← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 82

Sashe 25

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dadin sa baa magana. Ci take tana kada kai. Tana kuma godia agare su. Tana karasa ci. Ta dauki plate din ta wanko tas. Ta koma parlor wajen su Maa. "Akwai abunda za'ayi. ?" "Kwanukan can zaki wanko kawai Waheedah.... Wanda Yayan ku yaci." "Tohm Maa." Ta wuce dinning ta dakko kwanukan. Ta kai sink ta wanko su tas ta jera su a plates keeper . Ta dakko food flask din da akace abincin Umman su ne. Parlorn ta koma ta durkusa tana wa Maa sallama da ke tare da Zayn. Yana zaune a kujerar da ke gefen ta Maa Kamshin turaren ta yaci ka hancin sa. Sai lumshe idanu yake, Moment dinsu na kwanaki na kara dawo masa . "Science ki keyi ne ko art?" "Science.." "Masha Allah,.. menene future ambition din ki?" "Inason zama nurse ...." "Masha Allahu. Allah yabaki iko. Ya bada sa'a Waheedah .." "Amin Maa." "Masha Allah......!!! To shikenan Waheedah, ki gayshe da Hadizan kinji? Ki kuma yiwa yan uwan na ki sannu " "Insha Allah Maa. Zasu ji baki daya " "Tohm sai da safe. Allah ya kai mu " "Amin....." Cewar Waheedah. Ta nufi kofa ta bude kofa ta fice. Tana tafiya akan hanya tana mamakin kirki da mutunci irin na Haj Hameedah. Har zatabi ta layin majalisar su Ibrahim ta fasa. Ta layin baya ta ketara ta bi. Ta shige gidah bakinta dauke da sallama. "Ina wuni Marka?" "Yana gidan uban ki... Saboda yanzu kuna cin cima mai dadi ta gidan masu hannu da shuni shine kuke hura hanci kuna wami fankama da dagawa. " Waheedah tayi shiru. Don sam bataga abun da su kayin ba da har Marka ta dameta taketa fadan maganganun marasa dadi Ji kake kwas ta sakar mata rankwashi a tsakiyar kanta. Waheedah ta dafe wajen da sauri. Idanunta suka cicciko saboda tsananin zafin rankwashin da Markan ta sakar mata. Da sauri tace da ita cikin ladabi, "Kiyi hakuri Marka ." Marka taja dogon tsaki. Ta fi ce waje ranta na dada sosuwa ganin katuwar kular abincin da ke hannun Waheedah. Babban takaicin ta yadda nasu ne abincin sede su sanmata. Abunnan yana ci mata tuwo a kwarya dole ta nemo mafita.... Waheedah ta girgiza kai kawai ta karasa shiga ciki tana sallama. Ta wuce dakin su da sauri tana yiwa mahaifiyar ta sannu . Taci tuwon sosai Umma Hadiza. Har dare ya kai musu. Suka karasa cinyewa a abincin dare. Marka ma an zuba mata an kai mata .. Rayuwa nata garawa cikin aminci da yardar mai sammai da kassai. Lalle Allah qadirun ne ala manyasha'u. Sannu ahankali Umma Hadiza sai da tayi kwanaki 10 tana jinya chas. Waheedah ce kullum ke zuwa gidan na The Adams family. Sashen Umma Hadiza. Sunyi matukar sabo da shakuwa ga dukkanin yan gidan baki daya. Idan ku ka tsame Zayn ku ka ajiye a gefe. Shi kadai ne kaf a The Adams Family basa shiri kwata kwata . Har ta dau rashin shirin su a matsayin tsantsar kiyayya da kyama aganin tah . *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:28_ ======== Shirye-shirya ake gadan gadan na bikin dangin Ambassador Nasser Family. Gaba daya dukkanin yan dangin ciki da wajen sa sun fara hallara a garin na kano. Wadan da suke Kaduna dana Abuja da Lagos duk sun zo . Yayin da sauran dangi na Sudan dana Egypt duk sun fara sauka a kasar ta Nigeria. =========. Yana zaune a bakin gadon sa. Hannuwan sa dafe da kansa. Ya sauke ajiyar zuciya a karo na ba adadi. Kasancewar asabar ce ba aiki miqewa yayi ya fita kansa tsaye zuwa sashen mahaifin su. Da sallama a bakin sa ya shiga babban parlorn dake sashen mahaifin su. Professor Adams Nasser yana daga zaune akan wata hadaddiyar kujera kirar royal chairs samfurin turkey. Har kasa ya durkusa ya rissina ya fara gayshe da mahaifin na su cikin biyayyah da ladabi, "Abiey barka da safiya....!" Ipad din hannun sa ya ajiye a gefe. Ya daga kansa yana kallon Zayn dake durkushe. A hankali yace da shi, "Kana lapia ..?" "Lapia kalau Abiey ..... Ya murar? Allah ya kara afuwa, Aamin." "Na warware Zayn. Ya aiki?" "Alhamdulillah Abiey. Muna ta hutun weekends ." "Masha Allah .. Allah ya temaka " "Aamin Yaa Rabbi." "Akwai wani abunne Zayn ..?" Kasa cewa komai yayi duk kuwa da abunda ke damun sa a kasan zuciyar sa. "Babu komai ... Abiey " "Ka tabbata?" Professor Adams ya sake tambayar sa cikin