← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 102

Sashe 9

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dan Murmushi Sameer yayi tareda daga hannu dan he hardly smile, ahankali yakarasa har inda mutumin ke tsaye dawani hadadden award a hannunshi, hannu yamikamai suka gaisa, sanan yamikamai award din suka rike atare yan media anata musu hoto sanan Marshal ma yazo yabashi hannu yace "congratulations Lieutenant you deserve it" cikeda girmamawa yace "thank you sir" sai bayan sun gama hoton sanan Marshal ya karbi 🎤 din yace "hearty congratulations to you Sameer I must say, you deserve this, you deserve it Lieutenant" ihu Hall din yadauka da tafi saida aka dan tsagaita sanan Marshal yace "will you mind saying some few things? Come and say something about how you feel today, bazaka bar this stage without saying anything ba" ya matsamai aka shiga tafi sosai, takowa yayi yahau kan abin rikeda award din ya kalli dumbanin mutane dakenan makil a hall din ana kallonshi kafin yasaukar da idanunshi kan table din da yan uwanshi kekai yana kallon yanda bakunan su yaji rufuwa tsabagen farin ciki, ahankali ya saukar da idanunshi kan Ummi dake kallonshi tana share fuskarta da handkerchief tana murmushi, for the first time yasaki full smile dinshi a cikin Hall din cikin natsassiyar muryan shi yana daga award din yace "Ummi! This award is for you Mum" oh wow, oh wow, awwwn aka dauka a hall din ana ihu yayinda Ummi ta fashe da kuka sosai dan abin was so emotional da sauri Nabila da Fadila suka tashi daga kan kujerun su sukazo wurin ta suna lallashinta sukuma mazan suna murmushi. Anatse yacigaba yace "everything that I archive in this life is because of My Mum, My father died 25yrs ago, my Mother is an Iron woman, no she is my super woman she train 4boys and she thought us many many great things, part of it shine be truthfully Sameer, and everything you want to do in this life do it wholeheartedly, because anything that is worth doing then is worth doing well, give it your best my son" yay maganan yana kallon Ummi da Fadila ke pating shoulder dinta, murmushi yasake yi yace "this award is for you Ummi, and I love you, alot!" akahau tafi har Marshalsaida yamai tafi, Ummi kuma kuka, ahankali ya sauka yataho sojoji na kamemai ana saramai tashi Ummi tayi tawani irin rungume shi, rungume ta back yayi shima feeling calm and happy, dago kanta tayi tareda manna mai kiss a goshi murya chan kasa tace "am proud of you Sameer" mikamata award din yayi ta karba ahankali sai kallonsu ake ana daukansu hoto sanan suka zauna akan kujera, Ya Muhammad yamika mai hannu tareda saramai, Nur ma saramai yayi Mu'az kam rungume shi yayi cikeda murna yace "I love you Ya Sameer dina" kanshi Sameer ya shafa yace "love you too Kiddo" turomai baki yayi alamun baya so yana kiranshi kiddo hararan shi yayi, Nabila tace "congratulations Yaya Sameer" murmushi yadanyi yace "thanks Mum Princess" Fadila itama tace "congratulations yayan mu" itama dan murmushi yasakan mata dan baicika wasa dasu ba kuma yana mugun respecting nasu bamaya kirasu da sunansu yace "thank you Mum Little" shafamai kai Ummi tayi hakan yasa ya kalleta kafin ahankali ya rungumota suka cigaba da kallo program din har aka gama promoting sojojin dama su 18 za'a karama girma bayan angama akwai after party da su 18 din dudda Sameer baya ciki suka hada dan bai cika son hayaniya ba, yan uwansu suka hadamawa da abokan arziki, dudda yabasu kudi but ko kadan he's not interested, gamawa akayi tsaf sanan aka chanza wutan Hall din zuwa disco ball akai clearing babban stage din, sai wurin abincin serve yourself ne kawai akwai farin wuta aka fara rawa, tashi Nur yayi yamika ma Nabila hannu yace "let's go and dance baby" dan satan kallon Ummi Nabila tayi akunyace ganin hankalin Ummi baya kansu yasa ta tashi sukai gaba, Ya Muhammad ne shima yatashi yana daga Fadila sukai stage suma, kaman zaiyi kuka Mu'az ya kalli Sameer yace "Ya Sameer nima naje please?" dan hararan shi Sameer yayi kafin ya kalli agogon hannunshi shadaya da rabi yace "go but we all are leaving by 12, so you have 30min Ummi needs to rest and sleep" murmushi Ummi tayi she luvs it yanda komi Sameer zaiyi she is always first a lamuran shi, tafiya Mu'az yayi da gudunshi yarage su kadai akan table din, wayarshi yaciro daga aljihu dayaji tai vibrating sakonni ne keta shigowa Baffa yagani hakan yasa yabude sakon ya karanta sanan ya kalli