Sashe 64
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tashin kamshin da kofofin hancin sa basa mantawa. "Please Waheedah .. Kyale ni naji dumin jikin ki . Ko kinsan wata rana da muka fara haduwa da ke? A gate din gidan mu. Wanda muka bigi juna har glasses dinki suka cire?" Yana mai goga karan hancin sa akan nata karan hancin ya cigaba da cewa, "Tun ranar na tsinci kai na da kaunar ki. Kamshin turaren ki. Idanun ki, kyawun ki, nutsuwar ki, kyakkyawar halayyar ki da ma sauran dimbin ladubban ki suka kara ingiza zuciyata da kaunar ki .. Waheedah ke ce FARHATAL QALB na..I remember every second, Your magnificent smell, Your incredible eyes, I remember everything... You are my best present and future Waheedah.. Tun kallon farko ..I always liked you at first glance... Ki sake bamu dama Waheedah. Karki bari a raba auren mu..If only you could give us one more chance" Kiciniyar kwace kanta take son yi. Zayn yayi nasarar saka bakin sa ya sumbaci gefen wuyan ta. Ta rufe idanunta da sauri jikin ta na ta rawa. Ya busa mata iskar bakin sa a kunnen ta ahankali cikin wata iriyar murya ya shiga rada mata, "If only you could give us one more chance.... " Yana karasa fada ya samu kansa da saka hannu ya tallabo fuskar ta, Ya sanya labban sa akan nata. Cikin wani irin yanayi ya shiga sumbatar Waheedah. A hankali kuma cikin nutsuwa, "What did you hear.....uhm... Me kika ji, ?" Ta sauke numfashi tana kauda fuska. Ashe dan iska ne? Saboda ya kyaleta tace, "Naji...." "No... in english please ..." "I hear voices of children ...." Ta amsa shi hade da juyawa kadan ta kalli yaran da ke gara taya a tsallaken kwata suna musu ... "And then....?" "Kukan dabbobi da tururin numfashin..... "In English .... Kinji?" Ya karasa fada yana sinsinar bayan kunnenta.. "Crying of animals...And the hint of your breath...." Rarumota yayi ya rungumeta tsam a jikin sa. "Ina kaunar ki Waheedah.. I m in love with you..I love you more than anyone, Fiye da kowa da komai... Meyasa kike son a raba auren mu? Meyasa kike tsane ni haka?..." "Ka bari ... Ya Ahlam..." Ta shiga zame jikin ta. Tunowa da Ahlam da tayi, "U're worried about Ahlam... Yeah I knw..But what about us?what about my love for you? Kinsan irin kaunar da na ke miki Waheedah? Bansan so ba sai akan ki. Bansan tacacciyar kauna ba sai da na fara dakon soyayyar ki Waheedah.. " Yana magana yana sake matseta a jikin sa. Ganin zai iya nasara akanta. Hakan ya sa da sauri ta yage jikin ta daga nasa ta shige gidah. Sun bar tsakar gidan suna dakin gwaggo haule. Don haka fitsari tayi kawai da alwala ta kwanta tana tunano Zayn da ajiye kunyar da yayi a gefe yau. Ta dora hannunta daya akan lebenta tana zagaye su. A haka bacci ya kwashe ta... Wasa wasa sai da Waheedah ta kara kwana biyar agidan su kafin Haj Hameedah ta turo a dauketa da kayanta. Daki wadatacce aka bata asaman gidan na Haj Hameedah kafin komai ya sake sararawa Waheedah ta koma gidan Zayn. Duk sanda zai zo wasan buya suke. Bata bari su hadu. Ranar daya gaji ya kirata a waya taki dagawa. Ya tura mata sako da, "I'm in the car..." Ta karanta