Sashe 48
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka zaman na su ya cigaba da kasancewa. Sam lamarin Ahlam kara bunkasa yake babu gyara aciki . Har yau bata abinci. Ragamar gyaren gidan ta bai wa almajirai. Kullum ba kyakkyawar shiga sai kayan bacci. Safe rana dare tana kan kujera ko gado a kwance. Kullum tana kan Whatsapp tana chatting da kawayen ta. Babu wani saurin hakki na miji da ke kanta da takeyi dai dai. Sam sam ba bu. Hakan ya kasance har the Adams family sun fara lura da zamantakewar Zayn da Ahlam. Manya sun tsawatar amman lamarin yaci tura. Zayn bai karasa hasala da lamarin Ahlam ba. Sai da idanuwan sa sukayi masa tozali da contraceptive pills (maganin hana daukar ciki) din da Ahlam ke sha. Kwali biyu ta gama da daya. Daya kuma sauran rabi ta karasa shanye kwalin duka. Tsabar tsagwarar bacin rai har kuka Zayn yayi. Na ganin kullum ya kan hana idanun sa bacci yana rokon Allah ya basu albarkacin yara su ma. Amman Ahlam ashe munafurtar sa take tana shan maganin hana daukar ciki. Ya dafe kansa da hannu biyu. Ya kuma kasa barwa kansa sanin hakan. Ya tunkari Maa yasanar mata. Nan ma manya suka sake shiga tsakanin su. Ahlam sai da tayi sati biyu tana gaba da Zayn . A cikon sati na ukun ne dakyar da digon goshi malam na lado ya amince da zaman Waheedah agidan Zayn. Bisaga hukuncin duk karshen sati asabar da lahadi zataje gidah ta kwana. Waheedah bata so hakan ba. Sam tafu kaunar gidan su duk kuwa da talakawa ne. Bata kaunar komawar ta can. Amman tunda Umman su ta amince da hakan. Batada ja. Ta hada kayanta a babban akwatin da Haj Hameedah ta bata. Ranar talata aka kaita gidan na su Zayn. Dan taya Ahlam kula da harkar gidah. Musanman abinci da sauran abubuwan da suka kamata. ... #FARHATAL QALB #FARIN CIKIN ZUCIYA #ZAFAFABIYAR2022 _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:51_ *Tsaye* take agaban dressing mirror tana mai gyara zaman rigar jikin ta ta uniform. Ta kammala duk wasu aiyuka da suka kamata. Ta zaro dubu daya daga cikin kudin motar da Haj Hameedah ta bata ta zura acikin aljihun gaban rigar ta. Ta dakko hadin madarorin turaren ta data saya masu dan yawa a babbar kwalba. (Arabian perfumed oils) ta shafe jikinta da su. Ta bude kofar dakin ta leka zuwa parlorn kasa. Tana son tayiwa Ahlam sallama kafin ta tafi makarantar. Ba kowa a parlorn . Hakan ya sa ta dubi agogon da ke wutsiyar hannun ta don kada ta makara. Ta dan sake tsayuwar ta kafadar hannun ta daya dauke da jakar ratayawar ta . Dake dauke da notebook da handouts. Shiru shiru ba motsin su . Haka ta hakura ta bude kofar gidan ta futa. "Ina kwana Baba..?" Ta tsugunna ta gayshe da baba mai gadi. "Lapia kalau 'ya ta. Makaranta za ki?" "Eh! Baba...." "Toh Allah ya kai ki a sa'a. Allah ya buda kwakwalwa yasa albarka a abunda ake karanta." "Amin!! Amin... Baba. Nagode kwarai." Ta karasa fada fuskar ta ta fad'aad'a da farin cikin adduoin da yayi mata. Ta fuce daga gidan tana sa masa albarka itama. Da ke babu nisa da unguwar su. Nan da nan ta haye adaidaita sahu ya kai ta zuwa unguwar su. Gidan su Basira ta dauke ta su ka biyawa Fannah sannan suka nufi makarantar baki daya. "Kawata kinga yadda ki ka sake shar da ke?" Fannah ta fada tana taba kumatun Waheedah. "Ke de karyar ki bata sallah ...." Waheedah ta amsa ta tana dariya. "Allah ba karya na ke ba... Ko ba haka