← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 102

Sashe 89

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Karfe shida da rabi yashigo gidan yana sanye da faran jallabiya yayi wani irin mugun kyau Black dinshi na shining kodan jiya ya zubar da sperm ne oho, dakinshi yabude ya shiga yabude wardrobe dinshi yafito da wani leda da aka Mum Ramlat Beskope yabude kofa yafita daga dakin at this moment bawai dan wani abuba dan kanshi kawai yaji he's ready to live with this gurl for the rest of his life and he is ready to change tlher to his perfect liking, dakinta yabude ahankali kwance ya ganta kan gado tana bacci bata kashe wutaba ta kankame filoli guda biyu kana ganin yanda take kwance kasan atsorace take, karasowa cikin dakin yayi ya ijiye ledan kan gadon kafin ya zauna ta bakin gadon yajuya yana kallon fuskarta, sosai take bacci gashin kanta dukya barbaje bakin sun kanannade, ahankali yakai hannunshi ya tattare coily hair dinta yamaida mata dashi bayan kunnenta kafin ahankali ta shafa kumatun ta cikin bacci tai wani irin murmushi daya lotsar da dimple dinta yasa tai wani bala'in kyau tasaki filon data kwakume ta kama hanunshi da sauri tasa a kirjinta ta rungume tana murmushi cikin bacci tasauke ajiyan zuciya ahankali, samun kanshi yayi da kasa tashinta da kasa karban hannunshi data tura a kirjinshi ya tsareta da ido, shi kanshi baisan exactly abinda yakeji game da ita ba but yasan his heart deeply pity her, yana wani irin jin mugun tausayinta saisa dudda yace yanason yay handling nata da harshness yake sausautawa dan is not easy yarinya from 12yrs ta taso da tsanar asalin mahaifiyar data kawota duniyan nan sanan ta taso kuma cikin mugun life da kishiyar mahaifiyata ta nuna mata amatsayin shine rayuwa mai kyau batare data bata any chance dazaisa tasan abinda takeyi is bad ba, sosai yake tunani yama manta da zaije daki ya chanza kayan nan zuwa kayan dazaisa yaje jogging, motsi tayi sabida hadadden kamshin daketa shiga hancinta, bude idanunta tayi ahankali tana kyafkyaftawa trying to fitar da all ragowan baccin dake cikin idanunta tana kara rungume hannunshi a kirjinta da kyau tana kallon Sameer din datake gani blur tana murmushi kafin idanunta sunyi clear tar tahada ido da Sameer dake kallonta asanyaye, wani irin zabura tayi tai kokari tashi jin ta kankame abu a kirjinta yasa ta kalli kirjin nata da sauri ganin hannun Sameer ta rungume yasa tasaki da sauri ta tashi ta jingina da bangon gado tana gyara gashin kanta daya zubomata gaba tana maidasu baya tana jan bargo tana rufe kirjinta dan wani dan figigin shimi ne ajikinta, ahankali tadago kanta hada ido sukayi hakan yasa tasaukar da kanta kasa da sauri ahankali tace "good morning" murya chan kasa yace "morning" duk sukayi shiru, murya chan kasa yace "what about the menstruation, kin gama?" yay maganan ahankali yana kallonta, girgiza mai kai tayi tace "no" "yaushe zaki gama? How many days does it take you to finish" wani iri taji dan bata sabaji maza na tambaya ba, Mummy ne kadai kemusu tambaya kan period ko Abba babu ruwanshi iyaka yasai musu kokuma yabama Mummy kudi asayo musu pad, ahankali tace "4 days" "gobe zaki gama kenan?" ahankali ta gyadamai kai tace "eh" gyadamata kai yayi batare dayasake cewa komiba yadauko ledan kayan dya shigo dashi ya ijiye a gabanta yace "arrange the house and fix breakfast for me, inkin gama dress in this cloth we are going out" gyadamai kai tayi kawai batare data kalleshi ba, tashi yayi ahankali harzai fita saikuma yaciro phone dinshi yadawo ya ijiye kusada ita yawuce yafita daga dakin, kallon wayan daya ijiye kusada ita tayi ta tashi daga kan gadon ta shiga bayi brush tayi tai duk wani abunda yadace batare datai wanka ba tafito daga bayin wajen gadonta taje tadau ribbon dinta daya zamiye tsabagen bacci ta kama gashin kanta sanan tadau wayanshi kasancewa rigan jikinta yasaukan mata har cinya tabude kofa tafito tana daddannawa wayan tana kunna data tai hanyar stairs ko kadan bamata kallon gabanta, YouTube ta shiga tana searching easy breakfast tana sauka daga stairs din gabaki daya hankalin ta nakan wayan wani irin turgudewa tayi kafinma tasan meyake faruwa tai gaba zata fadi akife ta kurma wani uban ihu tareda runtse idanunta, chak taji anriketa ita batakai kasaba ita bataji tafadi ba sanan ita tajita acikin soft hands, bude idanunta tayi ahankali kaman wata matsoraciya hada ido sukayi da Sameer daya tarota dan yana biyeda ita abaya soyake ya sauko ya kalli sunrise daily ganin tabata taba wayanshi ta turgude zata fadi tasa yatarota da sauri, kasa koda kwakkwaran motsi tayi tana kallon fuskarshi, fuskarshi adan daure babu alamun wasa yace "next time know when u are walking and know the perfect time to be pressing phone" ajiyan zuciya ta sauke tana kallonshi tama kasa magana, harara ya watsa mata yace "dagani" da sauri ta tashi tana gyara rike wayan nashi a hannunta sanan tajuya da sauri ta karasa sauka tai kitchen shikuma yabi bayanta da kallo.

Ruwan tea ta daura tasaka kayan kamshi aciki sanan ta fere Irish da abin ferewa ta soya Irish da scrumble egg sanan yazuba ruwan tea a flask ta gyara komi tawuce dakinta gyarawa tayi tana nishi dudda babu wani datti tafito tai kayen kayen falon sama dan shima ba datti, falon kasa daman shi baida datti dan babu mai zama ciki sanan ta kwaso yan dattin data hado tazo tawuce ta shiga kitchen ta zuba adan hadadden abin sharan dake wajen ta wanke hannunta tana fitowa taga Sameer zaune akan dinning yana kallonta hakan yasa silently tazo ta zubamai kujeran kusadashi yaja hakan yasa ta zauna ahankali yadau spoon yasa yadau flask yazuba musu tea sanan ya ijiye ya kalleta yace "let's eat" faracin chips din yayi shima taste great better than abincin jiyan ganin ya kalleta yasa tafara ci ahankali yanda ya tsareta da kallo yasa batada option taci abincin deep down he's feeling happy ganin tanacin abincin ahaka, this alone is improvement tasoma cin ordinary food saida suka gama ta tashi zata kwashi plates din takai kitchen yace "don't worry jekiyi wanka ki shirya" da sauri ta kallai ahankali yace "go" juyawa tayi tawuce tai sama yabita da kallo sanan ya tashi ya tattare abinda sukai amfani dashi yakai kitchen din yasan aiki ita kadai zai mata yawa yanaso ya dinga taimaka mata but he don't wanna make her lazy kodan sabida yanda ba tasaba yin komiba gwara yasa ta koya, wanke plates din yayi tass kaman ba Sameer ba ya ijiyesu inda yakamata ya kara gyara kitchen din tass yasake goge gas din datai girkin dashi sanan yafito yawuce sama shima dan ya shirya.
Chapter 89 · 0% Book details