← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 102

Sashe 93

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"p....ls Ummi.....na" yay maganan muryan shi na breaking sosai, sosai Ummi taji she can not longer go on with this fight, tai missing Sameer dinta bana wasaba sauran yaran basa wani kula da ita kaman yanda Sameer ko tarinta yaji sai yace me kikeso Ummi, Sameer always put her first, dagokai tayi ta kallai ahankali irin kallon nan nayaya zanyi dakai hakan yasa Sameer yakama hannunta yakai kan fuskarshi ya lumshe ido, sharrr wani hawayen yazubo daga idanunshi, wani irin jawoshi Ummi tayi tasashi ajikinta ta rungume tana kokarin hana kanta kukan datakeji tace "sabida kaga ina sonka ina dagama kafa Sameer saisa kakemin duk iskanci da kaga dama, kanamin kashi da fitsari akai, for 39yrs kaki yarda kai aure sabida yanda nake sonka nakasa maka dole dan banson kayi rayuwa da abinda bakaso saisa koda kanunamin bakason Asiya ban zafafa abinba dan nasan ba'ama namiji dole, ya auri macen dabayaso wahala zatayi, shine zakaje ka auromin yar shaye shaye listen I might, might forgive you but I will never accept yar shaye shaye as my daughter in law nagayamaka, and stop crying, you are my Soja crying is for the weak men and my boy is not weak right?" gyadamata kai yayi ahankali yana dago kanshi daga jikinta, hannunta tasaka ta sharemai fuskan tass tai murmushi ganin kaman bashiba tace "is alright nahakura amman as far as am concern baruwana da yar shaye shayen daka auro" hannun Ummi yakama ahankali yana kallon fuskanta he don't know why but anytime aka kira Rahima da yar shaye shaye he feels bad, zuciyar shi batamai dadi, ahankali yace "tadena Ummi, am changing her bazata karaba, ko damaba badan kanta tayiba...." tabe baki kawai Ummi tayi tadan tureshi alamun batason maganan batare data cemai komiba, kwantar da kanshi kan cinyarta yana sauke ajiyan zuciya sosai taji yabata tausayi ahankali ta shiga bashi head massage tana tunane tunane ahaka bacci yay awon gaba da shi awurin.

Nabila data shigo daukan ma princess apple daga fridge din Ummi ne taga Rahima ita kadai afalon tana share hawaye da bayan hannu tausayi tabata sosai, Apple din tadauko tadawo inda take tace "Amaryan mu tashi muje shashin mu duk muna chan" ta dauketa ta tafi da ita chan flat din Noor dasuke ciki da ita, su Noor ne a falo da Muhammad da Mu'az sai Asiya duk suna buga game da sabuwar ps6 din da Sameer yasaima Mu'az, suna ganin Rahima duk suka natsu wani natsu suna wani murmushi adole ga matar yayansu ta shigo,

Daki Nabila tai da Rahima inda Fadila ke tare da yaransu tana musu wasa, zama duk sukayi sukahau hirada ita suna janta da magana amma takasa amsasu sai kallon kyawawan yaransu take dudda yaran duk Black beauty ne dan iyayensu bakake ne amma sunada wani irin kyau da kiba da kana ganinsu sai sun baka sha'awa, har azahar daga bayama bacci ne ya kwasheta ganin tana gyangyadi yasa Fadila tace "ki kwanta mana Rahima kin zauna kinata gyangyadi" gayamata kai tayi tacire katon gyalen daya isheta taijiye a gefe ta kwanta ahankali tareda daura kanta afilo sai bacci, dauke kai Fadila tayi daga kallonta ta kalli Nabila dake rikeda Princess datai bacci tace "wlh ina bala'in sonta, ni yarinyar burgeni take gashi batada magana shiru shiru, I trust Ya Sameer nasan komi yazo karshe tunda dai ta shigo hannunshi" Nabila tace "hakane, ga kyau kaman ita tai kanta kinmasan menene Fadila, anytime inna kalleta sai naji tana tunamin da Ummi, sai inga kaman tana yanayi da Ummi intai wasu abun saikuma inga kaman idanuna ne kemin gizo hala sabida ina tausayinta ne" dan dariya Fadila tayi tace "nikuma kinga bangani ba, bari kiga naje wajen Baby tun dazu bansashi a ido ba" hararanta Nabila tayi tace "wato yanzu kinsaba babu zancen kuka da tsoro kuma ko" kyalkyacewa da dariya Fadila tayi tace "wuce nan, ai tunda na haifo Amra nasan kar harkan shi kanshi Baby yanzu mamaki yake wai ashe zan taba dena kuka" dariya Nabila tayi tace "adaiyi ahankali Amra is just 2month plus kafin kije kiyo mata kani ko kanwa jarabatu" dariya Fadila tayi tafice daga dakin falonsu tayi daidai dukansu ukun na shigowa dan masallaci sukaje wajen Muhammad tayi ta mikamai Amra tareda kama hannunshi tarike tana kallonshi, murguda baki Mu'az yayi yana kunkuni yace "akama anata lalatamu ana soyayya agaban yara" da sauri Muhammad yace "mekace?" washe baki yayi yace "ni ba dakai nakeba" murmushi kawai yayi ya kalli Fadila yace "muje flat dinmu I want to sleep" ficewa sukayi, Noor ya kalli Asiya dake kallo abinta yace "Asiya je ciki kicema Nabila ta samen in my bedroom" tashi tayi da sauri cikeda girmamawa tace "to Yaya" dakin tabude ta shiga kallo daya tama Rahima dake bacci tadauke kai ta kalli Nabila tace "Anty Ya Noor yace kisamai in his bedroom" murmushi kawai Nabila tayi tace "ganinan" tashi tayi ahankali gudun kar Princess ta tashi ta kwantar da yarinyar kusada Rahima sosai sai sukai kwanciya kaman uwa da y'a na bacci sanan tai murmushi tajuya tafita daga dakin tareda maido musu da kofa tarufe.
Chapter 93 · 0% Book details