Sashe 40
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:44_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ *Ta* riqo butar itama. Suka shiga ja in ja... Sai data bari inna Sa'adatu ta riqe butar da karshen karfin ta. Sai ta saki riqon ita da tayi Inna saadatun ta bugu da bango. Da sauri ta dafe goshinta da hannu saboda radadin zugin da ya fara mata na zafi. Deluwa tayi murmushi tana girgiza kai . Cikin fushi inna Sa'adatu tace, "Baqar muguwa. Aniyar ki ta bi ki." "Mena miki na mugunta anan? Meye sunan ki ma? Yauwa Sa'adatu. kece muguwa.. Da kika dauki kwabin danwake na kika zubar. Wannan kazamar butar taki zan dauka nayi me da ita? Marka ce ta kawo . Kuma baa mayarda hannun kyauta baya shi ya sa ban ki ba. Na karba na ke rage wutar da ita. Sam bakya abu da hankali." "Kece bakya abu da hankali.. Shashasha." Inna saadatu ta fada tana sakin tsaki Deluwa ta taka daga inda take zuwa wajen da Inna Sa'adatu ta ke. Ta saita ta ta saki murmushi kawatacce . Sannan tace, "Da kika zubar da kwabin danwake na nace miki wani abun?" "Yo me kika isa kice? Ai kece baki da gaskiya." Deluwa ta sake shekewa da dariya wannan karon harda tafa hannuwan ta. "Duk bakaken maganganun da kike fada da sirikar ki Marka kike ba ni ba " Inna Sa'adatu taja tsaki. Fuska a murtuke tace, "Matsoraciya... Gafara can na wuce..." "Ni nasan hakki da mutuncin manya a tattare da ni. Sa'ar Marka kawai kika ci. Amman ki jira ramuwa ta. Zata baki madaukakin mamaki. " "Ke matsa can. Wai akace banza girman mahaukaci. Karamun mai wayo ya fishi... Banason sakarci. Ba kuma na bata lokaci na ga sakarkaru." "Zaki ga sakarkaru da idanun ki ... Babban labari ne da zaki raina wayon ki..." Mtssss.... Inna Sa'adatu ta sake jan dogon tsaki ta shige cikin dakin ta . Tana mai wake-wake. Ya yin da Marka ta shiga bawa Deluwa hakuri. "Laa bakomi Marka.... Karki damu dan Allah. Wannan din ba rabo bane. Ko da anci sai an amayar." "Duk da haka dai . Kiyi hakuri dan Allah. Lefi na ne." "Ya wuce Allah...." Ta tattare wajen. Ita kuma ta Deluwa ta shiga zubawa wadanda suke kaan layi da suka saya. Saura kuma ta basu hakurin kwabin danwaken ya zube. Tashin Zayn kenan daga bacci tun bayan da yayi sallar asubah. Bandaki ya shiga ya tara ruwa a kwamun wanka. Turaren wankan da mahaifiyar su Haj Hameedah ta bashi ya dauka ya zuba acikin kwamun wankon (bathtub) Tsayawa yayi yana karanta rubutun jikin robar turaren na kamfanin turarukan (yerwa incense and more). Ya shaki kamshin yana lumshe idanun sa. "Oud oudi Bath khumrah...." Ya karanta rubutun jikin robar . Wankan ya shiga yanayi. Yana karasawa ya zura bathrobe ajikin sa. Dayan hannun sa kuma yana dauke ne da karamun tawul yana mai goge kansa dashi Sannu ahankali haka ya shiga shiryawa. Ya shafa mai ya goga antiperspirant. Ya fesa turaruka kala kala. Ba kadan ba kananun kayan da ya saka sunyi matukar futo da zatin haibar kamalar sa. Domin Zayn dan gayu ne na bugawa a jarida. Gashi mekyau masha Allah. Ya yi shigar jeans da wata long sleeve shirt blue ta Armani. Hannun sa dauke da agogon Rolex da azurfa a yatsan sa daya . Kasa ya sauka bayan ya taje sumar kansa da comb. Hannun sa rike da ipad dinsa. Ya sauka kasan cikin takun kasaita na masu jini a jika . "Ahlaam.... Ahlam.... Ahlam..." Ya shiga kiranta yana sake nanata sunayenta a karo na uku. Shiru ba amsa. Ya leka kitchen bata nan ma. Dayan parlorn da ke a kusa da wani karamin garden ya nufa. Tun daga bakin kofar yake jiyo sautin maganar ta. Har zai shiga kuma sai ya fasa. Don bayaso yayi interrupting calls dinta. Juyowar da zai yi ya jiyo ta bayan ta gama kyalkyala daria "Wallahi nake gaya miki .. wallahi ke ba yadda na zata bane. Ina gaya miki ya rude sosai. Ba inda Zayn bai kissing ba a jiki na. Ya sa ka hannu z ..." Bai bari ya kara sa ji ba ya juya da sauri ya koma da baya da baya. Akan matattakar kafar bene na biyu ya zauna. Mamaki da takaici ne ya cika shi. Na jin baki daya yadda suke raya sunnah Ahlam ta kwashe tana gayawa kawarta. Komai da komai ba dadin sauraro ma. Tamkar ya tashi ya shiga ya lakada mata na jaki haka zuciyar sa ke hasaso masa. Ya danne kawai saboda abunda zai je ya dawo. Ya miqe kenan sai ga futowar ta daga parlorn. Sanye take cikin pajamas (kayan bacci) kanta ba dankwali . Sumar gashin ta yalwatacciya ta bayyana. Ta