← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 82

Sashe 80

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce Astagfirullahi.... Wani bai isa yayi wa wani wani abun ba. Ba tare da Allah ya rubuto haka kaddarar sa zata kasance ba.... Kuma in dai Hadiza dai kike nufi wacce ke wajen haulatu yayar ta. Matar Nalado ta fari. Maganar gaskiya ba zata aikata mugun abu ba... Dukkanin abubuwan da kike fada ya shafeta haka zalika kema ya shafeki Iya. Yaranta sunada ciwon sikila. Diyar ta ya macen kuma bata gani sai da temakon gilashi. Haka zalika ke kika sanyaa Nalado ya rabu da ita..Yaran nan nata jikoki ne agare ki Marka. Ko ba komai itama uwar 'yayan dan cikin ki ce. "Kada ma ki sake cewa wani ya tozarta miki rayuwa ta hanyar sanya miki ciwo ko gurbata rayuwar ahalin ki. Wannan ba dai dai ba ne. Baki imani da kaddara ba Iya. Babu hutu da kwanciyar hankali ga bawa a wannan rayuwa ta duniya sai yayi imani da qaddarar Allah. Wato ya sakankance cewa duk abinda Allah ya qaddara mai aukuwa ne, kuma abinda be so faruwar sa ba, to haqiqa bazai faru ba. Haka kuma lallai al'umma da zata taru gaba daya domin ta cutar da bawa da wani abu, to ba zasu iya ba sai dai da abinda Allah ya rubuta zai same shi. Hakanan da zasu hadu domin su amfanar dashi, ba zasu iya ba face da abinda Allah ya rubuta. anar Imani da Qaddara: Imani da qaddara na nufin yarda tare da gaskatawa cewa, babu wani alhairi ko sharrai da zai sami dan Adam face bisa qudura da hukunci na Allah Madaukakin Sarki. Sarki ne kuma shi, da yake aikata abin duk da ya so; ba abin da zai iya kasancewa, face da sani, da kuma yardarsa. Babu kuma wani abu a faadin duniyar nan, da yake wajen qarfin ikonsa, Madaukakin sarki ta fuskar samuwa ko rashi; shi yake samarwa da sarrafa shi. Amma, tattare da haka, ya shimfidaa wa bayinsa wasu umarce-umarce da hane-hane, wadanda a cikinsu, ya ba su cikakkiyar damar tsare alfarmarsu ko tozarta ta; babu wanda zai tilasta su. Iyakar abin da yake wurin shi ne, al amurran za su ci gaba da gudana ne gwargwadon iko da zabin ransu. Amma, yana da kyau a sani cewa, da su bayin nasa, da wannan dama da iko da suke da su, duk Allah Madaukakin Sarki ne ya halicce su. Saboda haka duk wanda ya shiriya daga cikinsu, rahama da jinqai ne, na Allah ya sauka gare shi. Haka kuma duk wanda ya bace, hikimarsa ce Madaukakin Sarki, ta tabbatar da haka. Babu kuma wanda ya isa ya tambaye shi dalili a kan haka. Amma, baya gare shi subhanahu wa ta alah, kowa abin tambaya ne. "Iya, Imanin nan kuma da iko da qudura irin na Allah Madaukakin Sarki, Daya ne daga cikin rukunnan imani, kamar yadda jawabin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya bayyana a lokacin da mala ika Jibrilu ya tambaye shi a kan abin da imani ya qunsa. Sai ya karba masa da cewa: Shi ne ka yi imani da Allah, da Mala ikunsa, da littafansa, da Manzanninsa, da Ranar Qarshe. Ka kuma yi imani da qaddara ta alhairi da ta sharri. [Muslim:8] "Ina fatan wannan dan karin haske daga cikin dan ilimin da na sani zaki duba agare shi. Ki kuma tabbatar wa kan ki da bawa baya tsallake kaddarar da Allah