← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 102

Sashe 2

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude kofar falon nasu tayi ta shiga daidai Auta dake shirin shiga corridor ta waigo jin anbude kofan, harara ta balla mata cikin murya kasa kasa tace "mayyar tabiyoni" dawani irin gudu Siddiqa tanufota dan taji metace wato itace mayya, ganin Siddiqa tabiyota da gudu yasa ta yunkura zata gudu amma ina Siddiqa tariga ta chapke bayan riganta ta fizgota azuciye ta bugata da bangon corridor cikin fushi tace "uban waye sa'idawa? Su waye zasu shanye miki jini sanan wakike cema mayya?" zaro idanu tayi cikeda rashin kunya tana kokarin ture hannun Siddiqa data chakumo gaban white t-shirt dinta tace "me haka? Kika batamin white rigana wlh saikin wanke shi, ki sakeni nace ko" bude kofar wani daki dake corridor akayi wasu yan mata guda biyu suka fito duk sunfi Autan girma alamun yayyunta ne suma dake kama da Siddiqa sosai, black beauty dasu, daya daga cikinsu wacce daga gani ita kebin Siddiqa tace "yauwa Ya Siddiqa cimana uban mara kunyan shegiya mai idanun mazuru" cikeda tsiwa tana kokarin ture hannun Siddiqa ta kwace kanta tace "eh kekuma mai idanun gapiya, gapiyan ma maicin kashi" dariya tayi sosai tace "eh gwaradai gapiya maicin kashi da mazuru mai satan kaji, kinji Ya Siddiqa lallasata dama atike nake da ita" bude wani kofa akayi dake facing corridor alamun dakin shine kodai master bedroom kokuma dakin wani babba agidan ne, wata matace baka itama Siddiqa na kama da ita sosai ta fito da akalla zatai shekara hamsin da hudu 54, dattijuwa ce amman jikinta nada kyau sosai tana sanye da doguwan rigan atampa da aka mata stone work hayaniyan dataji yasa tafito agurguje daga bayi dan tun dazu tana bayi ganin yanda Siddiqa ta chakume Auta yasa da sauri tajawo kofar dakin tanama Siddiqa wani irin mugun kallo tace "me haka kika chakume auta kasheta zakiyi?" cikeda fada dajin haushi Siddiqa tace "Mummy wai yarinyar nan nida Ya Sadiq zata kalla tacema sa'idawa, sanan wai zamu shanye mata jini, kuma wai ni take cema mayy......" da sauri Auta ta chabe maganar cikin muryanta mai zaki da dadi kaman zatai kuka tace "Mummy karya take mini, aini bance hakaba, sune keta kallona kuma sai hararana Ya Siddiqa takeyi fa, ni banmata komiba daga dawowa na" kafin Mummy tai magana Siddiqa ta bugata da bango tana jijjigata tace "dan ubanki nike miki karya, bakida kunya ko sabida kinga kinyi girma kema kin fara nono" cikeda jin dadi Lubabatu Mai bin Siddiqa tace "yauwa Ya Siddiqa ki gurje shegen bakin datake mana rashin kunya dashi abango, shegen bakin kaman tsuliyan kaza" harara Auta data fara kuka ta watsama Lubabatun tafashe da kuka tace "muguwa kawai, agulmawiya, ai nadai fiki nonon kumadai, da fuska ki kaman burnt abinci" yowa wajen Lubabatu tayi cikin son ta jibgeta tace "dani kike?" Lubabatu tai wajen ta daga hannu zata sharara mata mari Mummy ta daka musu tsawa. "Siddiqa! Luba!" duk dagokai sukayi suka kalleta, harara Mummy ta zuba musu tama Siddiqa dahar lokacin ke chakume da Auta tace "cikamini yarinya kafin na mugun sabamiki" sakinta ahankali Siddiqa tayi da sauri Auta tai wajen Mummy tafada jikinta tasaki kuka, cikin kuka tace "Mummy kinga Ya Siddiqa ta shakemin wuya kasheni takeso tayi, Mummy kice mata karta karacemin nafara nono banso" tafashe da kuka