Sashe 4
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
marka, "Duk abunda kika fada hakan yake Marka, Ban musa ki ba. Na kuma san kauna ce tasa kikeson ki hada auren nasu. Sai dai abunda nakeson cewa shine, Na'Ateeku yayiwa Waheedah girma Marka. Wallahi zaa cuceta idan har aka aura mata shi. Dansa na biyu Hashimu fa satin baya ya kara aure. Mata ta 3. " "Sai akayi ya ya? Ai dan arziki shi yasan abun arziki. Yadda matan sukayi yawa ai dama kamata yayi maza su ringa aure su , Su cike gurbi. " Najan Isubu ta sake gyada kai kafin ta zauna daga gefen Marka. "Marka.... Rayuwar auren daa da yanzu ba daya bane. Tamkar yadda kukayi rayuwar auren ku da tamu wallahi ba daya bane. Hakama yanzu wannan zamanin ba a irin auren nan Marka. Zamani yazo da sauyi." "Ni fa ban gane abunda kike nufi ba Najaatu. Gwara ma ki dena 'babaatu. Ahto!" Ta karasa hade da nanawa cinyarta duka. "Abun nufi yanzu zamani ya kara wayar da mu. Ciwukan yanzu a baya baa yi su ba. " "Uhmm Hu'uhm..." Marka ta numfasa tana gatsine gatsine. "Allah Marka. Na'Ateeku bakiga yana da yara hudu ba marasa lapia shima.?" "Bangane ba.. Yo sai me? Ba Allah ne ya doran su ba. Ina ruwan auren su da wahidin ya hadu da gamayyar rashin lapiar yaran sa?." "Ina nufin Na'Ateeku a dauke zancen ya haifeta da sauran su. Abunda nakeson ce miki shine. Shi ma Na'Ateekun yana dauke da kwayoyin cutar sikila. Kamar dai yadda su Kamalu da Najeeb ke fama da ita." Marka taja dogon tsaki data saurari karshen zancen Najaatu. Cikin takaici tace, "Banji ba, Ban kuma gani ba. Karki manta da sherri dan aike ne, Dik inda yaje zai dawowa mai shi... Sannan ni me sunan Malam (Na lado) Bayada wata cuta.. Domin idan da yana da ita da yaran wajen sa'adatu ba sa yi lapia ba. Ita kuwa uhm uhm Hadiza, Da cutar ta tayi guzuri. Aka liqa masa ita ya aure. Ashe lullube maganar cutar jikinta sukayi. ." "Kayya Marka ki dena cewa haka dan Allah .. Banda ishasshen ilimin da zan buda miki komai yadda yake. Amman Allah ya kai mu sati na sama. Wata kungiyar wayar da kan jamaa kan hanyar da zaa kula kar a fada halin qaqanikayi na ciwon sikila zasuyi taro. Da yardar Allah kuma dukkanin mu zamuje. Saboda har gwajin jini za'a yi ko kanada cutar duk zaa sanar maka. Hakama idan baka da ita." "Kingama?" "Kiyi hakuri Marka." "Baki gama ba kenan. To kici gaba idan kin gama se ki tashi ki koma inda kika fito." "Kiyi hakuri Marka. Ni kawai so nake ki janye zancen ki..." "Aure babu fashi..." "Nalado ka sa baki dan Allah. " Najaatu ta dubi nalado dake gefe yana katsar ruwan dake kasan tukunya na taliya. "Me zance Naja..?" Ya amsa ta hadi da lashe bayan hannun sa. "Yanzu ba zaka tausashi zuciyar marka ba ta janye zancen nan? Haba dan Allah." Malam Nalado yayi shiru bai ce komai ba. "Aure babu fashi. Yace dama inde zuciyar sa ta aminta da ita. To fa ko kayan daki yace shi zai yi. Ita kadai za a wanke akai. Saboda Allah meya fi wannan karamci? Na'Ateeku kyakkyawa da shi , Sambalele jazur da shi . Kina ganin matansa kowacce da kayanta maya maya. Sunyi 'bundun da su.. wallahi ance ba yunwa agidan sa. Duk sallah sai ya dinkawa matan sa turame maya maya. " Waheedah dake labe tana sauraron komai. Kasa jurewa tayi. Dan kukan da take rikewa ne ya kufce mata ya shigaa sharara a idanunta. Cikin rawar jiki da baki ta fita tsakar gidan. Ta sukwane agaban Marka tana faman rokonta. "Dan Allah Marka kiyi hakuri. Ki barni na cigaba da karatu na. So nake na zama ma aikaciyar lapia Marka. So nake na bawa harkar lapia gudunmawa Marka. Dan Allah kar ki mun aure ki bari na cika burina. " Ta karasa hade da riko kafafun Marka. Hawaye sai dalala yake daga idanunta. "Matsa kafin na hamb'are ki. Me sunan Malam kana jin maganganun da tsageriyar yarinyar nan take faada....? a. Ke yanzu Waheedah Markan kike gayawa haka?Uhm tab. Lalle. Kokari." Cewar Inna Sa'adatu matar Nalado ta biyu, Mahaifiyar su Zainab da su ke uba d aya da su waheedah #FARHATAL QALB #FARIN CIKIN ZUCIYA #ZAFAFABIYAR2022 *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:00 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _LAST FREE PAGE: 5_ _(SHAFIN KARSHE NA KYAUTA!)