ya ketara masa. Imani da ita kawai zaki. Ki karba da hannu dubu. Sai Allah ya dube ki da idanun rahama ya kawowa rayuwar ki sauki... Kar Allah ya karbi ranki acikin wannan yanayin da kike ciki. Kinsan kuma Allah baya yafe zaluncin da kayiwa bawan sa. Hakanan kuma adduar wanda aka zalunta batada hijabi ga Allah .. Ki roki dukkanin wadanda kika aibata wa rayuwa ko kika zalunta. Ko Allah zai dube ki da rahamar sa. Ya sassauta maki halin da kike ciki." Hawaye suka shiga zurara daga idanun Marka.. "Allah na tuba Astagfirullahi... Ka yafe ni. Allah na karbu kaddara tah. Allah kasa hakanne mafificin alkhairi agare ni da iyali na baki daya .. Deluwa, Mai sunan Malam, Zahara'u da ma su zabba'u dan Allah dukkanin ku ku yafe mun .. " "San samu gaba daya ahalin na ki su taru waje daya. Ki nemi gafarar su. dukkanin su manya da kankana... Kinji ko?" "Insha Allahu malam... Amman bana jin zasu yafe mun. Na aikata abubuwa marasa dadi " "Zasu yafe miki insha Allahu... Domin Allah ma kullum cikin yi masa laifuka muke. Kuma idan muka roke shi yana yafe mana. Ballantana mutum dan Adam. Insha Allahu dukkanin su zasu yafe miki... Allah ya yafe mana baki daya." "Aamin Yaa rabbi." "Aamin.." "Sai ku tsayar da rana nan kusa ku tara iyalan baki daya. Insha Allah nima zan zo don tausasar harsuka. Allah ya ara mana rana yasa muna da rabon haduwa." "Amin malam. Nagode Allah ya saka da alkhairi. Ya kara lafiya." "Amin Amin tare da ke da sauran baki daya.." Yayi musu sallama ya tafi. Bayan ya kara jawa zahara'u kunne ya tsawatar hadi da mata fada sosai akan muhimmancin girmama iyaye da tausasar harshe idan zaa yi musu magana. Ya kuma saka ta bawa Marka hakuri hade da neman yafiyar ta. Malam na lado ya shige gaba yayi masa rakiya... Marka nata tsiyayar hawaye. Idan ta kallo yaran Deluwa marasa lafiya da daya makauniya. Ga tulin yaran Adamushe ga biyu na wajen Na'Ateeku masu dauke da cutar amosanin jini. Ta sake fashewa da kuka. Ganin dukkanin aibatawar da takewa yaran Hadiza . Gashinan nata ma sun samu. Gaba da baya kowanne na da irin na sa ciwon. Ga ita kanta data zama jangwam sai dai a kwantas a tayas. Gefe daya zahara'u na rera nata kukan. Baki dayan su dai zukatan su ba dadi. Damuwa ta taru ta tumbatsa ta kuma gauraye ilahirin jini da tsokar su Basu da wani sauran FARIN CIKIN ZUCIYAH.. To dama hakan abun ya ke. Idan kana yiwa kaddarar wani dariya. Sai Allah ya jarabceka da irin ta ko ya ninka maka fiye da ita. Wani tun a doron duniya yake fara ganin hukuncin Allah akan sa. Shi yasa duniyar nan kayi me kyau. Ka kyautata mu'amalar ka da kowa. Kada ka zama silar da wani zai kai kukan sa wajen Allah akan ka... Allah ya raba mu da mummunar kaddara. Yasa mu wanye kalau. Allah ka kare zukatan mu da gangar jikin mu wajen fadawa kogin aikata haramun. Ka nesanta mu da haramun ka kuma kusanta mu da aikata mekyau cikin halaliyar ka me dimbin rahama... Domin kai din mubuwayi ne gagara misali.. Allahumma Aamin. IYALAN MALAM NA LADO ME IGIYA Bayan sati da faruwar mutuwar auren zahara'u. Kuma wanda yayi dai dai da lokacin da Marka ta saka wanda zasu hallara da ahalin