan anyi komai zai warware. Wallahi Malama sam bana gaban sa. Bashi da aiki sai chatting da yammata a duk wasu social media handles... Kullum idan na duba wayar sa sai naci karo da abubuwan bacin rai. Tamkar ba miji da mata muke ba, Yanzu ma na bara so a parlorn kasa ni ina daki na a sama. Sai ya kusan raba dare acan yana kallo. Malama da yan aji dan Allah a temaka mun da shawara. I will be in the comment section. Thank you." Mamaki ne ya mamaye sa. Ganin yadda ta girba zance tiryan tiryan kamar gaske. Comments din ya fara bi wasu na bin bayanta wasu na bin bayan sa. Wasu kuma zage ta suke tas. Kasa cigaba da karanta comments din yayi ya fice daga page din Ya sa ke searching HausaRoom don ganin wanda ta kai can din. Ya cika da mamakin ganin writeups kala kala har ya zo kan wanda yake da tabbacin natan ne. "Assalam.. greetings Malama. Hide my ID. I got married to the absolute love of my life some months ago. Dan ko shekara ba muyi da aure ba. Gaba daya na kasa gane kansa ya canza. Sam bana gaban sa. Amarya ce ni amman yadda kika san wadda ta tsufa agidan miji haka na gundure shi. Sam bama having lokacin kan mu ni da shi. Baya shiga harkata kwata kwata. Gashi da yawan kai korafe korafe wajen manya. Da ke ni da shi first cousins ne. Manya sun shiga tsakani sau ba adadi amma gaba daya yaki canza halayen sa. Maganar da na ke miki yana kasa yanzu a parlor yana kallo sai ya raba dare acan. Ya zanyi please? Ku ban shawara. Thank you." Yana karasa karantawa ya daga kansa sama yana madaukakin mamakin Ahlam lalle ta wuce gaban tunanin sa. Yan social media ta dauka yan uwa da take zuwa tana fadan matsalar ta. Wani abun takaicin ma ta mayar da lefin ta kan sa. Ya cigaba da bin comments wani ya bashi dariya wani haushi. "Amarya? Kuma first cousins? Yar uwa baku da manya ne a naku dangin da kika ketare su kikazo bidar shawara a duniyar social media? Ni dai ga dukkanin alamu kece me matsalar ba mijin ba wallahi. Allah wadaran naka ya lalace. Irin wannan matan gaba daya basuda sirri. Mijin poster idan kaga post dinnan kana kuma da raayin kara aure ka neme ni please. Zan baka kanwata. Tanada sirri ba zaa taba jin kan ku ba. ....
Chapter 53 · 0% Book details