← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 102

Sashe 62

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tareda Dr da receptionist din takiramai yadawo, Dr magidanci ne sosai dudda ba lallai ya haifi Sameer ba but Rahima kam ya haifeta, yana rike dawani dan babban kit da kayan aikinshi ke ciki, dan knocking kofar dakin Sameer yayi dan yasan yabarta tai wanka kafin yabude kofan ahankali ya shiga Dr biyeda shi yakafa mata idanu ganin baccinta take shrarawa ga towel akasa daga chan ta cikin gadon kuma kayan dayasayo musune bata mayar cikin ledan ba, maida idanunshi yayi kan fuskanta daya kara yin ja sosai kaman allergies din yakaru sai pink lips dinta dayay jajir shima na irin mai zazzabi, towel din data daura akanta yadan zame kasa hakan yabama gashin gaban kanta daman fitowa sun tattare and all coiled up kaman na karaman baby, kallon Dr yay yace "common in" shigowa Dr din yayi yana kallon Rahima dake bacci yace "is she the patient?" gyadamai kai Sameer yayi yakarasa gaban gadon ya daga towel din dake kasa ya shiga bathroom ya ijiye sanan yafito ya zauna kan kujera ya kalli Dr yace "kaduba ta" karasawa jikin gadon Dr yayi yabude kit dinshi dake kasa yadauko wani dan tocula yarike hannun yana kallon yanda fuskar nata yay wani strange red kaman jini yataru a fuskan yajuyo ya kalli Sameer da hankalinshi kekan TV yay wanan zaman nashi looking well compose and serious yace "yallabai yarinyar nan is her skin reddish haka kokuma bahaka bane?" yatsa Sameer yadan kada yadan kalli fuskarta kafin ya kalli Dr yace "she's not this reddish, just normal fair girl" gyadamai kai Dr yay yamaida hankalinshi kanta ya kunna torchlight dun dayake rikedashi yadan duka
yaja naman idanunta yabude idanunta ya haska da tocula hakan yasa tabude shanyayyun idanunta da sauri jin haske a kwayan idanunta, cire hannunshi Dr yayi daga fuskarta yace "sannu kin tashi, tashi ki zauna naduba ki, am a Dr, and am here naduba ki, sorry kinji tashi ki zauna muga" ahankali ta tashi ta zauna tana dafe kanta da kaman zai fadi akasa ta janye bargon daga jikinta, yanda Dr yaga tana rike kanta yasa yace "sannu" yay maganan yana dauko stethoscope da abun auna bp ya makala yakama hannunta yadaura ajijiyanta, wani irin tashi tsigan jikinta yayi hakan yasa tawani irin sosa wuyan ta cikeda gajiya da yanda tsigan jikinta ketashi ahankali Dr yace "sorry kinji" yadan juyo ya kalli Sameer dayay kaman baya jinsu idanunshi kan wayanshi dayake duba wani sako yace "officer yarinyar nan is suffering from chronic allergies she came in contact with kodai something da jikinta bayaso kokuma wani abinci taci da jikinta is trying to reject, and she is having maleria, akwai kuma yunwa tattare da ita, zan samata ruwa yanzu sabida karfin ta yadawo zanyi allura ciki dazaisa tadawo normal, sanan zan rubuta maka wasu magunguna da bandasu anan you should go and get them for her tasha sanan taci abinci and tasha fruits, anjima da daddare zan dawo nasake dubata in drip din yakare nacire mata" gyadamai kai Sameer yayi batare dayace komiba, Dr ya tsugunna yadauko wani drip ya sagale shi a jikin kan gado ya tsaya chak, sanan yadauko allura, tana ganin allura tabare baki takoma cikin gado da gudu tana kuka tace "dan Allah karkamin allura, in kanama iyayen ka karkamin kaji" kallonta Sameer yayi itama cikin kuka ta kallai tana girgiza kai hakan yasa towel din kanta yakarasa warwarewa yafadi akan gadon tace "dan Allah kar amin allura" dan dariya Dr yayi yace "opisa wanan kanwar takane ko Hajiyar ka zance anyi raguwa anan" yay maganan yana dan rage tsawonshi a gabanta, yamika hannu zai kamo hannunta takase komawa chan karshen gadon da sauri, wani mugun kallo Sameer yamata yace "give him your hand right away" gyadamai kai tayi kirjinta na bugawa sosai tana goge hawaye da dayan hannunta, tadawo inda take zaune ahankali ta zauna, hakan yasa Dr yakarbi hannun yana murmushi ganin yanda take kuka yace "yauwa muga hannun ahankali zan miki" sake bare baki tayi tace "to kabani magani wlh zansha Allah amma karka samin alluran nan ajikina" ta karbe hannunta ta boye hannun abayanta tafashe da kuka sosai tace "dan Allah kabarshi kabani magani zansha wlh wlh please" hada ido sukayi da Sameer wani mugun kallon dayamata yasa ta bashi hannunta tareda runtse idanunta da karfi, daure hannun Dr yayi da igiya sabida yasami vein sanan ya soka allura ahankali dudda hannunshi babu wani zafin kirki amma saida ta kurma ihu tace "Mummy, wayyo Mummy zafiii" dan dariya Dr yayi yace "a'a kace yar Mummy ce, saisa kikeda wanan uban rakin, to angama" bude idanunta tayi tana kallon hannun da Dr yamata fixing drip.

48.....

