Sashe 59
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: *FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:58_ *Ko da* ya shiga, Ja ya yayi yai turus. Ganin parlorn a hautsine. Tamkar ba gidan da mace ke ciki ba. Bayan dazun da safe kafin fitar sa ya tarar da parlorn baki daya a gyare a kuma tsaftace. Ya yin da komai ya ke muhallin sa. Har da guzurin kamsashshen turaren wuta na kamfamin turarukan yerwa incense and more. Robar faro ta ruwa a wulle a kasan kujerar da ta ke kwance akai. Gefen robar kuma sachets ne na biskit da ledojin chocolate na maltesers sai gwangwani na Pringles. Tana kwance akan kujera ta mike kafafun ta a tare ta dora su a hannun kujerar. Hannuwan ta duka biyu kuma ta rike wayar ta tana dannawa. "Assalamu alaikum wa rahamatul Allah, Wa barakatuh!" Ya daga murya wajen sa ke yin sallama a karo na uku. Ya yin da ya jingina da jikin kofar parlorn ya zuba mata idanu. Ganin sai a sannan ta daga kai ta dube shi. Wato duk sallamar da yayi bata jiyo ba. Saboda baki daya hankalin ta da nutsuwar ta na kan wayar da take dannawa. ? Shikenan idan har Waheedah bata gidan ba sauran mutunci da gidan yake da shi? Ba gyara babu kulawa? Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ganin ta kalle shi ta mayar da kanta kan wayar hannun ta Bai wani damu ba. Domin ya saba da shirmammakin halayen Ahlam irin na ko in kula din da take masa. Tamkar shi din ba miji bane a gare ta. Kai tsaye ya wuce kitchen, Ko'ina a kitchen din tatas ya ke. Komai a kintse a kuma gurbin sa. Ya dan dudduba mazuban abinci. Babu komai na abinci. Ya juya ya hango parlor Ahlam na kwance abunta tana karkada kafafu. Wato saboda Waheedah bata nan yau ba abinci kenan? Ya girgiza kai kawai, Ya bude freezer ya dakko wata fura daya saka jiya . Ya dauki cokali ya haura sama. Kasan zuciyar sa na masa zugi da radadin halin ko'in kula da Ahlam ke nuna ma sa. Zama ya yi a parlorn saman. Ya bude furar da basmala ya shiga sha. Dadi sosai tayi masa. Ta kuma cika masa ciki. Yana shanyewa ya shige bandaki ya wanko bakin sa. Ya kunna tv ya lalubo tashar labarai ta BBC yana kalla. Can ya janyo wayar sa ya shiga Whatsapp. Da status dinta ya ci karo. Ta dora hotunan akwatunan Zainab yar uwarta da aka kawo. Da caption din 'congratulations dear sis. Allah yasa albarka da alkhairi amin. ' Hoto na gaba da ta saka kuma ita da kawarta ne Basira. Dukkanin su sunyi dariya . Samun kan sa yayi da zooming din dai-dai saitin fuskar ta yana kalla. Tun daga kan girarta cikakkiya mai dauke da gashi baki ya zuwa manyan idanun ta dake dauke da gashin ido zara zara a kanannade suna sheki. Ta saka kwalli da ya karawa idanun annuri. Har ya kan dan karamun bakinta. Da ke da labba pink. Suna sheki saboda pink lipstick din da ta sa ka. Ya samu kansa da tsurawa hotan nata idanu tamkar yana nazarin wani abun. Can ya ajiye wayar tasa ya mike. Daki ya shiga ba jimawa ya fito ya sauka kasa bayan ya dauki wayar sa. "Zayn...." Ahlam ta kira sunan sa. Tana zaune akan kujera. Kalba biyu ce