kulawa da lurar yanayin 'dan na sa. "Eh .. Bakomi Abiey " "Tou shikenan Zayn. ... Allah ya temaka, Amin" "Amin Abiey. A huta lapia " Ya sake durkusawa yayi masa sallama ya tafi. Daga can ya hangota a tsaye suna guje guje da auta Moha . Kayan jikinta sari ne irin na indiya dinnan . Kirar riga da wando. Mayafin kayan ta daura shi akanta . Mayafin ya zume ya fadi. Yalwataccen gashin kanta baqi na larabawan usuli ya bayyana. Zayn ya samu kansa da tafiya ahankali. Hannuwan sa acikin aljihun sa biyu na wandon dake jikin sa. Tafiya yake. Yayinda iska na kadawa ahankali. Yadda suke guje gujen da Moha kwarai matuka ya kawatar da shi. Ya saki tattausan murmushin daya kasa gane na menene. A haka ya karasa sashen na Haj Hameedah. Moha ya tafi da gudu ya rungume shi . Waheedah tayi saurin jan mayafinta tana gyarawa. "Akieee. " "Na'am baby brother. " Ya dauke shi yana jujjuyawa dashi "Me kake ci ne ..? Ka kara kiba tubarkaAllah..." "Anything flour Akieeey .. Su waffles , Pancakes. Pies and the rest " "Um dan gayu. Maa na ciki?" "Yep" "To muje ka rakani." Suna shiga ciki Waheedah tabi bayan su. Itama bakin ta dauke da sallama Haj Hameedah na zaune akan kujera tana rubuta sunaye. Hannunta riqe sa biro da notepad. "Maa " "Naam Zayn." "Barka da safiya. " "Yauwa ... Ka tashi lapia?" "Alhamdulillah Maa. Ya aiki?" "Alhamdulillah yau ina off... Sai yamma." "Masha Allah! Allah ya temaka Amin." "Aamin Zayn ." "Waheedah zo muyi hide and seek ..." Moha ya fada yana tsalle. "Ka kyelata ta huta baby." "Ah Maa.. inaso muyi shiyasa." "Waheedah taga ta kanta." Waheedan ta nufi wajen sa. Ta kama hannun Moha suka fita waje. Zayn ya bisu da kallo. Maa tayi murmushi kafin tace, "Ai sun saba sosai. Waheedah ta zama babbar kawar sa. Kwana biyun nan na huta da fitinar sa." Ta karasa fada hade da daga kai sama tana tunani. Can ta mayar da kanta kan notepad ta cigaba da rubutu. "Maa list din menene kike yi...?* "Na bikin nan da zaai. Saboda kar na manta ban inviting wasu ba. " Kada kai yayi can ya nisa yace, "Maaa . Dama inason magana da ke..." "To ni kuma?" Ya 'daga kansa kafin yace, "Eh .." "To Allah yasa muji alkhairi....." "Aamin .." "Ina sauraron ka .." Ta ajiye biron da notepad din a gefe. Ta bashi nutsuwar ta baki daya. Zuciyar ta nata waswasi akan zancen da zai fada... Ta kasa gano koma menene..Don tabbas ta lura baya hayyacin sa. A hankali kuma a nutse yace da ita, "Maaaa... Dan Allah a fasa auren nan." Shiru tayi tana nazarin sa. Can ta nisa kafin ta bashi amsar maganar sa, "Kai ma kasan abune mai wahalar yiwuwa. Wanda ba zaa fasa a kan ka ba. You know that, don't you?" "Yeah I know right Maa. But ku duba zancena pls . Infact ba wanda na samu akan zancen nan sai ke " "Eh saboda ni ce marainiyar wayon ka ko? " Dariya ya kyalkyale da ita kafin yace, "Maa gaba daya kin koma cikakkiyar bahaushiya wallahi " Itama murmushin tayi kawai ta gyara zaman gilashin fuskar ta. "Eh inada gaskia. Meyasa ba ka samu Wanda suke a samana ba? " "Allah, Maa naje har sashen Abiey na kasa gaya masa. Dama kune options dina shi da kuma ke. Nasan idan na gaya miki zaki sanar masa. Shi kuma ya gayawa Ummimi. Please " "Toh ai Zayn. Zancen da kazo da shi kasan ko ni bazan amince da shi ba. Ballantana naje har wajen Abiey dinku na same shi da maganar. Ka zauna kayi tunani. Dangi na kusa dana nesa sun fara hallara saboda taron bikin ku ba? Kai kadai zaa yiwa auren ko kuwa sauran duk suna raayi ne? Tambayar ka na ke?" Ya girgiza kansa kawai yana sauke zuciya. "Maa ban gama fuskantar Ahlam ba." "Yo kai ai ko gaba daya lokacin zaa baka ba zaka amince ku fuskanci juna ba. Yarinyar da gaba daya bata gaban ka. Kullum ranka a hade kana muzurai tamkar wani shugabanmu. Kama dauke maganar nan. Maganin kar ayi kada a so ma kaji na gaya maka." Ya saka hannu ya shafo keyar sa da saman goshin sa. "Maa. Yarinyar nan is too lazy wallahi. Gashi ta baci da kashe kudi. Beside idanunta sun bude Maa. I can't stand her. Ita smooching a wajenta ba wani abu bane...." Haj Hameedah ta karasa sauraron sa. Can tace, "Toh idan ka aureta sai ka tankwarata. Kayi kokarin nuna mata dai dai da akasin haka. Ka mata wa'azi da jan kunne akan haramcin
Chapter 25 · 0% Book details