sosai, ta tsani insuna fada suce mata sabida tafara nono ne kaman su take musu ranshin kunya ta tsani maganan, shafa bayanta Mummy tayi cikeda lallashi tace "zan musu magana, ta Allah batasu ba kinji, je wuce dakinki kiyi wanka zan kawomiki abincin ki yanzun nan" gyadama Mummy kai tayi tasa hannu tana share hawaye tawuce sumi sumi sanan ta juyo ta kalli yanda suka tsaya charko charko suna kallonta wani matsiyacin murmushi tayi irin na neman tsokanan nan sanan tama Siddiqa da Luba gwalo, da sauri Luba tace "Mummy kinga tana mana gwalo ko" da sauri Auta tabude kofar dakinta ta shiga, kwafa Luba tayi cikin konkoni tace "wlh gamuwata dake bazatai kyauba, nakama yarinya wlh sainai mata jina jina saidai duk abinda za'amin amin" cikeda fushi Mummy tace "mafashi, inbaki daketa ba kin raina Allahan daya hallice ki, shegiyar yarinya yar bala'i kawai, da katon kanta kaman na giginya" bude kofa Luba tayi ta shiga tana magana ciki ciki tana kunkuni tace "badai kaina ba kan autanki dai" daga murya Mummy tayi tace "me kikace dan ubanki?" turo baki tayi da kyar tace "aini badake nike ba" "kimayi kiga in ban zubar miki da hakora ba da ranan nan" Mummy tafada tana huci, tabe baki Zeenatu da tuntuni tana tsaye tana kallon draman batare datace musu komi ba tayi tajuya zata shiga dakin da sauri Mummy tace "zonan Zeenah" juyowa tayi tama Maman tasu kallon haushi tace "gani Mummy" binta Mummy tayi da kallo daga sama har kasa tace "nasan duk yayana kece slow poison, wanan dabakice uppan ba Allah kadai yasan me kike hadawa aranki, wlh ko kurjewa naga Auta tayi, kurjewa nace to wlh sainaci ubanki, wuce kije kitchen kihado mata abincinta kikaimata taci" hararan kofar dakin da Autan ke ciki tayi tajuya tai hanyar fita daga Corridor, kallon Siddiqa dahar lokacin ke tsaye idanunta sun cika da kwalla tap tsabagen yanda abinda Mummy tayi ya bakanta mata rai tayi, yarinya tazo tamata rashin kunya sanan tama wanda zata aura Ya Sadiq rashin kunya dudda haka Mummy batace komiba, murmushi Mummy tayi ta taho wajen kama hannun Siddiqa tayi suka fita daga corridor sukai falo cikeda lallashi tace "ya isa to kekuma, bakomi Auta zatayi kudingajin haushinta ba, yarinya ce, dududu guda nawa take aduniya eh? Daga ke har Sadiq din ai duk yayyinta ne? Yakuri kinji zan mata magana zata dena, wuce ki koma wajen Sadiq kinbarshi shi kadai, kuma ki saki ranki karya ganki duk wani iri yagane akwai matsala, nunama saurayi ake kana tsananin son dan uwanka, tashi kitafi" tashi Siddiqa tayi tawuce tafita daga dakin deep down bata hakura ba tai alkawarin saitaci uban Auta wlh.

Fitowa da Zeenatu tai daga kitchen rikeda plate da jellof rice kekai dayaji fried plantain akai yasa Mummy tace "ahaka zaki kaimata abincin kaman zaki kaima awaki? My friend go back to that kitchen ki daura abincin nan kan tray, ki dauko mango juice din dana hadamata kidaura akai da glass cup, ki kuma samata salad ki sako mata nama guda biyar kinsan tanason nama" juyawa Zeenatu tayi tana kunkuni tace "saikace president zan kaima abinci" kasan cewan Mummy bataji taba yasa ta gyara zama tacigaba da kallon datake yi, jin Zeenatu tasake fitowa yasa tadago kai ganin tayi yanda tace yasa tace "kuma wlh ko kallon banza kika mata sainaci ubanki, kina bata abincin kifito kinajina ko banso adameta bacci zatayi" gyadamata kai tayi tai corridor.