Dr yadauko prescription sheet na hospital nashi yarubutamai magungunan sanan ya hada jakan yarufe yatashi yana gyara zaman eye glasses din idanunshi hakan yasa Sameer yatashi yamikamai hannu yace "thank you Dr" murmushi Dr yayi yace "bakomi saina dawo dubata anjima da night, makesure taci abinci yanzu dan saitaci abinci zata iyashan drugs dinan dazaka bata" ahankali Sameer yace "in sha Allah" sanan Dr yamusu sallama yawuce yafita tareda mayar musu da kofa yarufe, komawa Sameer yayi yazauna kan kujeran dayake kai yadaga land line din yakira hotel kitchen din dan kusa da landline din an rubuta various number places a hotel din kaman su reception, kitchen da bar, da sauransu, ringing daya kitchen din suka daga yace "I want fruit salad, anddd" yay shiru yadaga kai ya kalleta har lokacin hawaye take sharewa tana kallon hannun da aka makala mata drip din sai kawai ya dauke kai yace "fried rice with water, the one that's not cold" ya maida wayan ya ijiye, wayarshi ne dake kan jikinshi ya shiga ringing da sauri yadaga wayan ganin Ummi ne yasa yatuna bai sanar da ita bazai dawo gidaba kuma inba tafiya ba koyaje wani assignment a outside Abuja ba, baya taba fashin kwana agida, dudda Ummi na bacci da wuri amma yarasa ya akayi duk in bayanan take notising koda baidawo gida da wuri bane tasani, ajiye landline din yayi yadaga wayan yana kallo, answering call din yayi ahankali yace "Ummi na" yanda yafadi Ummi na saida Rahima tadago kai ta kallai cikeda mamaki dama wanan masifaffen sojan na ragema wani murya haka haladai mamanshi ne.

Cikeda dan bacin rai Ummi tace "I call to ask you one single question, just a question Sameer" dan faduwa gabanshi yayi dagaji yasan Ummi tai fushi dashi sosai, tace "na lura kasoma zama man of your own yanzu Sameer, you feel kai keda kanka you have the right to do duk yanda kaga dama, naji kuma nagane Sameer, tambayata itace incire idanuna ne akanka kawai na zuba maka ido?" shiru yayi yakasa amsata hakan ya mugun tunzurata ta dakamai tsawa. "answer me Sameer, nace in cire idanuna ne akanka na zuba maka idanu, dan I see no reason dazan dinga damuwa akan ka, sabida ka rainani Sameer kaga ka girma saika tashi bazaka kwana agidaba kuma kaki kira ka sanar dani eh Sameer and inama magana you kept mute kaman wanda yahadiyi dalma" cikeda damuwa ahankali yace "am sorry Ummi, please" tashi yayi akan kujeran yadan juyo hada ido sukayi da Rahima da tunda yafara wayan take kallonshi kaman yauta fara ganinshi harara ya balla mata yawuce yafita daga dakin, ya sauka chan kasa, garden din Hotel din yashiga yazauna kanwata kujera mai kyau tashan iska shi kadai awurin yasake dialing number Ummi din danta kashe cikin fushi jin baya amsata, saida wayan ke gabda katsewa ta dauka tai shiru batare datai magana ba hakan yasa cikin kwantacciyan murya irin ta lallashi yace "am sorry Ummi na, dan Allah kiyakuri kinji" cikin fushi tace "ban neman hakurin ka, just tell me kana ina yanzu haka?" dan jim yayi 1st policy din rayuwan shi shine baya karya ko zaka kasheshi baya karya, instead of yay karya to gwara yay shiru kawai yaki baka amsar tambayan ka koda zaka tsinemai ne. "kana jina kai shiru Sameer?" ahankali yace "ina Gombe Ummi, am sorry I was on my way coming back home da magrib jiya issue came up da dole I had to attend, Ummi am sorry karkiyi fushi dani kinji" cikin kakkausan murya Ummi tace "mekaje yi a gombe Sameer?" dan jim yayi kafin yace "aiki ne, anjima kadan zaki gani a news Ummi, news din will be a all kafafun yada labaran duniya" dan ajiyan zuciya tasauke tadamu da situation din Sameer saisa any abu nashi yake tadamata da hankali, jin tai shiru batace komiba yasa yace "I am sorry, rushing to the place nake saisa I couldn't call you nafada miki zanje aiki Ummi, kiyakuri kinji, kinyafe min?" ajiyan zuciya ta sauke tace "naji nayafema Allah maka albarka" murmushi yayi yaji wani sanyi aranshi tace "yaushe zaka dawo?" ahankali yace "tommorow or next tommorow" "okay daman Mu'az yadawo gida dazun nan wai ASUU sunje warning strike na 2weeks" gyadakai yayi yace "eh yafadamin yamini text, tunda yadawo gida tell him nace yaje farm house yataya su ishak aikin dana sasu" ahankali Ummi tace "tom zan gayamasa gamashi nan ya shigo yana jinka tunda yadawo yadaman wlh Sameer danai magana yace wai shine Auta haka autanni keyi, am fed up fa, ni yakoma school yazauna yajira su gama warning strike din tunda just 2weeks ne yafimin" dan murmushi Sameer yayi yace "put him on the phone Ummi" kafin ma Ummi tabashi wayan Mu'az ya fizge jin Sameer yace abashi, cikeda murna yana wani irin murmushi yace "Ya Sameer ina yini" yay maganan yana tashi daga kusada Ummi yay dinning da gudunshi Ummi tabisu da kallo tana murmushi tanason yanda yaranta keson junansu duka saisa ko kadan batama Sameer fada agabansu shima Mu'az shigowan shi kenan yanzun nan duk fadan datama Sameer ba a idanunshi bane.
Chapter 62 · 0% Book details