_ "Haba Sa'adatu, Wannan ba girman ki ba ne wallahi." Najan Isubu , Ta fadawa Inna Sa'adatu haka. "Yo ai gaskia ta fada.. Me sunan Malam kana jinta ko kayi kunnen uwar watsi?" "Kiyi hakuri Marka... Ke waheeda baa ta hakuri." Malam NaLado ya tsawatar wa Waheedah. Ita dai Umma Hadiza bata ce komai ba. Tayi zugum a gefe kanta a kasa. "Ummaaa kafaata, Umma kafata. Kafata ummah ..Wayyo, wayyo " Najibu ya shigaa maimaitawa yana mai dartse hakoran sa Marka taja tsaki, Umma hadiza ta miqe da sauri ta koma cikin daki wajen su Najib. "Haba wannan wahala har ina? Ga wannan ga wannan. Gaskia da sake " Marka ta fada tana mai hararo dakin su Najibu "Kai Marka ki dena cewa haka. " "Kinga Naja ki fita idanu na. Ni dama tun da na kyalla ido na hango shigowar ki, Nasan tabbas wani katsalandan dinne ya kawo ki.." "Kiyi hakuri Marka. Da yardar Allah komai ya kusa wucewa. Lokaci ne, Idan Allah ya nuna mana wucewar da sai kiga tamkar ba'ayi wannan tashin tashinar ba." Naja ta karasa fada idanuwanta akan Marka dake faman cin magani. Can ta sake sakin wani dogon tsaki tana karkada kafafu. Cikin kufulewa tace, "Kin isheni da zubar lallami Najaatu. Har kina wani lankwashe kai kina jin haushin Sa'adatu. Yo ai gaskia Sa'adatu ta fadi. Yaran Sa'adatu babu abunda zamu ce da su agidan nan sai san barka da fatan samun nasarar Allah akan dukkanin lamuran su. Zainab da suke kusan sa'anni daya da wahidin ne sau uku mai nemanta ya kawo mana kayan abinci ga su nan idan karya nayi." "Zancen ki haka yake Marka. Domin wainar yar tsalan jiya ma zainab ce ta sayo." Cewar Sa'adatu hade da kecewa da dariya. "Wannan duk ba abun damuwa bane Marka.." "Babbar damuwa kuwa Naja. Natsani safiya tayi dare ya maye idanuna su sake dora ganin su akan Hadiza da ahalinta. " "Kash. Assha Marka. Ki bar cewa haka. Babu fa bawan da ya tsara rayuwar sa haka fyace wadda Allah ya rubuta. Kuma menene yan uwantakan da zumuncin idan har dan uwanka baya kyautata maka?" "Ke Naja. Duk abubuwan da zaki fada ba tasiri zai yi a zuciyata ba don in gaya miki..." "Kibar cewa haka Marka..." "Dole na fada. Kinga wuya. Nan inda abu ya tokare mun yaki tafiya. ? Ba komai bane fyace bakin cikin da Hadiza da yaranta suke samun. Nagaji idan da gaban gajiya nayi..." "Ya SubhanAllah! Ki dubi girman Allah Marka ki dena cewa haka, Dukkanin yaran nan fa jikokine. Haka kuma Allah yaso acikin jikokin naki zaa samu biyu marasa lapia " "Marasa lapia? Nakasassu zaki ce. Masu tattare da kunci da 'dacin rayuwa." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Marka!! Marka!! Ki dena cewa haka. Malam ka saka baki. Wannan ba dede bane." "Ba ze saka ba Najaatu. Idan kin gaji da ji ki tattara ki fice mana daga gidah ." "Kiyi hakuri Marka. Kawai dai gani nayi wannan maganganun dik basu taso ba." "Dole ne ayita . Shi ya saka nace wallahi kwayar hatsi nawa hadiza dasu Najib ba zasu sake ci ba. Su dan kinibibi sunyi shabe shabe ga nakasassu da baza su fita su nemo ba. Ita kuma uwar tasu ta daure musu gaba ba zata tursasu ba. Kullum dan tsagwarar munafurci suna daka suna sakin numfarfashi. Ita kuma ta faake kullum tana gefen su ba zata fito cikin mata tayi shiqa ba ta samu kudin batarwa. Ragowar me lapiar kuma ta tsiri boko ba kakkautawa. Ba zeyiwu ba wallahi. Su tunda maza ne suje can su karata ita kuma tinda macece dole ne a aurar da ita. Baqin jini ya mata katutu maza basa zuwa. An samu kuma Na'Ateeku yace yaji ya gani zai aure akan wane dalili zamu fasa? Bayan idan ta aure shi kakarmu ta yanke sa'a . Ita kanta Hadizan sai tafu jin nutsuwa da kwanciyar hankali... Wahala zata ragu. "Marka ta karasa fada tana gyade kai. Najan isubu ta numfasa kafin tace, "Kowane bawa da yadda Allah ya kadarta masa rayuwar sa, Wala dadi wala akasin haka. Rayuwar hadiza da yaranta haka Allah ya rubuta mata tata jarabawar. Sai dai fatan Allah yaba su ikon cinyewa yasa jinkirin alkhairi ne Aamin . Zancen nauyin dake kanta da yardar Allah yazo karshe. Domin na samo mata aikin wankau da yan kaude kaude a layin manyan can na shurah. Saboda haka zata sauke nauyin wasu abubuwan . Haka zalika itama Waheedan akwai abunda zaa sama mata ta dingayi bayan su Najeebu sun ji saukin jikin su. Don haka Marka ki ajiye zancen Na'Ateeku agefe yanzu." "Na ajiye na zuba mata idanu ina kallonta? Ba dan mashinshini a kusa sai zuryar boko? To bokon yaci uwatas."