Sashe 28
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan juyowa yayi ya kalleta cikeda natsuwa yace "anything local meal Mama" wani irin murmushi tayi tace "shikenan Lieut" ta kalli Rahima tace "bani plates let's serve ko" gyadama Mummy kai tayi ta tashi, Mummy kuma ta kalli Abba tace "Abban su meza'a zuba muku?" kallon chairman Abba yayi yace "mezaka ci Chairman" dan dariya yayi yace "fried rice is okay" jin haka yasa Mummy tace "angama" plate din Da Rahima tabata ta karba ta dau wani ta zuba white rice da beans agefe, sea food stew ta zubamai dayaji sea food tasa spoon tadaura kan tray, sanan ta dau wani portable bowl tazuba pepper soup tadaura kan mini tray din tace "Rahima dauka ki kaima Lieut" dudda tsakanin su baifi 2 zuwa 4 feet ba saida ran Rahima yabaci ganin Abba na wurin yasa ta dauka ahankali ta mike tana tafiya kaman batason yi tana kallon Sameer din da bamaya kallon inda suke hankalin shi hakan zancen dasu Abba keyi, karasawa tayi kusada shi tadan duka zata ijiyemai abincin agabanshi daidai shima ya juyo suka hada ido, gyalen data yafane akafada ya sauko hakan yasa idanunshi suka sauka kan wuyanta da jelan kitson kanta suka sauka awurin, turo baki tayi ta ijiye agabanshi ta tashi tsaye, cikin wani irin murya na wanda ya cika fam kaman zai fashe da kuka tace "akwai wani abu dakake bukata?" dan haka Abba yakoyamusu tun suna yara inhar yay baki sukai serving na bakin su tambaye su if they need any other thing that is how to make your guest comfortable, tsayawa yayi chak yana kallon fuskanta, this is the first time daya bama fuskarta 1min attention, a kumbure ganin iskanci dayake mata yasa tace "eh?" cikin wani irin yanayi nako ajikinshi yace "me kika ce? Can't hear you?" kafin tai magana Mummy tace "kiyi magana da kyau mana Auta bakowa kejin yar muryarki ba" turo baki tayi idanunta suka cika da hawaye ta kallai kaman yanda yake kallonta da kyar tace "nace dawani abu dakake so namaka?" ba yabo ba fallasa yace "get me a fork" juyawa tayi fuuu tai kitchen dinsu, Mummy ta shiga zuzzubawa kowa na dakin abinci, dawowa tayi rikeda fork shi kadai a hannu tuk kafin ta iso Mummy tadan Harare ta tace "haka akemaba bako abu? Jeki daura fork din on a very nice plate ki kawo" sjarr hawaye ya zubo mata ta mugun gaji juyawa tayi takoma kitchen din ta dauro fork din kan plate tadawo tazo har gabanshi ta ijiye mai, sanan tajuyo Mummy tanuna mata kusada ita tace "zoki zauna kici abincin ki kowa nacin abinci banda ke" zama tayi kusada Mummy, Mummy ta shafa kanta tace "me zaki ci eh?" makema Mummy kafada tayi kaman a idanun Abba yace "zuba mata abinci taci, so kike ciwo ya kamaki" zuba mata fridge rice Mummy tayi dan kadan sanin bazata ci, karba tayi tadan saci kallon Abba ganin hankalinshi nakan Abincin dayake ci yasa ta kalli Mummy dake kallonta girgiza mata kai tayi, hakan yasa Mummy ta shafa kanta tace "please eat Rahima ko kadan ne" tai maganan tadan saci kallon Sameer dayakai tamarin juice bakinshi yana sha anatse. Ahankali ta shiga cin abinci kadan kadan shiru akayi dakin tsit anacin abincin, Mummy gabaki daya tarasa sukuni bata sakan talatin cikakke bata saci yanda Sameer kecin abinci ba baimasan tanayi ba, almost 30min suka dauka sunacin abincin sanan aka gama su Siddiqa sukai clearing falon tass, Chairman ya kalli Mummy yace "I really enjoy your food Madam, I must