← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 102

Sashe 6

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Fitowan su Siddiqa yasa yajuya yana kallonsu kitchen duk sukayi harda Mummy suka shiga fito da kulolin abinci da tray, bajewa sukayi akasan babban falon Mummy tafara serving Abban su kafin ta zubama yaran, sallame sallan Rahima tayi ta jingina da kujera tana kallonsu duktai kalan tausayi, taba Abba Mummy tayi tace "dan Allah kayakuri Abban su aikin tubako Auta bazaki karaba ko?" gyadama Mummy kai tayi tana share hawaye tana turo baki, murmushi Mummy tayi ta kalli Abba tace "kagani bazata karaba, oya bama Abban ki hakuri" ahankali cikin muryan kuka tana kallon Abban tace "kayakuri Abba bazan karaba" murmushi Mummy tayi tana washe hakora tana kallon fuskan Abban daya daure batare dayace mata komiba tace "yauwa Auta na dena kuka Abban ki yahakura, bama yayyin naki hakuri suma" kallonsu tayi kaman yanda suke kallonta hawaye ne yazubo daga idanunta ta share sannan tace "kuyakuri" murmushi Siddiqa tayi tace "yawuce" murmushi Mummy tayi tace "yauwa oya zo wajena" kaman jira take da sauri ta tashi tazo tafada jikin Mummy tana rera kuka ahankali, Abba bai kara cewa komiba yacigaba dacin abincin shi yanajinsu yanda Mummy ke lallashinta, saida yagama sanan yatashi yafita daga dakin motarshi yaje yabude baya wani babban leda yadauko na Teems Pestry shop gabaki daya bacin ran da Rahima tasa shi yasa yama manta da tsaraban daya sayo musu sanan yadawo daki, Mummy yabamawa sanan yay corridor dan zuwa wanka ganin ana gab da kiran magrib, ice creams ne aciki Mummy tabude, murmushi tayi taciro biyu ta mikama Rahima dake jikinta tace "iyye kinga ice cream dinku jekisaka a freezer yay kankara kaman yafara narkewa anjima sai kidauko kisha" ahankali tasa hannu ta amsa ta tashi tai wajen fridge sanan Mummy ta cicciro daya daya ta mikama sauran yaran duk karba sukayi basu cemata komiba dan inda sabo sun saba kome Abba yakawo na Rahima double ne nasu dai dai, sawa a freezer tayi tadawo zama tai kusa da Mummy tai lamo akan hannunta, ahankali Mummy tace "nazuba miki rice kici" girgiza ma Mummy kai tayi tana yatsine fuska ko kadan batason cin abinci, abinci ma baya mata taste abaki yanzu, shiru Mummy tayi tana kallonta sanan tace "ankira magrib yi saikije dakina ki jirani zanje wajen Abban ku" gyadamata kai tayi ta tashi ahankali tai dakin Mummy duktai wani irin yaushi.