ta baki daya don neman gafarar su da yafiyar juna baki daya. ... Hakan kuwa akayi. Ranar dukkanin su kwan su da kwarkwatar su sun taru a tsukukun gidan na Marka. Ciki harda Umma Hadiza da nata iyalan su biyu. Waheedah da Najib. Duk wanda ya dora idanun sa akan Umma Hadiza da iyalanta sai ya sake mayarwa ya dube su. Gamin yadda suka yi bulbul da su. Fatar su na sheki, Gefe daya da nutsuwar zuciya. Musanman Waheedah da tayi wani irin fresh tamkar a tsaga jikinta jini ya fito. Sanye cikin kayan alfarma. Kana ganinta kasan ta samu gidan hutu da wadatar zuciya. Dubada yadda komai na jikinta mai kyau ne da tsada. Wai ahakan ma bata kure adakar ta ba. Tayi saisa saisa. Gudun kada suyi ta yada maganganun ta zama yar karya da sauran su. Bata zo hannu biyu ba. Ruwa leda leda na pure water. Sannan na cartons cartons na roba da lemo. Gefe daya ga kayan abinci buhun shinkafa ta dafawa data tuwo , Da kayan shayi da jarkar mai. Wannan kayan abincin Haj Hameedah ce ta bata tace ta kai gidan su. Baki daya sai aka yayyabe ta. Kowa na yabawa da alkhairin da tayi. Marka tsabar dimaucewa kuka kawai take. Ganin wadanda ta muzantawa a rayuwa a baya. Sune a yanzun suke temakon ta da karfin su da gumin su da kuma aljihun su. Hawaye take tsiyayar wa sosai na nadama... Hakika tayi dana sani da abubuwan da ta aikata a baya... Zuwan malam me carbi ba dadewa ... Ya bude taron da addu'oi sosai. Sannan ya shiga yin wa'azi mai ratsa jiki da fadakarwa ga dukkanin su yan wajen baki daya .... Daga bisani kuma ya bawa malam na lado dama shima ya fara tasa maganar. Daga karshe ya shiga neman yafiya da afuwa ga dukkanin su. Da su yafe masa akan dukkanin abubuwan da ya aikata wa kowannen su na bacin rai akan sani da na rashin sani ... Bayan ya gama nasa bayanin. Marka ta karba. Muryar ta na rawa da kakkarwa. Idanuwan ta taf da ruwan hawaye. Ta shiga bawa daya bayan dayan su hakuri akan dukkanin muzgunawa da tayiyyi musu. Hususan (musanman) Umma Hadiza da ahalin tah. Marka ta sake fashewa da kuka... Hakuri sosai take basu. Numfashin ta na fuzga. Neman yafiyar su ta ke. Nadama sosai take yi. Ji take dama a tariyo baya . Ta goge halayen da ta aikata ta musanya wa kowannen su da alkhairi .. Wasu daga cikin su hawayen suma suka fara, Musanman Umma Hadiza, Waheedah, Najib, Nalado, inna Sa'adatu da kuma Deluwa. "Yanzu ba gashinan ba ? Na girbi abunda na shuka. Duk wasu sharruka dana aikata daya bayan daya sun dawo mun. Daman ance sharri dan aike ne. Duk inda ya zaga ya zagaye da aiken da ka yi ma sa. Sai ya dawo gare ka ko ga wanin ka.. Dukkanin mugayen alkaba'en dana dinga yi wa Hadiza da yaranta yanzun ba gashi nan ba. Sun dawo gare ni da na wa yaran da jikokin? Ciwon da nake musu dariya ina zunde gashi nan akan nawa jikokin na wajen Zahara'u. Makantar Wahidin... Au Waheedah da na ke aibata gashi nan Deluwa ta haifo yara daya makauniya ce. Baki daya ma ita bata gani kwata kwata. Sakin da na saka mai sunan Malam ya yiwa Hadiza gashi nan an sako tawa 'yar har sau biyu. Yara kuma dukkanin mazajen sunce basa ra'ayin su. Jikar da na fi kauna
Chapter 80 · 0% Book details