Sashe 62
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallo Alokacin Haj Hameedah ke tambayar ko an sanar wa Waheedah wanda aka aura mata? Su Gwaggon suka amsa mata da a'ah... Alokacin da sukayi niyyar fada kuma zazzabi yaci karfin ta don har tasha panadol ta kwanta bacci tun dazu. Haj Hameedah da kanta ta mike ta shiga daki wajen Waheedah ta tattaba jikin ta zafin ya ragu. Don haka ta dan tashi waheedan. Dakyar ta iya gayshe ta saboda yadda kanta ke sara mata. Ta dauke MacLean da brush dinta ta nufi bandaki tayo brush. Ta gayshe da mutanen tsakar gidan tana bin su su da kayan da kallon madaukakin mamaki. Ta koma daki ta sake gayshe da Haj Hameedah . Sannan ta zauna tana matsa yatsun hannuwan ta. Maa ta leka da kanta ta kira su Gwaggo da Umma Hadiza. Tsakar gidah ya zama sai su Najan Isubu dake kirga kaya. Ta dora dan karamun kit din da sakar gold ke ciki dauke da zobuna da awawwaraye manya manya... "Waheedah ya jikin naki?" "Da sauki Maa." "Akwai inda ke miki ciwo?" "Babu sai kai na kawai da ke sarawa kadan kadan.." "Masha Allahu. Sannu kinji?" "Yauwa.. Maa" "Waheedah Ina son ki bamu aron hankalin ki. Ki kuma tsayar da shi waje daya. Ki kuma ajiye zantukan da zamuyi a mizanin hankali . Kinji?" "Insha Allah Maa." "Ki sani har gaban abadan ba zamu miki zabi da zai cutar da ke ba. Ina nufin ba zamu zaba miki abokin zama wanda ba nagari ba ne. A har kullum adduoin akan ki basa wuce Allah ya hada ki da abokin zama na gari. Inda zaki je ki huta wani naki ya huta. Ki samu nutsuwar kwanciyar hankali. Kina fahimta?" "Eh..." "A baya kinsan mahaifin ki ya karbi kudin auren wanda ke neman ki amatsayin abokiyar rayuwa ta aure ko?" "Eh...." "Bakisan waye ba kika amince ko? Saboda biyayyar iyaye da amincewa da zabin su da yafi son rai ko?" "Eh Maa " Ta amsa gabanta na tsananta bugawa .. "Tohmmm... A yau an daura aure ke da yan uwan ki ku uku idan har ban manta ba.... Ko Hadiza?" Waheedah da sauri ta daga kai ta dubi Haj Hameedah. Tabbas tasan an karbu kudin auren ta don har ciwo tayi amman ta hakura ta amince . Ko dan farin cikin mahaifiyar ta. Amman bata taba zaton da ita aka hada aka aurar yau ba... "Kiyi hakuri Waheedah..." Umma Hadiza ta fada kanta a gefe. Waheedah gabanta ya sake bugawa. Ta mayar da kallon ta kan Maa data daga mata kai ta sauke itama, "Yadda kika bi umarnin mahaifan ki. Kikayi hakuri da sa hannu biyu ki ka karbi zabin da suka yi miki. Ina fatan Allah yasa wannan shine matakin farko na shiga sabuwar rayuwar ki mai tattare da FARHATAL QALB!! (FARIN CIKIN ZUCIYA...) Daga yau kin dinga samun FARIN CIKI a ZUCIYAr ki har ya zuwa ranar da zaki koma ga mahaliccin ki Waheeda.. Allah ya saka miki da alkhairi ya hade kawunan ku. Amin" Hawaye ne suka shiga reto a kyakkyawar fuskar Waheedah masu dumi. Hakika dukkanin wanda ke jiyo sautin kukan Waheedah dole zuciyar sa ta karaya. Da tausayi matuka ga dukkanin wanda ya samu kansa a halin da Waheedah ke ciki. Hawaye ne mai dauke da labarai masu tsuma zuciya acikin sa... Wanda take so da kauna daban ... An raba su ta hanyar auren dolen da akayi mata da wanda batasan awacce nahiyar yake ba. Ta karbi kaddarar ta da hannu dubu duk kuwa da bata da tabbacin hannun da zata faada. Ta samu FARHATAL QALB da Dawood wanda suka yiwa junan su alkawarin aure don cigaba da gina soyayyar da suka fara... Duk kuwa da bata haduwa