← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 82

Sashe 55

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamal. A nasa bangaren kuwa dakon jidalin kaunar ta ne kullum ke dada tasiri a zuciyar sa da gangar jikin sa. Yana kaunar Waheedah fiye da yadda al aluma zasu rubuta. Zuciyar sa na begen samun Waheedah a matsayin matar aure. Gangar jikin sa na ingiza da kwadaituwar kasancewar Waheedah a tattare da shi. Amman gaba daya ya kasa sanar mata. Ta kuma kasa gane inda ya nufa. Ta riga da ta dauke shi a matsayin dan uwan ta na jini. Tamkar babu aure a tsakanin su. Ganin yadda kullum ya ke dada karewa a tsaitsaye. Gashi Maa ta ki zama ta fuskanci maganar. Ranar da ya sake zubewa ya nemi rokon alfarmar samun Waheedah. Ta wanke fuskar sa da gigitaccen marruka a dama da hagu na gafen fuskar sa. Bai sake bi ta kanta ba da maganar. Kai tsaye ya samu mahaifin sa ya sanar da shi. Alokacin kuma Ummimi mahaifiyar mahaifin su ta zo . Zayn ya kasa cigaba da boye maganar. Daman Ahlam ta karasa kai shi karshe da halayen ta. Tamkar zaman haya haka suke yi a gidan na su. Ta tattara shi ta watsar a gefe. Hakki na rayuwar aure ma sai ya ta rokon ta zata bashi dama. Idan kuwa bataga dama ba sam bata bari ya kusance ta. Dukkanin abubuwan da ke faruwa daman dangi sun sani. Don haka zuwan da Ummimi tayi ta kirawo dukkanin sauran yaran nata da ke kusa da matayen su. Ciki har da mahaifiyar Ahlam. Ummimin tace gwara ayi me yiwuwa. Ta yanke ta gille. Ahlam dinma Ummimi ta sa Zayn ya kawo ta gidan na The Adams Family. A babban parlorn gidan duk suke a zazzaune. Ahlam sai wani fiffika ta ke yi. Ummimi tayi gyaran murya ta fadi komai a takaice. Kasancewar kowa ya san masaniyar tsakanin Zayn da Ahlam . "To ni Ummimi menene laifi na? Shi ne tun farko dama ai ba kauna ta yake ba. Bayan munyi aure halayen sa suka fito " Ahlam ta fada tana hararar Zayn. "To naji mu dauka ace hakanne. Ke menene yasa kike tauye masa hakkokin auren sa da ke kan ki? Eh? Tsinke wannan bakya dauke wa karya nayi?" "A'a..." "Toh kadan kenan daga cikin sakacin wasu matan akan bai wa yan aiki ragamar komai na rayuwar aurensu...... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:56_ _____ Ahlam ta daga idanu da sauri ta dora akan Ummimi. Kafin cikin bacin rai da takaici tace, "Bangane ba Ummimi.... Sakacin me nayi?" "Da fari kafin ma a samo miki me tayaki aiyukan. Ba almajirai kika dauka har biyu ba yara suke gudanar da aikace aikacen gidan baki daya?" Ba tare da ta ce komai ba. Ta zumbura baki gaba tana mai yatsina fuska. Ummimi ta sake zare mata idanu, "Tambayar ki na ke kinyi shiru. Haka ne ko ba haka ba ne?" "To ai aiyukan ne sunyi yawa ba zan iya ba ." "Haba Ahlam, To menene ladan da zaki samu na rayuwar auren idan har bakya aikace aikacen gidan da mijin ki zai sanya miki albarka? Kullum kina kwance kamar ruwa lamama. Da waya a hannun ki hannu bibiyu. Tunda na ke ban taba ganin me danna waya a duniya irin ki ba Ahlam. Na hane ki tun kafin auren nan ashe baki dai na ba? Kinyi uwar watsi da zance na.... " "Ummimi please ... Abar zancen nan." "Ba za'a bari ba. Ummimin kike kalla kina abar zancen nan? Wacece ke? Shashasha, sakarya. " Cewar alhaji nouh mahaifin na Ahlam kuma da ga Ummimi. "Yi hakuri Baba. Kiyi hakuri Ummimi." Ahlam ta basu hakuri. Kanta a k sa. Ya yinda