say Chief judge is lucky to have you wlh, saisa kullum he is looking fresh" dan dariya Mummy tayi cikeda jin dadi Chairman ya yabeta Abba yay murmushi, ahankali Sameer yace "thank you so much for having us Sir" yadan kalli Mummy yace "it was such a nice meal Mama, I really enjoyed it" tashi tsigan jikin Mummy yayi sabida yanda yay maganan cikin wani irin yanayi tana kallon fuskarshi tace "Allah Sameer" gyadamata kai yayi yanadan gyara zama, ahankali tace "to ko nagode muku naji dadi yanda kukaji dadin abincina" ajiye toothpick Abba yayi ya kalli Chairman yace "sai asan juna ko yanzu Chairman, gani ga Family na nan duk kun gani" dan dariya Chairman yace "ahhh what can I say, as you all know nine chairman din NDLEA, ni family man ne, matana yarana 6, 5 boys 1 girl, my eldest son yana University yana karantan computer engineering, sauran yara mazan duk secondary school suke, macen kuma bata fara school ba har yanzu breastfeeding nata akeyi" Abba ne yace "masha Allah Allah ya raya mana, in sha Allah one day I will bring all my family over mu kulla zumunci" da sauri chairman yace "da izinin Allah kuwan" shiru akayi Mummy takosa Abba ya tambayi Sameer nashi, kaman Abba ya shiga zuciyan ta yace "Lieutenant kaifa" dan murmushi Sameer yayi yace "actually ahhh, well I don't have much to say" wani irin ajiyan zuciya Mummy tasauke tana kara gyara zama tana kallonshi tsigan jikinta har wani irin tashi yake in yana magana. cikin calmness dinshi yacigaba yace "nine first born din gidanmu, the eldest, I have 3 brothers, mu hudu maman mu ta haifa, my Dad is late" ahankali kowa na dakin yace "Allah ya jikanshi" dan murmushi yayi yace "Ameen, so that's all akaina" da sauri Mummy tace "are you single Sameer, bakai aure ba?" gyadama Mummy kai yayi batare daya kalleta ba yace "not yet Mama" da sauri Mummy tace "how old are you? I mean shekarun ka nawane?" wani irin kallo Abba yama Mummy dan he felt somehow datai tambayan dan tana shiga privacy nashi ne a yanzu, he already told us abinda yakeso musani game da shi why asking him wasu questions kuma. Dan juyowa Sameer yayi ya kalli Mummy ido cikin ido yace "39 Mama" Mummy wani ruwa yafara dan tsiyayo mata the way he looked at her right in the eyes and say to her face he is 39 was damn sexy, goosh Sameer is hot wlh, dan murmushi tayi tabude baki zatai magana Abba yace "yaudai kin dawo yar jarida wifey" dan dariya Mummy tayi tace "Alhaji just wanted to know Lieutenant better ne kasan kona nema mai mata tunda yadawo tuzuru" tai maganan tana kallon Sameer dan dagokai yayi ya kalleta kafin yasake dauke kai, ahankali Abba yace "to Alhamdulillah, Siddiqa kutashi kutafi dakinku ku kwanta" tashi duk sukayi Rahima ma ta tashi zata bisu Abba yakirata. "Rahima" da sauri tajuyo ta kalli Abban, da hannu yamata alamun tazo yace "come back here" dawowa tayi ahankali tazauna a inda Abba ya nuna mata akan kafet a tsakar dakin duk sukai shiru a falon, tashi Abba yayi yahau kan kujera yace "kutashi kuhau kujera please" tashi duk sukayi sukahau kan kujera harda Mummy duk aka natsu, gyaran murya Abba yayi yace "to Alhamdulillah ina farin ciki da irin wanan rana" ya dubi Chairman da Sameer yace "a yanzu na daukeku Family na najini, aduniyan nan banda kowa ni kadai mahaifiyata ta haifa kafin daga baya ta rasu, gona biyu data barimini dasu na shiga dakaina makaranta