akan ta sun mimmike. Gata da cikar gashi amman ba kula. Ya kalleta ya kauda kansa zai fita ta sake kiran sunan sa. "Zayn." "Ya akai?" Ta turo baki gaba . "Subscription dina ne ya kare. Na ke so kayi mun renewing " Girgiza kai kawai yayi. Ya kalleta sosai kafin yace da ita, "Kin gama?" "Me fa?" "Maganar" "Eh..." "Toh." Ficewa kawai yayi kai tsaye ba t are da ya sake ce mata komai ba. Baba mai gadi na zaune akan kujera . Hannun sa dauke da yar rediyon sa ya saka ta a saitin kunnen sa. Yana hango Zayn ya tashi da sauri ya shiga tura gate. Zayn din ya nufe shi yana murmushi, "Sannu da kokari Baba." "Yauwa sannun mu." Hannu ya saka ya zaro dubu daya ya mikawa Baba mai gadin. "Kayi mana gafara Baba. Bamu kyauta ba. Ga wannan kaci abinci yanzu da daddare ma . Dan Allah" "Ah kar ka damu ranka ya dade. Kudin da ka bani jiya ma har yanzu da shauran su. Na ci abinci na dadewa awajen me sayar da abincin tsallaken titi , Ga kudin ka." "A'a Baba. Ka bar su ka sake sayan me nauyi kaci sosai dan Allah. Ni zan fita " "To shikenan. Nagode Allah ya saka da alkhairi." "Amin Amin." Mota ya koma ya shiga ya tayar da ita ya fita. Kai tsaye ya wuce gidan su. Dai dai kofar gate din layin ya tsaya da motar sa. Ya janyo wayar sa ya tura wa Ahlam data ta bank. Kafin ya karasa gidan na su. Masu gadi suka bude masa gate ya shige da motar sa. Dakin sa ya shiga da yake na kwanan sa a da kafin yayi aure. Dan lokaci zuwa lokaci ya kan je ya buda ya shiga ya kwanta. Domin komai na nan a mazaunin sa baa cire ba. Sannan wasu kayayyakin na sa suna nan bai dauka ba. Kwanciya yayi akan gadon sa bayan ya karkade da addu'oi. Wayar sa dake gefen sa ce ta shiga kara. Tamkar ba zai dauka ba. Sai kuma ya daga yana kallon screen din don ganin me kiran. Abiey din su ne, Don haka da sauri ya dauka ya kara a kunnen sa. "Wa'alaykm Salam... Barka da yammaci Abiey.. Eh, Eh... Ina daki na, Okay tohm, Gani nan " Mikewa yayi da sauri. Ya fita daga cikin dakin bayan ya kulle shi da mukulli. Kai tsaye ya wuce sashen mahaifin na su. Bakin sa dauke da sallama ya shiga. Da ke transparent sliding door ce a babban parlorn. Ta nan ya hango har da mahaifiyar su aciki da kuma Ummimi. Ya shiga parlorn bakin sa dauke da sallama. Ya tsugunna har kasa ya gayshe su cikin girmamawa. Suka amsa fuskokin su a sa ke. Haj Hameedah sai kallon Zayn ta ke ta gefen idanu. Ya faada sosai tamkar wanda ya tashi daga ciwo. "Ina Ahlam ...? Tana gidah?" "Eh Abiey..." "Fatan kowa da komai lapia dai ko?" "Alhamdulillah Abiey....." "To masha Allahu ." "Zayn... Kasan akan meyasa na sa aka kirawo mun kai?" "A'ah Ummimi .." "Kayi hakuri da hadin auren ka da na saka akayi da yar uwar ka Ahlam..." "Haba Ummimi. Hakurin me kuma? Dan Allah ki dena cewa haka. " "Dole na fara da ba da hakuri Zayn. Domin ni ce maqasudin shigar ka wannan mawuyacin hali. Dubi yadda ka rame ka fice daga hayyacin ka. Kasancewar ka mai dimbin zurfin ciki. Baka fadin damuwar ka. sai an tasa ka agaba an maka tilas. Banyi zurfin tunanin mabambamta