← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 82

Sashe 65

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bugawa, tunani ta farayi, yanzu me zatayi wanda zai sa ya kyaleta? Share hawayen tai tana fadin. "Ina so kaje wajan Aunty Ahlam ka tambayeta, idan har ta amince dani a matsayin abokiyar zamanta ina mai tabbatar maka zanje gidanka a matsayin matarka. Idan kuma bata amince ba ina so dan Allah ka rabu dani kaje ka rungumi matarka, dama a duniya ba komai mutum yake samu ba." Zayn yai mata wani mugun kallo wato sai da ta tabbatar da cewa Ahlam ba zata taba yadda da ita a matsayin kishiya shine tace haka. Bazai mata dole ba hakan yasa shi tashi zaune yana jan dogon hancinsa wanda tsarin yanayin halittarsa ya karawa fuskarsa matukar kyau. Tsaye ya mike yana so ya kalleta sai dai zuciyarsa na san ta koyi yin hakuri da kasancewa da ita har zuwa lokacin da zatayi hankali ta gane cewa shi din mijinta ne mai tsananin kaunar ta. "Shikenan zanje, ina san kiyi addu'a ki roki Allah abinda kike so, ni kuma zan tayaki da amin koda kuwa rabuwarmu itace ta ratso tsakanin mu." Hanyar fita yayi, har ya kama hannun kofar ya murda sai yaji kamar ya koma, ya juya tare da kallanta, tana kwance idanunta a rufe, girgiza kai yayi kawai ya fice zuciyarsa na tsananta harbawa. Yayi sa'a parlorn babu kowa har ya fice daga gidan. Mota ya shiga tare da dora kansa jikin glass door yana jin wani irin yanayi, harga Allah yana matukar san ganin Waheedah a tare da shi, sai dai yaga alamar samunta lokaci guda zai bashi matukar wahala dan yana hango tsoran Ahlam a can cikin idanuwan Waheedan. Dakyar ya iya samun damar kunna motar ya wuce gidansa cike da tunaninta. Fitowa yayi daga motar hannunsa rike da briefcase dinshi ya nufi cikin gidan kansa tsaye. Zaune a kasan carpet ya tarar da Ahlam tana waya, ya karasa ya zauna kan daya daga cikin kujerun parlorn, kallanta yai yaga fuskarta tayi wani iri alamar taci kuka har ta godewa Allah. Inda yake zaune bata kallaba ballantana yasa ran zata amsa masa sallamar da yayi. Yanata zama a wajan amman Ahlam bata da niyar katse wayar da takeyi, ran Zayn ya fara sosuwa cikin bacin rai yake kallanta yana fadin. "Bansan wace irin mata bace ke, kina ganin na shigo har na samu guri na zauna amma baki san ki ajiye wayar ba, a haka kike tunanin zan yi rayuwa dake ke kadai? Bakisan yadda zaki kula da mijinki ba bare ki bashi girmansa na matsayin miji?" Cikin rashin damuwa Ahlam ta katse wayar tana yi masa wani irin kallan raini take fa "Oh wai kai har yanzu kana tunanin zan yi maka wani abun? Zayn ka manta cewa amanata kaci ta hanyar auro wacce ta gama sanin sirrina? Kun gama cin amanata kake tunanin zan baka muhimmanci?" Ta saki wani murmushin takaici tare da gyada kai tana cizon lebenta na kasa. "Wallahi indai sai a waje na zaka samu farin ciki zaka dade Yah Zayn, kaje can ita munafukar ta yi maka duk wani abu da kakeso, amman indai nice nagama." Tana gama maganar ta sake bude wayarta, wannan karan chatting ta ci gaba da yi tana dariya. Wani irin bacin rai ya bayyana a fuskarsa ya mike tsaye yana girgiza kai irin na takaicin nan yace. "Dama can