ba Basira?" "Zancen ki haka yake fannah... Allah gidan nan ya karbe ki Waheedateey... Inji ya Ibrahim . " Dan murmushi kawai Waheedah tayi. Tana mai girgiza kai kawai. Haka suka karasa makaranta suna ta wasa da dariya. Tashin sa kenan. Ya waiga ya dubi alarm da ke gefen bedside drawer. Kallon lokacin yayi yana mai ware idanun sa. Da sauri ya mike ya gyara zaman bedsheet din da pillows. Ya karkade komai ya mayar da shi muhallin sa. Bandaki ya faada yayo wanka ya sauya kayan sa zuwa manyan kaya. Samfarin riga da wando wagambari kalar toka. Ya dora hula akan sa bayan ya gyara karin ta. Hancin sa ya shiga budawa sakamakon kamshin da ke dukan kofofin hancin sa. "Ahlam..... Ahlam.. Ahlam...." Ya daga murya yanata kwarara mata kira. Jin bata amsa ba. Ya feshe turare ajikin sa ya fice daga dakin bayan ya dau wayar sa. Ba kowa a parlorn sama. Don haka ya bude kofar dakin Ahlam din tana kwance. Ya dauka ma bacci ta ke. Har ya juya zai rufe mata kofar. Sai kunnuwan sa suka jiyo masa karar waka ta video Ya juya da sauri yana tunanin ko data ne a kunne tabar wayar. Ya tafi ahankali da niyyar ya dauka. Ganin ta baya ta juya masa baya ganin gaban ta. Yana lallabawa a hankali don ya dakko wayar. Idanuwan sa suka sauka akan fuskar Ahlam. Hannu biyu da wayar a hannunta ta fito da kanta da hannuwa. Yayin da sauran jikin ke cikin bargo tana kallon wani biki a Instagram sai murmushi ta ke. Can ta fita daga handle din ta koma hausaroom tana mai ci gaba da karanta sauran abubuwa tana tuntsirewa da dariya. Girgiza kai kawai yayi. Ganin tsabar shagala da kallon da takeyi sam batasan shigowar sa ba . Ya fice daga dakin ya sauka kasa Ko'ina tsaf. Kamshin turaren wuta sai tashi yake yi. Mamaki ne ya cika sa. Lalle ba su Waheedah da akayi ba karamun temako akayi musu ba. Ko'ina kamshi ne ke tashi mai sanyi da kwantar da zuciya. Ya wuce kitchen nan dinma tas. Ta jere tukwane da sauran kayan amfani duk a muhallin su. Kan dinning ya wuce. Abinci a jere a food flasks sai kamshi ne ke tashi. Ya bubbude doya soyayyiya an sakata acikin jarida saboda gumi acikin flask din Sai soyayyyen dankali da kwai da plantain. Dayar food flask din kuma sauce ce ta hanta. Da shayi a flask da yaji kayan kamshi. Bayaso yaci saboda aqidar sa ta abincin Maa din sa da yake kauna kawai. Cikin sa ne ya shiga kara . Tabbas yunwa yake ji. Don haka yayi azamar zama akan kujera ya shiga zuzzuba komai a plate iya kacin cikin sa. Ya yi basmala. Ya diba ya saka a bakin sa. Take idanuwan sa suka ware. Ji yayi tamkar abincin Maa... To ko itace ta bayar a ka kawo musu da sassafe? Ya daga kai da tabbacin hakan. Ya karasa cinyewa tas. Ya shiga bandakin da ke corridor ya kuskure bakin sa da mouthwash. Ya dauki mukullin motar sa ya fice "Ranka ya dade ... Sannu da fitowa." "Sannunmu Baba... Barka da safiya." "Barkan mu dai .. An kwan kalau?" "Lapia kalau Baba ... " Ya sosa keyar sa da kasan mukullin motar da ke hannun sa. Kafin ya sake cewa. "Ah... Na ce ba." "Eh ina sauraron ka mai gidah." "Ahh baba nace ka dinga kira da Zayn...." "Ai sunan na ka ne mai gidah ... Na yan gayu ne " Zayn ya saki murmushi kawai yace "An kawo sako daga gidan mu ne?" "Sakon me ranka ya dade?" "Sako haka na abinci .. kulolin abinci." "Yau kuma?" "Eh...." "Gaskia babu wanda ya zo. Ba re kawo sako. Tun wayewar gari na ke anan. Ba wanda ya