halayen ku ba. Na yi amfani da kasancewar ku a dangi daya. Ka gafarce ni kaji?" Zayn yayi murmushi kawai kafin yace, "Allah Ummimi ba komai. Kuma ba kiyi lefi ba. " "Ka dai yi hakuri. Ka kuma yafemun. Kaji?" "Tohm " "Allah ya maka albarka .." "Aamin Ummimi." "Yauwa .. Sai batun yarinyar da kace kana so. Wacece? " "Wata ce.." Ya fada ahankali. Ya daga idanu ya dora akan Maa data murtuke fuskar ta. Tana cilla masa kallon kashedin kada ka kuskura ya ambaci Waheedah. Saukar da kansa kasa yayi sosai. Gaban sa na tsananta bugawa, "Yar gidan wacece? A'ina take? Ina fatan kuma ta fito daga tsatso masu dattako da sanin ya kamata. Sannan mai hankali ce da wadatar zuciya... Toh Alhamdulillah. " Ummimi ta karasa fada tana kallon farfesa Adams Nasser. "Haka zancen ki yake Ummimi... Zayn kaaji dukkanin abubuwan da Ummimi ta fada. Ina fatan kamar yadda Ummimi ta fada yarinyar na da hankali da sanin ya kamata. Sannan wacece?" Zayn yayi shiru. Rashin sanin abunda zai fada. "Magana ake ma ka." Kansa a kasa yace, "Wata ce.... Ummimi" "Budurwa ce ko bazawara.? Karka ji komai dan na tambaye ka ha ka.. Dukkanin su da za'a aura ne. Sai dai bazawara ana son aji dalilin da ya fito da ita daga gidan mijin ta na baya ka gane?" "Eh! Ummimi." "To masha Allahu. Waccece daga ciki?" "Bu... Budurwa ce." "To masha Allahu. Allah ubangiji yasa kayi zabi na kwarai. Allah kuma yasa haka ne yafu alkhairi. Kaji ko?" "Eh..Aamin Yaa Rabbi. " "To Insha Allahu. Manya zasu shiga cikin zancen. Sai dai har yanzu baka fadi yar gidan wacece ba " Hannuwan sa a hade yana harhade su . Rashin sanin abunda zai fada. Ganin sun zuba masa idanu suna sauraron cewar sa . Hakan ya sa shi yanke shawara kan cewar, "Ba .... Ba mu. ... Bamu gama... " "Baku gama dai-daita tsakanin ku ba kakeson cewa?" Ya daga kansa alamar eh. "To ku dai-daita din. Kada abun ya dau lokaci. Saboda manya su shiga ciki kaji ko?" Ya gyada kansa sama. Kafin yace da su, "Toh! Insha Allah." "Masha Allahu. Allah yayi muku albarka baki daya, Amin." "Allahumma Aamin." "Zaka iya tafiya... " Durkusawa yayi ya musu sallama. Ya fice daga sashen. Kai tsaye ya shiga motar sa ya bar gidan. Bayan fitar Zayn ba dadewa.. Ummimi ta dubi Haj Hameedah . "Menene Hameedah?" "A'ina Ummimi?" Ummimi ta danyi murmushi, "Akwai abunda ki ke boyewa. Naga kallon da kika yi wa Zayn shi ya hanashi furta komai akan yarinyar da ya ke so. Shin akwai wata matsalar ne a tattare da yarinyar?" Haj Hameedah ta girgiza kai. Cikin sanyin jiki ta dubi farfesa Adams da shi dinma ita yake bi da kallon karin bayani. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Kafin cikin sanyin murya tace, "Gaskia akwai matsaloli Ummimi . Domin na farko ma dai yarinyar da yake ikirarin yana so zai aura. Bata masan yanayi ba. Babu wata soyayyah dake tsakanin su. Ihu yake a ..... A .." "Ihu a bayan hari" ummimi ta karasa mata. "Yauwa!ihu yake a bayan hari. Ya sameni da maganar nace masa kada ya kara taso da ita. Domin abune mai wahalar yiwuwa. Bazan bari ya tauye wa