mekike yi min Ahlam? Tunda mukai aure mekikai min da zan iya nunawa nace naji dadi?" Bata kulashi ba ya cije lips zuciyarsa na zafi, cikin son ya bata mata rai shima yace. "Ko yanzu daga wajanta nake, kuma Alhamdulillahi sai da na samu fiye da abinda baki san matan aure na yiwa mazajensu ba. Ke kuma ki zauna a haka kicigaba da chatting dinki har zuwa randa zamuga ribar yinsa." Yana kaiwa nan ya juya zai bar mata parlorn yaji tana cewa. "Ai dama na gane cewa ba tun yau ta fara baka abinda bana baka ba, ni tunda naji kace ita nasan dama kun dade da mallakar juna a watse, gwarani sai da mukai aure ita kuwa fa? Yanzu na san ragowar abinda ka rage a wajanta shi kake son kwakulewa daga nan sai na fara jin kace zakai wani auran." Habawa Ahlam ta sosa masa zuciya, metake nufi da kalamanta? Zarginsa takeyi kome? Lallai dole ya takawa Ahlam burki akan tunaninta. Juyowa yai yana sake kallanta, tana zaune a inda take tana murmushi tare da danna waya. "Koma dai menene kekika janyo, idan ma iskancin nayi tabbas yayi min dadi tunda gashi har na aureta ta zama kishiyarki sai ki gaya min dame kika fita? Kuma bari kiji na gaya miki na dena wani lallabaki akan kiyi hakuri, kar Allah yasa ki hakura. Waheedah kuma matatace wacce tasan darajar aure tasan darajar miji, ba irinki ba da chatting kawai kika bawa duk wani lokaci naki." Yana kaiwa nan yai tafiyarsa, kalamansa kuma sun konawa Ahlam rai da zuciyarta. Afusace ta mike tabiyo bayansa, kofar ta murda taji an rufe ranta na suya take fadin. "Wallahi karyane Waheedah ba zata taba zama matsayi irin nawa ba, Waheedah yar talakawace wacce bata san komai ba sai wahala da kauyanci. Kuma kaima nasan ka aureta ne kawai dan tazo tayi maka bauta tunda kasan ita din yar wahalace." Kafa tasa ta buga masa kofar dakin sannan ta juya tana masifa da bala'i, ji take kamar ta tsaga kofar ta shiga cikin dakin tai masa shegen duka ko zuciyarta zatai sanyi. Zayn kuwa yana shiga kamar yasan zata iya biyoshi ya murzawa kofar mukulli, briefcase dinshi ya ajiye akan madubi shi kuma ya karasa wajan gado, a hankali ya fada saman shi tare da rintsa idanuwa, tunani ya fada yana jin zuciyarsa tamkar wuta, sam baya cikin jin dadi saboda ta ko'ina baya samun farin ciki, duk inda yake babu farin ciki gaba kura baya sayaki, dama haka mata suke? Waheedah dan yana santa sai gwarashi takeyi yadda taga dama? Ahlam na gwarasa cikin borin kunyarta da babu gaskiya a ciki, yanzu ya zai yi? Ta ina zai fara yiwa Ahlam bayanin cewa sai ta yadda sannan Waheedah zata amince masa? Gashi yanzu yazo ya sake damula komai. "Ya Allah." Ya furta yana rintsa idanuwa. Yana jin muryar Ahlam harta gama ta bar wajan, kansa ne yaji yana masa wani irin nauyi kamar an dora masa dala da gauran dutse. "My love.." Ya fada yana hango hotan Waheedah acikin idanuwansa. Maimakon yaji soyayyarta na raguwa a'a sai yaji ana sake ninka masa. Wayarsa ya zaro daga cikin aljihu ya lalibo sunanta, kamar ya kira sai kuma ya fasa besani ba ko tana tare da su Maa. Online ya hau ko zai ganta yana kunnawa yaga Ahlam is online, yaja dan siririn tsaki, shi kam be taba hawa yaga bata kai ba saboda tsabar