← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 102

Sashe 15

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiga cikin motar yayi ya rufo kofar sanan yadaura jakan nata akan jikinshi ya tada motar yaja ahankali, baya wani gudu dan baiso sukai department dinsu dawuri, soyake yadanyi hira da ita yanda yaci sa'a takula shi yau dinan, dan satan kallonta yayi sanan yace "who is she?" yadan kalleta itama kallanshi tayi wani iri yaji sabida yanda dara daran idanunta suka sauka akanshi da sauri ya kalli hanya yace "I mean who was that girl that made you cry?" daure fuska tayi cikin dan fushi tace "my sis, elder sis" dan yatsine fuska yayi cikin isa yace "tell her Chris yace today should be the last day dazata saki kuka haka inba hakaba saina rama miki" wani irin murmushi tasakinmai ta mugun ji dadin yanda yay maganan, kallonta yayi ganin tana murmushi yasa shima yay murmushi baisake cemata komi har sukakai department dinsu na Vet, tun kafin yayi parking suka hango lecturer ya shiga ajinsu kuma ka'ida ba'a barinsu shiga in lecturer ya shiga, dan ajiyan zuciya yasauke yace "wat a day! We are late" daure fuska tayi tamiko mai hannu tace "give me my bag I want to go, thanks for the ride" zare key yayi daga jikin motar ya kalleta yace "beautiful let's chat a bit now, lecturer yariga ya shiga please" harara ta watsamai cike da rashin kunya tasa hannu zatadau jakan da sauri ya fizge jakan hakan yasa bottle din codeine yafado kan kafarshi dan dama bata rufe jakarba bayan tadauko waya dazu, wani irin kwalalo ido tayi cikeda mugun tsoro ta kalli kafarshi kaman yanda shima yake kallon kafar kafin ahankali yamika hannu yadau kwalban dudda yasan codeine sosai danba bakonshi bane but yanaso yakara tantancewa shine yake gani bawai gizo idanuwanshi kemai ba, dago kai yayi zai mata magana takawo hannu zata fizge kwalban da sauri yadauka da hannunshi harda jakan yay sama hakan yasa karan wiwi shima ya fado kasa dagawa yayi tareda ajiye jakan agefe ya kalleta yanda yaga tai zuru zuru yasa yagane natane ita kesha bawani ba, ahankali yace "so you do drugs beautiful?" girgiza mai kai tayi ahankali muryan ta har rawa yake tace "n....no....banawa bane ba" fashewa yayi da dariya sosai harda rike ciki saikuma yadago kai yace "alright naji, lemme take them then" yashiga bude marfin zai kafa abaki kaman zatai kuka tace "karka shamin abuna wlh" sake kyalkyace wa da dariya yayi kafin yasauke ya kalleta yace "you don't have to lie to me am your friend and your secret is safe with me, besides codeine ai na yarane, will show you abubuwan dat will make you feel kaman kina heaven" dan kaiwa baki yayi yasha kadan sanan ya janye ya mika mata rufewa tayi ta fizge jakanta ta zuba ciki ta rufe, kallonta yake tayi shidai tana bala'in burgeshi ga shegen kyau kaman ita tai kanta, dago kai tayi ta kallai hada ido sukayi hakan yasa ta danyi murmushi tace "zantafi" murya chan kasa yace "before you go, how about I give you invite to my birthday is in two days Beautiful, you know I will feel honored if a beautiful girl like you will grace my occasion, please Beautiful" yay maganan yana ciro katin invite din daya hadu iya haduwa kallo daya zakama Chris din kagane shima iyayenshi nada dan kudi ba laifi, makemai kafada tayi tana kallon katin tace "once I live school bama fita again" da sauri yace "how about you attend the pre birthday party" da sauri tadan yatsine fuska tace "and when is that?" "tommorow 2pm, then ai muna school u can come and leave by 4 kitafi gida, and is just few people, please do dat for me My beautiful Friend kinji" shiru tayi tadan juya ido saikuma tace "okay I will think about it, to if I decide to go who is taking me to the place?" da sauri yace "give me your number Beautiful, I will enter school tomorrow just for you saimu tafi tare kinji her majesty" murmushi tayi yanda yake lallabata namata dadi tace "Tom" ta mikamai wayanta, karba yayi ya sassaka numbers dinshi yay saving da sunanshi sanan yabata, karba tayi tajuya tafita daga motan tanata waige waige harta sami kasan wani bishiya ta zauna, hango ta dayayi all alone yasa yafito yay wajen haka yadinga janta dahira harta saki jiki suka dinga hira yanata sata dariya cikinta har yana kullewa kaman dama chan sunsan juna daga wani wurin, kusan zaniya cewa Chris is the first friend datayi tunda ta shigo makarantar nan 100level 2months ago.

