Sashe 66
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fuska ya shiga sashen Maa. A parlor ya tarar dasu Waheedah kuma tana kitchen ya gaishe da Maa kannansa suka gaishe shi. Idanunsa na hanyar stairs yana son zuwa wajanta kawai yaji motsi ta bayansa, be juya ba har ta karaso parlorn rike da wani jug mai kyau ta ajiye a kan center table. Ido ya zuba mata yana kare mata kallo tana sanye da hijab har kasa. Bata bari sun hada ido ba ta durkusa tana gaishe shi. "Ina kwana Ya Za.." Ta kasa karasawa saboda kunya, Zayn ya cije lips. Muryarta yaji tana yiwa Maa magana. "Maa an kammala kawo komai bari naje daki zan watsa ruwa." Cikin fara'a Maa ta ce. "Shikenan Waheedah idan kin dawo sai kiyi breakfast din." Da sauri Waheedah ta wuce Zayn yana bin ta da kallo har ya dena ganinta. Kunun gyada ne Maa ta zuba masa dan tasan beci a gidansa ba, da awara wacce tayi irin ruwa-ruwan nan tasha eggs akai mata wata hadaddiyar sauce din kwai ga yankakkun veggies a kai. Ci ya farayi amman duk hankalinsa yana kan yadda zai shiga gurin matarsa, Maa ta mike da sauri tana cewa. "Oh na manta Abiey yasani abu, kai Allah ya kyauta min yanzu abubuwa saurin mantasu nake." Tana fada tana wucewa wajan maigidan. Zayn ya dire cup din da sauri ya haye wajan Waheedah. Da sauri ta juya jin yadda aka rufe kofar, ganin Zayn yasa ta ware idanuwa, batayi aune ba kawai ta ganshi a gabanta, hannu yasa yaja mata hanci ganin yadda ta kame a guri guda yana cewa. "Zuwa nai ki gaidani." "Gaisuwa kuma? Nafa gaida kai a parlor." Tayi maganar tana kauda fuska. "Wata nake so kiyi min." Ya fada yana sake matsawa kusa da ita. "Please Ya Zayn bana so, shin matarka ta amince da aure na da kayi?" Zayn ya lumshe idanuwa yana tuno yadda ta kasance tsakanin shi da Ahlam. A hankali ya bude ido yana kallan Waheedah da idanunsa masu cike da zallar kaunarta. Hannu yakai zai kama nata tai saurin jan baya. "Please Ya Zayn ka tafi wajan aikinka." Rintsa ido yai yana jin wani irin babu dadi a ransa, ya gyada kai ba tare da ya iya cewa komai ba ya bar mata dakin. Ko Maa be yiwa sallama ba yabar gidan, mota ya shiga tare da figarta yana mamakin lamari irin na mace. Koda ya dawo gida ya wuce saboda yana san ya bawa Waheedah fili karyaje ya sake sanya tsanarsa a zuciyarta. Ahlam ma bata san ya shigo gidan ba saboda be nemeta ba tana cikin daki tana bacci. Zayn kam mazewa kawai yake yi na rashin sanya Waheedah a idanunsa yanzu. Yana kwance ya tasa laptop a gaba, shi beyi aikin ba sannan ya kasa rufewa. Har akai sallar isha yana jin zuciyarsa tana tunzura shi akan zuwa gidan Maa amman yana daurewa. A ranar dai shima be samu wani bacci mai dadi ba, ya bari kawai da safe dole zaije gidan dan ba zai cuci kansa ba akan sharadin da ta bashi...... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAF A BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:62_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ ______ *A* hankali ya fara zura fuskar sa ya leka cikin dakin. Kafin gangar jikin sa ta biyo baya. Gabansa na tsananta bugu. Hamdala ya saki ganin babu kowa acikin dakin. Haka ma parlorn kasan. Dan haka ya murza key ya koma bakin gadon ya zauna Motsin ruwan dake zuba a bandaki ne ya tabbatar masa tana ciki. Don haka ya gyara zaman sa. Ya janyo wayar sa a aljihu ya shiga