****
[7/7, 9:02 PM] +234 816 822 7336: 💫 _*BIN ABINDA ZUCIYA KESO*_💫

_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favour you always💔

✍️ M Shakur

5️⃣ & 6️⃣

Wani babban bedroom ne hadadden da everthing looks absolutely neat dakin sai kamshin turaren wutan yan maiduguri dakin yake. Mata biyu ne sunci gayu sosai wearing wani material iri daya da aka musu irin gown dinan da ake kira da dinner gown mai ruwan gold sun daura head black shima sunyi kyau kowacce na sanye da makeup akan fuskarta. Tsaye suke kan wata magidanciyar mata dake zaune kan kujeran gaban makeken hadadden mirror kwalliyan dake dakin, daya daga cikinsu namata daurin kallabi, murmushi matar tayi tana kallon matan biyun ta madubi yanda suka dage dauri sukemata, daya daga cikinsu ne dake left side din matar tace "Ummi kinyi kyau wlh sosai" murmushi matar da aka kira da Ummi tayi cikin natsassiyar calm voice dinta irin na kamilallun manyan mata tace "nagode Nabila" karasa daurin dayan tayi ta kalli madubin tana kallon fuskan Ummi ta mirror tace "yauwa angama Ummi" murmushi tamata tace "angaida Yusra sarkin iya daura kallabi" dariya Yusra tayi cikeda farin ciki compliment from Ummi kaman kyautan kudi ne dan Ummi bata fiye surutu ba ko kadan, tashi daga kan kujeran Ummi tayi ta kalli kanta a madubi ba karamin kyau tayiba wani mahaukacin lace tasa mai bala'in tsada mai ruwan gold dakeda tiny zanen flower na Black, tasaka wani sarkan zinare daya dace da shape din wuyanta da warwaron shi a right wrist dinta, ta daura fine agogo mai kyau a left wrist dinta, purse dinta tadauka Black tazura takalmi na vinci irin mara takurawan nan mai dadin tafiya tadauko wani hadadden mayafin ta yafa tadaga kai ta kalli babban agogon bangon dakin cikeda dan masifa tace "me suke bata lokaci haka ba 9 za'a faraba this is past nine shine har yanzu basu fitoba, bari naje na tattaro su su fito mutafi" tai hanyar kofa harzata fita saita juyo ta kalli matan guda biyu tace "Nabila kun tabbatar kun fadama Nani komi banson jikokina suyi kuka, makesure you set everything and tell the Nani all she needs to know" gyadamata kai sukayi atare, Nabila tace "to Ummi, ba zasuyi kuka ba matar ta iya kulada su sosai, yanzun nanma na dubosu har sunyi bacci kuma basa tashi cikin dare in sukai bacci sai gab da asuba dinan" gyadamusu kai tayi batare datace komiba tafice, fita daga flat dinta tayi tai wani flat dake bangaren wanda tafito daga ciki, shiga tayi bayan tai sallama babu kowa a falon hakan yasa tai bedroom kai tsaye tun kafin ta shiga takejin hayaniya, muryoyin maza suna surutu, bude kofa tayi ta shiga da sauri, tsit sukayi kaman basu ke uban surutu ba da akejin hayaniyar su har falo, maza hudu ne adakin, uku ne atsaye duk suna sanye da Black suit da bakaken cover shoe sunyi masifan kyau da covers kaman wanda zasuje dai wani babban occasion, sai dayan dake zaune kan gado yana sanye da wani green wando dakeda layi jaa tagefe kafarshi sanye da farin safa sai jikinshi sanye da singlet. Agogon hannunta ta kalla kafin ta kallesu duka one after the other tace a"hiranku kawai kuke tayi daman ba shiryashi kukeyi kuda kuka cemin zakuzo tayashi shiri, kunsan karfe nawa? Oya kuwuce kufita kuje falo matan ku najiranku kufito dasu kuwuce mota gamunan zuwa" ta matsa daga jikin kofan ta nuna musu kofa alamun suzo su fita, sadaf sadaf sukazo suka fice one by one har dukansu ukun suka fita sanan ta maida kofar tarufe tayo inda dayan yake zaune yana kallonta murmushi shimfide kan fuskarshi, karasowa gaban gadon tayi tasa yatsa ta dungure mai kai tareda zubamai harara tace "biyema kannenka kayi kunata surutu instead of kashirya gashi lokaci yayi" murmushi yayi batare dayace komiba hakan yasa tasake watsamai harara taja ledan dake gefenshi wanda rigan sojoji ne keciki, hannu tasa ta zaro rigan tana balle maballin tace "oya stand up" tashi yayi ahankali dogone sosai dan yamafi mahaifiyar tashi tsawo, murdadde ne bana wasaba, ga wasu shati shatin six packs dayafito ta white singlet din dake jikinshi, baki ne shi very dark, yanada wani irin bright white idanu da gashin ido sosai bakake gasu dogaye yanada cikan gira gawani siririn hancin shi dogo dayakara ma fuskar nashi kyau, bottum lips dinshi is so so pinkish sai upper lips dinkuma baki hakan yabama bakin nashi wani irin alluring kyau baida gemu ko daya hakama saje baidashi kodan sabida anhana sojoji ajiyewane saisa oho. Yanada cikan jiki dan ko kadan he is not skinny one element dayasa aka dauke shi a soja shine tsayin shi dake karamai kyau koyana cikin mutum dubu zaka ganeshi sabida cikan haibanshi da kwarjini.
Ahankali yamika hannushi ya zura cikin hannun rigan kaman yanda Ummi tabashi sanan yamika dayan hannun yasaka yana kallon fuskanta yanda take rufemai boturan rigan, Murya chan kasa yace "Ummi yaushe zaki dena treating dina kaman baby wai?" batare data kalleshi ba tana sakanmai boturin tace "inka girma"
Chapter 6 · 0% Book details