tayi shiru. Ya sake tura mata da, "Come down! I won't accept no.or I will alert the whole neighborhood .." Tana karasa karantawa ta kashe wayar baki daya. Zayn ya shiga gidan kan sa tsaye. Yayi hamdala Maa bata nan tana sashen Abiey din su. Da sauri ya haye saman dakin da Waheedah take ya tura kofar ya shiga ya murza mata mukulli. Nufar ta yayi gadan gadan ta gudu bayan kofa ta tokare tana rau rau da idanu, Yayi murmushin gefen fuska kafin yace, "Waheedah you made a big impression on me .." "Ya a Zayn..., Dan Allah ka bari.." Girgiza kai yayi. Tana baya baya yana kara matsawa kusa da ita. Ta rakube a karshen kofar tamkar zata shige cikinta baki daya. Tana mai rufe bakinta da tafukan hannayenta. Cikin rawar baki ta shiga cewa, "Sis Ahlam......" "Shhhhhh!!! I love you more than anyone .. Enta FARHATAL -QALB. . yes Waheedah ke ce FARIN CIKIN ZUCIYA tahhh..#ItWasAlwaysYouW ..." Yana karasa fada ya saka hannun sa yana sharce mata hawayen da ke tsiyaya a fuskar ta... Kafin ya samu kansa da tallabo bakin nata. Ya shiga bata deep and passionate sumba mai ratsa mugudanar jini da bargo.. Yayi nasarar kashe mata lakar jikin ta. Daga shi har ita sun shagala sai bugun kofa suka ji. "Waheedah kinyi bacci ne?" Suka jiyo muryar Maa. Waheedah ta tattake iya karfin ta ta ja hannun Zayn ta tura shi abandaki. Ta rufe bandakin da mukulli gabanta na tsananta bugawa. Kunya duk ta dubibiyeta tamkar Maa din na ganin su. Ta kalli kanta a mudubi gaba daya ko ina a hautsine. Ta juya ta dankarawa kofar bandakin harara sai kace Zayn din yana gani. Tayi sauri ta gyara ko'ina sannan ta bude kofar. Maa ta shigo tayi hanyar bandakin tana, "Ashe shower ta lalace sai Nadra ke fada. Haka kiketa wanka da sanyin nan Waheedah? Bari na dau hotan wajen na turawa me gyara sai ya sayo abunda babu..." Tamkar mota haka Waheedah taja kafafuwa a guje sai gata agaban Maa. "Ki..ki..ki barshi Maa." Maa din ta kalleta tayi murmushi, "Haba Waheedah? Dan Allah ki cire wannan kunyar ai an riga da an zama daya.." Waheedah ta shiga girgiza kai. Tamkar zata fashe da kuka. Yayin da Zayn dake ciki yanata murmushi da adduar Allah yasa Maa ta bude ta ganshi ta bashi matar sa. "Akwai ... Shan..." Ta kasa karasawa tanata rawar murya. Maa ta yi murmushi kafin cikin kulawa tace, "Okay ko kin wanke undies ne bakyaso agani? Well kina da gaskia. Ba damuwa zuwa da safe sai ya zo kawai ya gyara. Idan zaki wankan to dan Allah ki fada a kawo miki ruwan zafi ko ki shiga bandakin Nadra . Kinji?" "Insha Allah Maa. Nagode kwarai." "Yauwa... Sai da safe." Tana fita Waheedah ta sauke zuciya. Hannunta akan kirjinta. Yau da Maa ta yi ido biyu da Zayn batasan wacce iriyar kalar kunya ce zata shiga tsakanin su da Maa din ba.... #DESTINED LOVE... #ZAYNUL-WAHEEDAH.. #ITWASALWAYSYOU:W _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:61_ *Gefen* gado taje ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya, tana sane taki sanar dashi cewar Maa ta tafi yayi ta zama a bathroom in ita ba ruwanta. Kafin ta gama zancen zucin da takeyi kawai taga ya fito sukai ido hudu, ta janye