dannawa. Bayan ta kammala wankan. Ta sake tara ruwa ta zuba masa after bath khumrah na kamfamin turaren yerwa incense and more. Ta dauraye jikin ta da shi. Take jikinta ya fara kamshi sosai. Ta daura bathrobe a jikinta ta fito daga cikin bandaki tana adduar fitowa daga cikin bandaki. Kai tsaye ta wuce wajen mirror ta zauna bayan ta dauki wata kulaccam ta kamfanin turaren yerwa incense and more . Ta shafe jikin ta da shi. Lungu da sako na bayan kunnen ta da kasan maman ta da cinyoyin ta. Zayn ya zuba mata idanu. Sam batasan yana dakin ba. Sai data tsiyayi khumra a tafun hannunta tana shafawa a jikinta. Tana daga idanuwa ta sauke akan mirror ta hango shi ya mayar da nutsuwar sa da tattaro hankalin kansa baki daya ya dora akan ta. Ta janyo glass ta zura don tabbatarwa. Wani abu ya taso ya tokare mata a makoshin ta. Ta janyo hijabin da ke sakale a gefe ta zura. Dan murmushi ya bi ta da shi yana mai lashe kasan leben sa. Drawer ta bude ta dakko kayanta ta koma can karshen closet ta zura su. Ta zura hijabin ta ta rataya Jakarta a kafada. "Ina kwana?" Ta gayshe shi kanta a gefe. Ya mike ya isa inda take a tsaye ya riko ta. Ta shiga zillewa. Amman da ke karfin ba daya ba ne... Sai ya sake tukwikwiye ta . Sam ta kasa kwatar kan ta. "Makaranta.....?" Ya tambayeta cikin muryar rada. Ta hanyar dora bakin sa akan kofar kunnenta . "Uhmmmm" Tace dashi, Domin baki daya ya kashe mata jiki. Ta kasa tabuka komai. Janyota yayi suka zauna a bakin gadon. Ya yinda ya riko hannuwanta ya saka acikin nasa. Idanuwan sa na sauke akan ta. Ta kasa hada idanu dashi saboda kwarjini da girman sa daya kamata.. "Waheedah....." Ya kira sunanta cikin kwarewa da jan haruffan karshe. "Na'am..." "Bazan gushe ba fa-ce na cigaba da baki hakuri .... Ko kinsan Dawood?" Yana karasa fadar sunan Dawood gabanta ya yanke ya fadi. Daman jikin ta ya soma raya mata wani abu game da chatting dinsu da Dawood... "Kinyi shiru .... " "Zan makara ne a school.." Ya dan matse hannunta da har sai da tayi yar kara. Ya kuma saka hannu ya lakuto kumatun ta. Kafin yace, "Saura 1 hour 30 minutes ku shiga lectures... Ai inada timetable dinku. Dan Allah kiban hankalin ki nan. Ki auna zance na. Tabbas ni me lefi ne awajen ki Waheedah... Nayi miki lefuka da dama wadanda na ke neman gafara awajen ki a koda yaushe. Amman this particular one da nake jajantawa Waheedah ki yafe mun. Soyayyarki ce ta jawo haka. Na dade zuciyata na neman begen kaunar ki. Na kasa sukuni. Waheedah kece FARIN CIKIN ZUCIYA tah.. kaunar da nake miki Waheedah dadaddiya ce,.. Har hankali na ya gushe na nemi samun soyayyar ki ta hanyar fito miki a zummar ni.... Ni....ne Dawood." Yana karasa fada ya runtse idanun sa. Hawaye suka shiga kwarara daga idanun sa... Ya zare ta daga jikin sa. Ya zube gwiwoyin sa a k sa ya durkusa agabanta. Ya janyo hannuwanta duka biyun ya rike . Ahankali cikin murya tamkar ana busa sarewa. Cikin wani salo ya shiga cewa, "Soyayya na iya chanja mutum, domin ita soyayya ba'a ganin ta balle a koreta ko a hana ta shiga ZUCIYA. Ba'a cewa soyayyah ga yadda ake so, sai-dai kayi yadda take so. Ba'a shiryawa soyayya, ko babu shiri Idan tazo kamar mutuwa haka zata shiga ZUCIYAr mutum. Duk wanda yayi so dan Allah to shine keda riba, Waheedah soyayyar ki ce ta dasar mun da FARIN CIKI har tayi tsiro