jarabar santa da chatting. Contact din Waheedah ya duba yaga ta dade bata hawa WhatsApp din, ya dan duba abinda zai iya dubawa ya sauka tare da kifa kansa akan pillow.... Zayn yayi iya yinsa wajan ganin bacci yazo masa amman ya kasa, banda juyi akan gadon babu abinda yakeyi. Yadda zai yiwa Ahlam magana akan ta amince Waheedah ta zama mallakinsa ita kawai yake nema, ya rasa dalilin da yasa Waheedah ta bashi wannan sharadin, gashi daga shigowarsa ya batawa Ahlam din rai. Juyawa ya sakeyi yana mai rintsa idanuwa tare da tunanin anya zai biyewa Waheedah? Gaskiya ba zai biye mata ba dan ya gaji da zama babu ita a tare dashi, idan kuma ba so takeyi zuciyarsa ta samu matsala ba akan soyayyarta. A ranar haka Zayn ya karaci juyi a gado, gashi ko aikin office da ya taho dashi gida kasa yi yai bare ya rage. Tashi yai ya gabatar da sallar nafila, ya dade yana addu'o'insa kafin ya tashi, gado ya koma tare da janyo wani english novel yana karantawa, sai dai tunaninsa gabaki daya yana kan matarsa abar so da kaunarsa sannan kuma FARIN CIKIN ZUCIYAR sa. Bashi da wani buri irin yaga itama ta sakko daga dokin tsoran Ahlam da takeyi, wanda yake neman ya hanata ciki umarnin ubangiji. Har aka kira assalatu bai rintsa ba haka ya tashi ya sake yin sabuwar alwala ya fito ya tafi masallaci. Bayan sunyi sallah ya dawo yaje ya yiwa Ahlam knocking dan ta tashi itama tayi, bai jira ta bude ba ya nufi bedroom dinsa ya fara shirin fita. Yasan dama ba wani breakfast zai samu ba a wajanta hakan yasa yana gama wanka yasa kayansa yai duk abinda ya zame masa al'ada ya feshe jikinsa da turaruka na musamman, fitowa yai kafadarsa rataye da briefcase yana danna waya. Ahlam ya gani tsaye a bakin kofar dakinta tayi kicin-kicin da ita Zayn ya kauda fuska yana nufa hanyar fita yaji tana cewa. "Za'a fita inda aka saba zuwa?" Ya dan yi murmushi, kallanta yai yana lumshe idanuwa yace. "Kwarai da gaske kina da sautu ne?" Rai a bace take yi masa wani kallo mai nuna bacin rai Ahlam in ke cewa. "Wallahi Zayn ka badani, ni wallahi kacuceni ina jin bakin cikin irin yarinyar da zaka auro min matsayin kishiya sai Waheedah, duk yan matan dake fadin jihar Kano. Ina gaya maka ni bazan iya kishi da yarinyar nan ba wacce a gabana ta fara sanya bra, ta fara sanya kaya na alfarma, a gabana ta fara iya sanya lipstick ace kuma ita zaka kawo min a matsayin wacce zan hada miji da ita, tabbas ka yaudareni." Zayn ya dan lashi kasan lips din shi tare da sauke numfashi yana murda handle zai fita yake cewa. "Dama bake na aurowa Waheedah ba, na aureta ne saboda ina santa, itace zata iya bani duk wani hakki na aure ba wai kyal-kyal banza ba." Kamar yasan zataji haushi, yana gama magana yai saurin ficewa ya rufe kofar da key din hannunsa. Yana jinta sai murda kofar take yaje ya bude mota wace tuni an gama wanketa sai sheki takeyi tana walwali. Briefcase din ya ajiye a back seat tare da jan numfashi yana girgiza kai, motar ya kunna ya fice daga gidan gaba daya. Kai tsaye gidan Maa ya wuce, a waje yai parking saboda yana son fitowa ya tafi aiki. Yana shiga mai gadi ya gaishe dashi Zayn ya amsa cikin sakin
Chapter 65 · 0% Book details