kalle shi ta sake kallon sa tana langabar da kai. "Ina zaka je haka? .. Sai wani kamshi kake " Yayi yake kawai kafin ya ce da ita, "Ba gaisuwa...?" Baki ta turo gaba. Ta koma kan wata kujera ta zauna. "Naga mun zama daya. Gida daya . Kai de kanason gaisuwar nan. Ni mantawa na ke " "To banda abinki ai dole ne ki dinga gaishe ni. Kiyi tunani mana Ahlam.. ko ba aure a tsakanin mu ai a sama nake da ke. Ni Yaya ne a gare ki kar ki manta.." "Ina kwana?" Ta gayshe da shi kasan maqoshi Bakinta ya kalla ya gano gaishe shi tayi. Bai amsa ba ya wuce kai tsaye wajen dinning. As usual ya daga tea flask ba komai aciki. Ya wuce kitchen ma kamar ko da yaushe babu abinci. Ransa ya kai kolokuwar baci. Ya danne dakyar yace da ita, "Ba abinci ...?" Ta daga kanta . Kafin tace, "Akwai bread ... Ko na dama maka custard ? " "Ahlam me na ce miki jia? Da shekaran jia wa cen? Ina ga kullum se na miki maganar nan... Amman sam kinki yi. Tun dazun me kike a k sa?" Ta sake yamutsa fuska tana turo bakinta gaba. "Ai na gaya maka..... Ka dinga hada breakfast dinki. Kai picky eater ne. " "Ahlamm... Fisabilillahi kusan kullum abincin daya ne. Indomie, sandwich , bread . Coffee. Ko fruits.. Tunda aka kawo ki gidan nan baki taba girka komai ba.." "Ina dama maka custard mana... " Ta amsa ba tare da wata damuwa ba. Yaja kasan lebensa yana taunawa. Yama rasa abun cewa. Hannun sa ya saka ya gogo kitchen cabinet sai kura. Ya nuna mata. "What is this?? Ahlam... Wannan wane irin rayuwa ce uhm? Kalli datti please." "To aiki ya mun yawa. Ance zaa bani me aiki ka hana... Zan kashe kai na da aiki ne?" Iskar bakinsa ya furzar mai matukar zafi. Cike da kosawa yace, "Ina almajiran da ke miki komai??" "Ba dai komai ba. bayan ka hana su dinga wanke duk wani plates da sauran kayan abincin dazaa zuba maka." "Lord! To Hakan shine laifi Ahlam? Nagaya miki ba sau daya ba. Ni mutumi ne me tsantsami. Alla ya sani, Bazan iya cin abinci da plates da sauran abubuwan da suka wanke ba. Almajiran dake wari suna tsami. Komai tabawa suke da hannun su basa wankewa. Haba Ahlam..wannan wane irin rayuwa ce? Mu biyu ne fa sai baba Mai gadi. Wane abu muke batawa da harsai almajiran ne zasu wanke. Just 3 of us... Haba Ahlam..." Qunqumi ta shiga yi bata sake ce masa komai ba. Ya gyada kai kawai yana girgiza shi cikin takaici. "Akwai abunda kike bukata ne da babu anan din?" "Bakomi .. sai dai ko recharge card.." "Oh ya rabb... Ni banga abunda kike da kati ba Ahlam sai renewing data plans shi yasa na yi deactivating wifi na gidan nan. Gaba daya 300gb ke kika karar da shi cikin kwanaki .. " "Noo. Ina kiran yan uwa mana..." "Ba dai yan uwa ba... Harda kawaye. " "Bushra ce kawai. Kuma ita ai bestfren dina ce." "Ta fini muhimmanci ai awajen ki na sani... Bakya boye mata komai." Ko ajikin ta. Da abunda ya fada sai ca tayi "Itama bata boyemun komai. Human diary din juna ne mu." "To ki zauna kina biye mata... Naga ba aurene da ita ba. She's much less busy than u ahlamm.. That aside yau su Maa zasu zo kinsani ai. Kuma kinga ai ba zasu zo su tafi ba ba tare da sunci abinci ba. Da snacks and drinks haka.. Me zaki dafa musu?" Bata ce komai ba. Ta yi shiru. Idanunta akan wayar da ke hannun ta. Tanata latsawa "Ahlam...." "Naam..." Ta amsa da sauri tana daga kai "Magana nake miki ... Dan Allah ki rage danna waya ... " "Me kace?" "Nace me zaki dafawa su Maa da zasu zo. ? Da su snacks haka da drinks?" "Tab..." "Pardon ...?" "Gaskia sai dai ko babbar me aikin Maa dinnan tazo ta dafa abincin." "Ke meyasa ba zaki ba.?" "Ban iya ba." Ta amsa shi kaii tsaye. Ya sake jan leban sa ya ciza. Kafin ya sake cewa da ita, "To drinks fa akwai? Zasu isa?" "Eh... " "Tohm bari naje na dawo .." "Alright...." Ta amsa shi. Ta juya ta zauna taci gaba da danna wayarta. Haka ya shiga mota ya nufi gidan su kai tsaye. Zuciyar sa nata tafasa. Ya kasa gane kan Ahlam. Tamkar ba mace ba? Ba sirri. Ba ladabi. Ba tarairaya. Ba tsafta... Ba godiya. Hakika babun ta tayi yawa. Haka ya karasa gidan su yanata tunani ya saka wannan ya ware. Yana karasa parking ya shiga ciki bakinsa dauke da sallama. "Wa'alaykm Salam..." Tsugunna wa yayi har kasa ya gayshe da mahaifiyar tasu Haj Hameedah. Ta amsa da fara'a. Lura tayi da yanayin sa. Sannan tace, "Ga abinci can a dinning... Ko zaka coi." "Tohm Maa...." Ya mike