nata gefe tana cizon farcen yatsanta. A hankali ya karasa inda take zaune ya tsaye yana kare mata kallo. Shikam me zai yiwa wannan baiwar Allahn ta yadda cewar shi din yana sonta da gaske ba wai wasa ba? Me zai mata ya tabbatar mata da cewa be aureta dan ya cusgunawa Ahlam ba? Muryarta yaji tana cewa. "Yah Zayn zaka danneni fa.." Zayn ya kalleta, gani yai sauran kiris ta fada kan gadon. Maimakon ya matsa sai ya dora kafarsa daya a gefen gadon, Waheedah ta zaro ido, d'an rankwafawa yai ya sata a tsakiyarsa kamar mai san yi mata rada. "Please Ya Zayn bana so." Ga mamakinta sai taga ya sake rankwafawa kawai sai ta kwanta akan gadon tare da kauda fuska cikin ranta tana fadin kaci kanka. "Oh Masha Allah dan naga kin fiso muyi maganar a kwance ko?" Bata kulashi ba saboda bata san hirar tasu tayi tsayo, so kawai take yabar mata dakin amma bashi da niyar yin hakan. Ji kawai tayi ya kwanta a bayanta tare da rikota ta hanyar sanya hannu ya riko shafaffen cikinta. Waheedah tayi saurin zaro ido kirjinta yana wani irin bugawa, gani kawai take Ahlam tana kallan irin cin amanar da suke yi mata. Idanuwanta a lumshe sakamakon wani irin yanayi da ta tsinci kanta, murya na sarkewa take fa "Yah Zayn k..." Tattausan tafin hannunsa taji a saman lebenta, ji tayi yana kokarin juyo da ita wajansa, da sauri ta tirje tana girgiza kai. "Yah Zayn bazan iya ba, dan Allah kadena tabani bazan iya wannan cin.." Zayn ya sake katse mata hanzari ta yadda yake goga mata dogon hancinsa da tattausan lips dinsa akan fatar wuyanta, gabaki daya numfashinsa dake fitowa ta hanci da lallausan gashin daya kaawata wajan bakinsa zuwa habarsa sai sake kashe mata jiki suke, banda tsuke kafafuwa babu abinda takeyi. Zayn ya dan rintsa ido yana girgiza kai, husky voice dinsa ne ya daki cikin kunnanta inda yake cewa. "FARIN CIKIN ZUCIYA tah (My Farhatul qalb) kina tunanin na aureki ne dan wata manufa tawa akanki ko akan Ahlam?" Waheeda tayi shiru ta kasa cewa komai, Zayn ya dan saki murmushi tare da janyota, gabaki daya sai ta juya suka fara kallan juna tayi saurin rufe ido. Bazata iya kura masa ido sosai ba saboda wasu sirrika dake cikinsu, ya hadiye wani mugun saliva wanda tsagwaran san ya mallaki lips din ta dake ta faman motsawa tamkar wata mai shan sweet. Yaci gaba da cewa. "Ki cire tsoro da duk wata shakka da kike yiwa Ahlam kizo kiyi biyayyar aure, na dade ina jiranki, zuciyata ta jima a cikin so da kaunarki, ki tausaya min ki shigo cikin rayuwata ko zan samu jin dadi da kwanciyar hankali." Ya karasa maganar yana shigar da fuskarsa gefen wuyanta. Wasu hawaye ne suka dinga bin kyakkyawar fuskar Waheedah, ta shiga girgiza kai tana zamewa daga jikinsa, ganin ya hanata yasa ta fashewa da kuka, Zayn ya rintsa ido kukan ta yana jinsa har cikin ransa, ba zai iya jurewa ba dan haka yai saurin matsawa daga jikinta, muryarsa tana sarkewa yace. "Ki gaya min abinda kike so nayi wanda zai sa ki kasance a cikin rayuwata ta har abada, sanar dani please but banda saki bana san jin kalmar nan daga cikin bakinki." Yadda Waheedah taji yayi maganar ne yasa kirjinta