harna dawo mutumin nan da kuka gani yau zaune agaban su, saisa dudda kudina I try as much as possible naga ina rayuwan rufin asiri sabida nasan duk wani wahalhalu na rayuwa, banda haka kuma randa komi zai kare wanda ba'a fata my family will be able to survive, bakomi nasa Rahima should stay back ba inaso ka dauketa amatsayin yarka ne" yadafa Chairman sanan ya kalli Sameer yace "Lieutenant inaso kadau Rahima amatsayin kanwarka kuhadu kumata fada, d'a na kowa ne, mutum shi kadai baya ya kula da danshi sabida idanu biyu kacal Allah yamai, but by the time aka hadu ana kula da yaron idanu dayawa akanshi yaron yasan da haka saikaga ya natsu, baran muku karya ba duk cikin yaran nan nawa dakuka gani banda fitinanniyar yarinyar, yar bala'i, da tonan fada, rashin kunya da rashin ji kaman Rahima ba, nasan Rahima bataji wanan bazan taba musawa ba amma bansan rashin jin yakaiga harta Tara abokanai na banza kuma maza harsu dorata kan shaye shaye ba, bansa abin yakai hakaba, sonake kumata fada sosai da sosai" Abba yay shiru yana kallon Rahima da kanta akasa, Chairman ne ya nisa yace "Rahima ki daure ki rabu da iyayen ki lpy, nasan kowa baya tsallake kaddaran shi but abokanen banza kaika suke baro su halaka maka rayuwa, ki rabu dasu baki babu su daga yanzu kinji" gyadamai kai tayi ahankali Sameer na kallonta.
Ahankali Chairman yace "saura kai Lieutenant, mezaka fadama kanwar naka" dan nisawa Sameer yayi ya gyara zama yace "In Islam Shaye Shaye is forbidden, na farko akwai manufofin shari’ar musulunci guda biyar akwai ;
1- حفظ النفس kiyaye rai
Duk wanda yasha taba, yasha su shisha, codeine, tramadol da sauran su dakeda illa akan lafiyan shi domin kwayoyine masu kashe rayuwan dan Adam, duk sun shige anan da duk wani abu da mutum zai sha ya cutar da kansa. Sai na biyu
2- حفظ المال kiyaye dukiya
Duk wanda barnatar da kudi ta hanyar busa hayaki, ya kone kudinsa haramun ne, duk wanda yay amfani da kudinsa ta wata hanya ta barna wanda wulakantar da kudin bazata dawowa d mutum amfani ba haramun ne.
3- حفظ العقل kiyaye hankali
wanan shima yana daga cikin manufofin shari’ar musulunci, ba’a yarda mutum yasha abinda zai gusar masa da hankali ba ya kasa banbancewa tsakanin maman sa da kanwar sa, ko ya dinga ganin sama ta koma kasa da sauransu, wanda duk kayan shaye shayen nan sunasa hakan kinga wanan haramun ne.
Ahankali Chairman yace "saura kai Lieutenant, mezaka fadama kanwar naka" dan nisawa Sameer yayi ya gyara zama yace "In Islam Shaye Shaye is forbidden, na farko akwai manufofin shari’ar musulunci guda biyar akwai ;
1- حفظ النفس kiyaye rai
Duk wanda yasha taba, yasha su shisha, codeine, tramadol da sauran su dakeda illa akan lafiyan shi domin kwayoyine masu kashe rayuwan dan Adam, duk sun shige anan da duk wani abu da mutum zai sha ya cutar da kansa. Sai na biyu
2- حفظ المال kiyaye dukiya
Duk wanda barnatar da kudi ta hanyar busa hayaki, ya kone kudinsa haramun ne, duk wanda yay amfani da kudinsa ta wata hanya ta barna wanda wulakantar da kudin bazata dawowa d mutum amfani ba haramun ne.
3- حفظ العقل kiyaye hankali
wanan shima yana daga cikin manufofin shari’ar musulunci, ba’a yarda mutum yasha abinda zai gusar masa da hankali ba ya kasa banbancewa tsakanin maman sa da kanwar sa, ko ya dinga ganin sama ta koma kasa da sauransu, wanda duk kayan shaye shayen nan sunasa hakan kinga wanan haramun ne.