Sashe 94
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Wuraren la'asar Rahima ta farka daga bacci tana dan mika ganin yarinya a kusada ita tana bacci hankali kwance yasa tasaki murmushi tana kallon yarinyar kafin tamika hannu ta taba kuttubeben kumatun yarinyan tana dan murmushi sanan ta janye hannunta ta tashi ahankali tazauna, idanunta ne suka sauka kan wayan Nabila dake ijiye kan side drawer, wani irin faduwa gabanta tayi ahankali tace "Mummy na" waigawa tayi ta kalli kofar dakin ganin a kulle babu kowa yasa dasauri tasauka daga kan gadon, wayar tadauka tana kallon kofa saikuma tayi kofan data tabbatar cewa na bayi ne ta shiga, maida kofar tayi tarufe tasa sakata sanan tabude wayan tana addu'a Allah yasa ba password aiko taga babu, number Mummy ta shiga sakawa hannunta har rawa yake tai dialing number saidai harya gama ringing ba'a dagaba, sake dailing tayi akaro na biyu wayan na gabda tsinkewa aka daga kafin Mummy tai magana tace "Mummy nine Auta, call me please kar agane nakiraki in kudin wayan yakare" jin muryan Rahima yasa da sauri Mummy tace "to to" katse wayan tayi takirata back da sauri Rahima ta dauka muryanta narawa sosai tace "Mummy na ya jikin ki kinji sauki?" murmushi Mummy tayi tana shiga daki ta maida kofar ta tarufe harda saka key gudun karajita ta shiga bayi tace "awwwn don't worry about me naji sauki, I have to be strong 4 u Rahima na, ni kadai ce on your side in this whole planet I need to help you, ya kike" kasa amsawa Rahima tayi tafashe da kuka sosai tana tuna yanda jikin Mummy yayrudu rudu tace "Mummy na are you sure kinji sauki? Narasa yanda zanyi nakiraki banda waya I've been so worried bama na iya bacci da kyau, Mummy nagaji da komi ke kawai nakeso nagani, Mummy please help me wajenki nakeso nadawo am not happy at all Mummy, kaman ina cikin keji tareda aljani nakeji am so scared of him sabida karya zaneni, Mummy nima ranan saida yazaneni sosai sai jiya jikina yadena ciwo" tafashe da sabon kuka, cikeda damuwa Mummy tace "Rahima Rahima, Autana" ahankali Rahima tace "uhm" cikin kuka, cikin makirin voice dake kara dulmiyar da Rahima tace "listen to me Autana inhar ina rate aduniyar nan wlh babu wanda ya isa ya wahalar min dake, ba dukana ba ko kasheni Sameer zaiyi I must come and get you kuma gobe da shirina zanzo kema ki shirya kinji" da sauri Rahima tace "to Mummy" ahankali Mummy tace "anya kinsha abubuwan nan kuwa dan inda kinsha daban jiki da mugun sanyi hakaba, Auta na danasani dakeda tsiwa bata tsoron akwana balle tai yami, bakida energy, babu inspiration bakida vibe u sounds so dull, anya kinsha kuwa?" girgixa mata kai Rahima tayi tasa hannu ta goge hawayen daya zubomata ahankali tace "nakasa sha Mummy, inya kamani nasha zai iya kasheni wlh, Mummy mugune shi sosai gashi katoto, ko karkashin gadon banma kara lekawa ba tundaga ranan" sosai Mummy taji badadi ko kadan bataji dadin rashin shanta ba dan wanan mix din ko kaffara bazatayi ba in Rahima tasha sai kwakwalwanta yajuya irin mix dinan ne da yan shaye shaye nasha shikenan kuma saiya taba brain dinsu su haukace combination of crack ne da indian herm saikuma wasu kwayoyi da ake kira _Tsigai tayi yami amma sai bala'i aiki_ tun ranan data kawo take kasa kunne taji an kwantar da Rahima a hospital amma taji shiru rasa yanda zatai tai magana da itane yasa kawai tai shiru ta zubama sarautan Allah ido, danne zuciyarta tayi tace "yamiki wani abune ya sadu dake?" ahankali tace "a'a ni am on my period ma" wani irin murmushi Mummy tayi tace "to yaushe zaki gama?" cikin yar muryanta tace "gobe is the last day, the fourth day, jibi zanyi wanka" gyadamata kai Mummy tayi tace "shikenan dudda gobe zanzo dole nafada miki wanan maganan for security purpose, Rahima in mutumin nan yazo