Bude kofar dakin Zeenatu tayi babu kowa adakin saidai karan saukan ruwa dataji alamun tana wanka, dakin fess fess sai kamshi yake, fentin dakin off white ne sai dan gadonta dakeda girma normal normal an shimfida bargo mustard, curtains dinta kuma combination of white and Mustard kana shiga dakin zaka gane mai dakin nason this two colors white da mustard, karasawa ciki Zeenatu tayi tana kallon cookie jar dake kan bedside drawer ta dako rabi basuyiba, suma sunada cookie din dan Mummy ke ijiye musu adaki yara sudan sami kayan kwalama but su harsun cinye nasu dayake su ukune da ita sai Ya Luba, da Ya Siddiqa, itako Auta dakinta ita kadai dudda ma tsabagen rigima da fadan dasuke yi ne yasa Mummy taraba musu daki but dudda haka shegiyar bata iya kwana ita kadai dakin kawai zamanta ciki da ranane kawai dare nayi takeyin dakin Mummy, Mummy ma saitai bacci take iya sneaking out ta tafi dakin babansu in yana garin in kuma bayanan to tare suke kwana, ajiye mata abincin tayi akan gado daidai lokacin tabudo kofan bayin tafito daure da mustard towel dinta akirji daya saukan mata iya cinya tana kallon Zeenah data ijiye mata abinci tana turo baki takaraso ciki tana hararan ta tace "me kikemin adakina dakin kine eh, kifita kona hadaki da Mummy wlh" hararanta Zeenah tayi saikuma tai murmushi cikin lallabawa ta kalli jar din cookies din tace "auta indan dibi cookies dinki?" wani kallo auta tamata saikuma ta balla mata harara ta zauna kan gado abinta tareda daukan tray din tadaura kan cinya zata faraci, ahankali Zeenatu ta zauna kusada ita murya chan kasa irin muryan begi begi dinan tace "haba yar kanwata Rahima naaa, indan dauka, 2 kadai zan dauka namufa yakare ne please" turo baki tayi ta make mata kafada ashgawbe tace "ba bakusona ba Mummy kadaine ke sona agidan nan, kuyita sa Dady namin fada, jiya saida kikaja Dady yasani nai wanke wanke bansan wani gulma kikamai ba, bazan bayarba" da sauri Zeenatu tadaura hannunta kan kafadarta aranta cewa take "shegiya mai shegen kafiya wacce bata mantuwa kawai, zaki gane kurinki ne yau" cikin sigan lallashi tawani jawota jikinta tace "kai, Allahu Rahima, to kiyakuri bazan karafadamai ba kinji Autan mu, yakuri, in dauka eh Autan Mummy da Daddy mu" wani irin murmushi tayi cikedajin dadi ta gyadamata kai tana gyara zama tace "dauki 10 nabaki duka" tashi Zeenatu tayi da sauri cikeda jin dadi tai wurin jar din tace "thank you Rims Auta" tadebi cookies din tai hanyar fita daga dakin sanan ta juyo ta kalleta ganin bata faracin abincin ba tana kallon abincin tace "kici abincin mana" yatsine fuska tayi ta dago kanta ta kalli Zeenatu tace "Ya Zeenah the food smell peprish wlh" aran Zeenah tace "mayya, ba Ya Zeenah ba ko Anty Zeenah zakice min bazanji tausayin ki ba, kinsaba kirana ai gasai, hancinta kaman na aljanna hartaji kamshin yajin" murmushi tayi tace "common ai Mummy bata bari asa yaji tasan bakison yaji, ci babu yaji ko kadan, natafi" gyadamata kai tayi tadebo rice din takai baki, maida kofar Zeenah tayi tarufe bayan tafito takafa kunnenta jikin kofar tana murmushi kaman an mata kyautan makka ba'a banza Mummy ke cemata kunama slow poison ba saitayi baxaka taba cewa ita bace ko zata iyaba, su Siddiqa da Luba biyemata suke suyita hauka tana haukata su, itako cin ubanta take ta karkashi.
Chapter 2 · 0% Book details