da shi ba tun bayan bikin su Zayn amman kaunar sa tayi tasiri a zuciyar ta alokacin da suka fara magana ta WhatsApp har suka dai-daita kan su. (Gara Ta saka kasan hijabin ta ta share hawayen da ke tsiyaya daga fuskar ta. Sai shessheka kawai da take yi. "Kiyi hakuri Umma. Na kasa tsayar da hawayen ne" Ta fada ahankali don kada ta raunata ran mahaifiyar ta. Zatayi zaman auren ne kawai saboda farin ciki ya wanzu a zuciyar mahaifiyar ta ta dama sauran yan uwa da masoyan su "Ki yafe ni Waheedah. Ki yafe mana baki daya kinji?" Umma Hadizan ta fada itama muryar ta a raunace. "Ba abunda kuka mun Umma.... Allah ya yafe mana baki daya." "Amin Allah ya miki albarka. Allah ya saka miki da mafificin alkhairi. Allah ya shiga lamuran ki baki daya." "Amin Umma." Haj Hameedah ta janyo Waheedah jikin ta tana mai shafa bayan ta. Har cikin magudanar jininta take jin kaunar Waheedah. Can ta nisa kafin tace, "Waheedah..." "Naam Maa." "Kiyi hakuri da abunda labbana zasu furta...Don bamuyi wannan hadi dan munantawa rayuwar ki ba." "Tohm Umma... Au Maa " "Zayn shine wanda aka daura miki aure da shi yau. Kinji Waheedah.." Ai baki daya.... Ji da ganin ta ne suka dauke na yan wasu dakikai ta zama tamkar mutum mutumi.... #DESTINED LOVE... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ ______ _PG:60_ "Kinyi shiru Waheedah.... " Cewar Haj Hameedah. Ta dan jijjiga waheedan. Umma Hadiza ta sake dukar da kanta a k sa. Tausayin tilon yar ta ta mace ya kamata kwarai matuka "Waheedah... Diyar albarka." Gw aggo haule ta fada itama gabanta na harbawa. Waheedah ta daga kai. Ta sauke numfashi da kyar tana jijjiga kanta da sauri "Menene Waheedah?" Maa ta sake tambayar ta cikin kulawa. "Maa, Umma, Gwaggo. Kuyi hakuri amman ba zan iya zaman aure da Ya Zayn ba." "Meyasa Waheedah... Why?" Maa ta tambaye ta cikin fargaba. "Bar cewa haka Waheedah.... Kinji?" Cewar Gwaggo haule. "Ya Zayn tamkar marigayi Ya Kamal na dauke shi. Na dauke shi tamkar wanda muka fito ciki daya. Yaya Ahlam itama tamkar Yaya ce awaje na. Ta dauke ni kamar kanwar ta da suka fito ciki daya.... Ya zata ji idan har taji ni da ya Zayn an daura mana aure? Zata dauka naci amanar ta ne. Dan Allah kuyi hakuri amman ba zan iya zaman aure da ya Zayn ba. Na amince a auramun koma wanene amman banda ya Zayn.. Dan Allah...Zuciyata zugi ta ke Maa. Kasan zuciya ta tamkar zai ballo saboda radadi.." "Dan Allah Waheedah ki bar cewa haka kinji? Wannan aure Allah ne ya hada. Da kuma rokon da Zayn ya dukufa yanayi a sujjada har Allah ya karbi adduoin sa. Zayn ya dade yana dauke da kaunar ki a zuciyar sa Waheedah. Ke ce FARIN CIKIN ZUCIYAr Zayn ... Yana kaunar ki tun kafin a daura auren su da Ahlam Waheedah. Zan iya tabbatar miki cewar kece first love din Zayn kamar yarda ya sanar da mu. Ya fara kaunar ki tun kafin ki zama yadda kike a yanzu. Maana tun kina karama... Ki sani auren ku da Zayn ba kici amanar Ahlam ba. Hakama Zayn bai ci amanar Ahlam ba. Zaki fi dukkanin mu masaniyar komai saboda kece kike zaune a tare dasu... Kinsan irin zaman da suke yi. Wanda maslahar sa aure ce. Na karkare miki zance har satin bikin Zayn bai dai na roko na a fasa auren nan ba don yanada wacce zuciyar sa ke muradin kauna., Bamu amince da auren ki da Zayn ba don mu muzanta miki. ko dan muci amanar ki mu kuma tauye miki hakki.. No! Auren ki da Zayn alheri ne. Auren ki