zai sadu dake ke sai inda karfinki ya kare, dambe zakiyi dashi kome kika samu ki buga mai, keko zai kasheki da kuka gwara ya kasheki din amma karki yarda ki yardan mishi yay amfani dake dan yanayi ya zubamiki kanjamau kenan S, HIV, HIV baida cure yana zuba miki mutuwarki yazo kenan gashi ke bakison mutuwa, koba wanan ba dama nariga na tsine miki albarka inhar kika yarda ya sadu dake, Rahima inhar zaki iya budema wanda yama mahaifiyar ki lilis gaba yaciki ai keba yar halas bane, sanan baki kishin mahaifiyar ki, Sameer makiyin kine, makiyanki nahar abada, ko hannun ki bai kamata kibari yarike ba Rahima, Rahima banson nafadi miki ne, kuma baniso nafadi ma Abban ki dan nasan nagayamai Sameer yamin dukan fitan hankali saiya kusa kasheshi zai iya samun heart attack Abban ku ya tsufa but Rahima naji jiki sosai a hannun Sameer....." tafashe da kuka sosai daya wani irin mugun taba zuciyan Rahima event din ranan yadawo mata sabo fil arai, hawaye ta share tace "kiyakuri Mummy kinji, wlh sainasan yanda nayi na ramamiki, mugu kawai azzalumi, Mummy kiyi shiru in kina kuka jinake kaman zan mutu kaman in kashe kaina, Mummy banso ana batamiki rai am sorry Mummy....n.....a" tai maganan muryanta na rawa zata sake fashewa da kuka, murmushi Mummy tayi ganin ta dana tarkon da kyau tana kara yabama kanta wato tagama da zuciyan Rahima ne tatas da babu wani matsiyaci aduniyan nan daya isa yace zai shigo yafadi nashi Rahima taji, ahankali Mummy tai magana cikin muryan ban tausayi ta yanda Rahima zata kara dilmiyawa tace "is okay, am fine, zanzo na daukeki gobe garinma zamu bari gabaki daya, nakaiki wani gari daban da babu wanda ya isa ya ganki, gobe kawai ki zauna da shiri sanan ki ijiye kunnenki akasa, take good care of yourself kinji, I love you so much Autana, kin tuna wakan danake miki?" gyadama Mummy kai tayi cikin wani irin kuka mara sauti gwanin ban tausayi tana mugun kewan Mummy tace "uh.....mm" jin muryanta yasa Mummy cikeda so tace "I said is okay kinji, don't cry your Mummy is coming tommorow, and trust me I am coming da shiri na babu abinda ya isa yamin so karkiji tsoron komi, stop crying wipe your precious tears, dakiyi kuka gwara kowa na duniyan nan yayi da Autana tayi, oya oya goge fuskar nan tass Mumy's heartbeat" da sauri Rahima ta goge hawayen tanajin kaman duk duniya batada kaman Mummy, Mummy tace "yauwaaa Auta na, My little little Rahima, my ballarina girl, bari namiki wakan kiji" _"Rahima Rahimomi, ta burka uban tumbudi, tadinga uban karni, yan-yan-yaaaaaaa"_ kyalkyacewa da dariya sosai Rahima tayi harta manta tana ma cikin bayine cikeda shagwaba ta turo baki tace "Mummy nifa bana tumbudi" da sauri Mummy tace "wai wai wai ai kece tumbudi factory Auta, kinsan nono baya kosanki anhada miki da madara aiko dan jijjiga kadan burrrrr kin burko tumvudi" dariya Rahima tadinga yi kaman ba itaba aranta tana cewa uwa dabance yaushe rabon datai dariya haka niko nace Rahima bakisan dawa kike tareba, Mummy ne ta dakatar da ita tahanyar cewa "okay okay dariyan ya isa haka, jeki ijiyema masu waya waya, wait, a inama kika sami waya dan wanan ba number Sameer bane" cikeda dariya kan fuskanta tace "gidansu mukazo, wayar matar kanin shi ne, Mummy kinga tsoho ne duk kannenshi sunyi aure" da sauri Mummy tace "bashine nake fadamiki ba, yaki auruwa ne, wace jakace zata yarda ta auri mai kanjamau shima babanki baya bincike ne saisa nakeso nazo na daukeki mu gudu na kaiki chan wani gari" aranta tace "straight to gidan karuwanci" sanan tace "just stay put koki ganni da wuri ko akasin hakan, karki fadama kowa da zuwana, oya bye" murmushi tayi tace "okay bye Mummy na I love you sosai Mummy na mai sona" tabe baki Mummy tayi tace "bye my Auta, the apple of my eyes" sanan ta katse wayan.