Karshe ma batai attending aji kodaya ba ranan motar Chris ta shiga yasauketa a unguwarsu tamai waving bye sai gobe sanan tawuce gida, sai murmushi take Chris is really funny and such a sweet guy yana treating dinta like a queen, duk duniyan nan banda Mummy that treat her like a queen shine second person that treat her like a queen tana zuwa xatabama Mummy labarin shi tayi friend a school yau.

***************
Washe gari.
Cikin full shiganshi na kayan sojojin shi ya shigo Barrack din da motarshi Bentley da plate number kana gani xakasan na sojane, parking yayi a inda aka tanada dan parking kafin yabude motar wasu sojoji da aikin su shine gadin wajen sukazo da sauri daya daga cikinsu yabude mai motar tareda saramai. "Sir!" ahankali yafito daga motar bakaramin kyau kakin sukamai ba, yafito cikin shi ganshi na sojoji, lips dinshi sunyi pink sosai kaman wanda ke mura, hannu yasa yazare bakin glasses din dake kan idanunshi sanan ya maida kofar yarufe yasa key a wando yajuya ya shiga building din, lift ya shiga dayakai shi 4th flour sanan ya shiga wani office da aka rubuta Lieutenant ajiki, shiga office din yayi yana kokarin zaro wayarshi dake aljihu data fara ringing, wayar yaciro ya kalla ganin Ummi ke kiranshi yasa yakarasa ya zauna kan hadadden kujeran shi sanan ya amsa wayan.
"Soja na ankai office lpy?" dan murmushi yayi da muryan shi mai natsuwa da dadi irin muryan full cikakken namijin nan yace "Ummi na, yes nakai inama cikin office yanzu haka, inaso nai some paper work ne yau, gobe ne zandanyi supervision na various post din mutane" cikeda jin dadi Ummi tace "Masha Allah karka manta katofa addu'a, Allah yakare ka daga shairin makiya, Baffan ku kana fita yana shigowa, yakawo ma rubutu wai kadinga sha" dan lumshe ido yayi irin na gajiya da zancen Baffan nan kafin yadan yatsine fuska yabude ido yace "okay" jin wani kira na shigowa wayanshi yasa yacire wayan daga kunnenshi ya kalli wayan ganin Mu'az ne yasa ya maida wayan kunnenshi yace "Ummi bye, Mu'az na kirana bari na amsa naji" "oh ba jiya jiyan nan yakoma school ba hope badai kudi yakeso ba, karka sake kabashi kudi Sameer kuna bata yaron nan da kudi dayawa jiya babu wanda bai bashi kudi agidan nanba harda Baffan ku" dan murmushi yayi yace "okay Ummi naji bye" "alright son bye" katse wayan yayi yana kokarin kiran Mu'az din kiranshi yakara shigowa hakan yasa ya amsa da wuri. "Mu'az" ya kirashi kai tsaye dan bai fiye wanan wasan ba, daga ta chan bangaren cikin dan dari dari wanda yadau wayan yace "Yaya Sameer Salisu ne, Uhnn Salisu abokin Mu'az na school ajinmu daya" dan shiru Sameer yayi dan Mu'az hardly bama wasu wayanshi meya faru yau abokinshi ya kirashi, kai tsaye yace "uhum Salisu" irin alamun yanajinshi, cikin tsoro tsoro da fargaba yace "Yaya Sameer Mu'az baida lpy, yanzu haka muna sick Bay tun jiya da daddare baisan inda kanshi yakeba, we tot he will feel better tun jiya saisa bamu kira kowaba but munga har yanzu ciwon kaman ma is getting worse ne" sosai yaji zuciyarshi tabuga dudda all his brothers he is not into them like that dan bayason raini ko kadan but yana sonsu sama da tunanin kowa barinma Mu'az da kusan shine ya raineshi dan lokacin Ummi was battling da rasuwan babansu which Mu'az was a year old daya rasu saisa yakeson yaron danshi yakemai komi a lokacin, natsuwa yayi dan part of training dinshi da akayi tun yana sabon soja shine dakewa and not to panic kodakan mutuwan iyayensu ne, su sojoji ne they're meant to protect lives not to sober, soja jarumi ne maikuma dakakkiyar zuciya, anatse yabashi tambaya kai tsaye. "meke damunshi?" cikin wani irin murya kaman Salisu zaiyi kuka yace "ciwon ciki ne, terribly ciwon ciki" shiru Sameer yayi yana sauraronshi. "juyi kawai yakeyi kaman ana zaremai rai yana kuka sosai shine naga yana yawan mana maganan ka kaine babban yayan su shine nafara kirana danna sanar dakai" ahankali yace "don't leave his side, ganinan zuwa" katse wayan yayi yatashi ya kalli agogon bango this is 8, akwai meeting dayake dashi by 5 Allah yasa bazaiyi missing meeting dinba, key motarshi yadauka yafito daga office din yasauka kasa, motarshi yabshiga yatada yaja motar da mahaukacin gudu yadau hanyar zaria.
Chapter 15 · 0% Book details