kasan zuciyar ta ke mata zugi. "A mata afuwa Ummimi..." Farfesa Adams ya fada yana murmushi "Ai ni baki daya ba ni da tace wa... Sai fatan shiriya. Allah ya kuma ya huci zukatan dukkanin mu Amin." "Amin Ummimi." "Amin." "Zayn wane hukunci ka yanke akai eh.?" Alhaji Nouh mahaifin Ahlam ya tambaye shi. Kan Zayn a k sa cikin ladabi yace, "Duk hukuncin da kuka zartar ya yi." "A'ah ai ba zamu tauye maka hakki ba son. Kuma magana ta gaskia duk wanda ya zauna ya auna rayuwar da kukayi da Ahlam zai ga kana cutuwa aciki sosai. Ba bu kuma iyayen da zasu so haka ya faru da dan su. Dan haka ni de a nawa ra'ayin. Rabuwa da Ahlam shine mafi alkhairi a tattare da kai." Da sauri Ahlam ta daga idanu ta sauke akan mahaifin ta jin abunda ya ke cewa. Saboda bata taba zato ko tsammanin haka daga gare shi ba. "No kar ka ce ha ka dan uwa. Ni tunanin da na ke ma Allah yasa laifin ba daga Zayn ba ne. Saboda yanada zurfin ciki matuka." Farfesa Adams ya fada yana kallon Zayn Shi dai Zayn kanzil bai ce ba. Alhaji Nouh ya girgiza kai kafin cika daga yatsa ya nuna Ahlam yace, "A'ah zancen nan fa ba sabo bane. Anyi fadan Anja kunnen yarinyar nan yafu a kirga. Ni da kai na gata ba karya nake ba wallahi sai da na kirata waya video call lokacin ina Cappadocia. Na ja kunnenta sosai tace mun ta dai na . Ashe ashe labarin kanzon kurege ne. Don haka babu ruwan Zayn wallahi. Ai dama na sha jiyota da mahaifiyar ta ga tanan tana mata fada akan yin aiki da dai na sangarci saboda aure zatayi. Amman taki yi. Ga banzan halayen data tsira na gayawa kawa komai. Da turawa bloggers neman shawara duk fadin dangin da muke da shi ba mu isheta ba mu sai iyayenta na waya. Na karanta writeups dinnan ba adadi wallahi. Ina mamaki wanda ko a mafarki ban taba zato ko tsammanin haka ba. Kuma wallahi wallahi yarinyar nan ba ta kaunar Zayn." Baki daya sai akayi masa caaaa jin abunda ya fada a karshe kan Ahlam din bata kaunar Zayn. "Zancen ka na karshe da gyara ...." Ummimi ta fada tana murmushi. Alhaji Nouh ya girgiza kansa kafin ya cigaba da cewa, "To bata kaunar tara iyali da shi. Wai kamar Ahlam har ta san ta dinga shan contraceptive pills? Kuma guzurin su tayi ta tafi su da gidan. To Ummimi bata kaunar karuwa da shi ai bata kaunar shi wallahi. " "Eh to da wannan gaskia..." "Yauwa ..Ni dai idan ana neman shawara ne. Shawara daya zan bayar itace ta rabuwar su. A raba auren nan dubi yadda yaron nan ya zama fisabilillahi. Tamkar ba Zayn ba. Ita kuma dubi yadda take hawa kamar farashi. Idan aka bar shi ya cigaba da zama da ita tabbas an cuce shi. A cire batun zumunci a dubi hanyar gaskiya. Idan ya cigaba da zama da ita Allah karasa illata shi zata yi. Tunda dukkanin abubuwan da suke faruwa ma ba shi yake fada ba tursashi ake idan an ga damuwa a tattare da shi. Kuma ace kaman Ahlam kuna garin nan unguwa ma kusan daya amman bata san ta zo nan gidan ta gayshe da surukan ta ba? Kafin ku zama surukan natan dan uban ta ai iyayen ta ne ku. Kullum 24/7 yarinyar nan tana online tana chatting. Gaba daya rayuwar auren a wasa ta dauke ta da kuma shiririta. Saboda haka gwara a kawowa tufkar hanci. Dan Allah Ummimi.. ko kuwa Yaya?" Ya juya saitin Yayan su mahaifin su Zaid . Alhaji Nouruh. Alhaji Nouruh ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ya dubi Ummimi
Chapter 55 · 0% Book details