Ummi dake ta kallonshi yace "is Baffa Ummi he's congratulating me, yace gobe shida family shi are coming over, bai dade da sauka ba" ahankali Ummu tace "kamai Allah huta gajiya ya gaida Maman su Aisha" gyadamata kai yayi ya shiga typing itakuma ta juyar dakanta tana kallon stage din yanda su Muhammad da matansu ke rawa irin couple dance dinan anatse gwanin ban sha'awa, juyoda kanta tayi ta kalli Sameer din dake shan bottle water, ahankali tace "Sameer kalli chan" ta nunamai kan stage, ajiye ruwan yayi ya kalli inda take nunamai, ahankali tace "basu burgeka ba? Kalli kanenka Sameer, inda ace Nabila batai barin cikinta na farko ba da yanzu yaran Nuru biyu, jibe Muhammad dat got married last year yanzu baby girl dinshi is 2month old, look at auta yanda yake girma yatasa shima, he is 25 now, Sameer so kake duka kannenka suyi aure subarka kosokake saiki tsufa tukunna zakai aure, bazakai aure ba tun da kuruciyan ka uhm Sameer....." "excuse please!" maganan dasukaji daga kansu yasa duk suka daga kai, wata doguwan budurwa ce tana sanye dawani red dinner gown dayamata kyau sosai, ta makala ID card awuya daya nuna ita media personality na NTA news ne, hannu tamika ma Ummi cikin harshen ta na turenci mai shegen dadi tana murmushi tace "congratulations Ma what an amazing son you have here, I must say you are bless Ma'am" dan murmushi Ummi tamata ta karbi hannun nata data miko mata tace "thank you" ahankali yarinyar ta kalli Sameer da yaciro wayarshi yacigaba da dannawa kaman bai gantaba, cikin harshen turenci yarinyar tace "please can I borrow your son just for few minutes, please Ma'am, plsssssss" taja please din tana hadema Ummi hannu looking so desperate, babu alamun wasa akan fuskanshi yace "am busy right now, can't come with you" yanda yarinyar tai kaman zatai kuka tana kallonshi da dukkan alamu dai sunsan juna yasa ahankali Ummi ta dafa kafadar Sameer ta gyadamai kai tace "kaje Sameer bakasan me takeson fadama ba" karara taga rashin son hakan akan fuskarshi amma sanin baya iya mata musu yasa ahankali yamike tsaye wani irin murmushi yarinyar tayi tace "love you Mum thank you so so much" tabi bayan Sameer din da sauri, fita sukayi har outside d Hall din ya tsaya agefe yace "wat?" kallon yanda mutane ke kallonsu tayi gashi yanda yamata maganan was so embarrassing dan yadaga murya, dan matsowa gab da shi tayi kaman zatai kuka tace "please Lieutenant, for the sake of your Mum let's go to my car mutane sunyi yawa anan" Ummi data kiramai yasa ya bita har inda tai parking motar tata Toyota camry bude bayan tayi ya shiga tarufo sanan ta zagayo ta dayan side din itama ta shiga tareda rufo kofan, cikeda seriousness dan bai tolerating nonsense yace "wat, why did you drag me here?" matsowa kusada shi tayi sosai tareda kama hannunshi, ahankali takai hannun saitin bakinta tama hannun kiss sanan ta kallai murmushi kwance kan fuskarta tace "congratulations on your promotion and award, am so proud of you Sameer you deserve it" karban hannunshi yayi daga cikin hannunta yace "thanks" yasa hannu zai bude kofan da sauri muryan ta har rawa yake tace "please no, ka tsaya" tsayawa yayi batare daya juyo ya kalleta ba, da sauri tawani irin fadawa bayanshi jikinta har rawa yake ta kankameshi gam, hannunta kan chest dinshi da breast meat dinshi sunyi bulbul tsabagen workout tafashe da kuka sosai. "Sameer please mesawai bakason aure? I love you so much dan Allah ka aureni kaji inata jiranka am not getting younger anymore am 28 Sameer please" hannunshi yasa yacire hannayenta dake kan kirjinshi sanan yajuyo ko kadan babu rahama akan fuskarshi yace "this should be the last time dazakiyi trying such thing dani Aliyya, bansan ki, you are not getting younger that is your choice kinada masu sonki so choose one and get married, Aliyya for Godsake don't you get it? Kokin aureni bazakiji dadina ba am not ready for anything marriage, I don't know I can't even imagine tayaya zanyi rayuwa da nace amatsayin matana my property please ki taimaki kanki trust me am not the right man for you" yana fadin haka yabude motar yafita tareda dajan tsaki yarinyar nan has been bothering him disturbing wayarshi da calls tun ranan data fara ganinshi da aka gayyace shi NTA danyi hira dashi, baima san tayaya tasami number shiba, and shi ko kadan batamai ba bama hakaba shi baitaba ganin macen datamai ba aduniyan nan, to yanada ma wani lokacin matane?.
Chapter 9 · 0% Book details