← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 102

Sashe 61

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

_Alhamdulillah am back, stronger than ever in sha Allah, thanks for all your prayers, I love you all VIPs_

47.

"St.....stan....stand up from my body" yay maganan muryan shi nadan breaking, cigaba da duba jikinta tayi tana wani irin sauke ajiyan zuciya duk tabi tarude saida taga babu komi again sanan ta sauka daga jikinshi ahankali takoma kan kujeran datakekai tana kuka tsigan jikinta na bala'in tashi gawani mugun kunya datakeji ba riga ajikinta dan bazata iya saka rigan data cire ba ta kife jikinta kan kafafunta tana kuka tsigan jikinta na tashi, jacket din sojojin jikinshi yacire ya ijiye kan kafarshi sanan ya tube white light shirt din dayake sawa akasa uniform dinshi mara nauyi wacce take short sleeves, batare daya kalleta ba ya jefa mata rigan ajikinta yace "put this on, and stop crying" da sauri tadago kanta ta kallai ganin baya kallonta yasa tadau rigan da sauri tana kuka sosai tasaka, rigan na wani mayen kamshi mai shegen dadi sanan ta makure akan kujeran tana sauke ajiyan zuciya tana wani irin kuka mai tsumai rai, sunkai kusan 5min baice mata komiba yatada motar batare daya kalleta ba yabar wurin, wani irin abnormal ajiyan zuciya dayaji take saukewa yasa yadan kalleta, tsigan jikinta daya gani yana mugun tashi tai wani irin red reddish, farin fatarta yakoma ja ta runtse ido sosai tana kama jikinta, yanada Broad knowledge on many field kallo daya daya mata yagane she's having allergies and she needs treatment inba hakaba she can loose it, cikin Gombe ya shigo hakan yasa yadau wata hanya bata barin garinba ta shiga cikin garin yana gudu, acikin wani babban hotel yay parking mai suna Swiss Resort, Gombe.

Jacket din sojojin dake kan kafarshi batare dayasaka ba yadauka ya daura akan jikinta dan white shirt din daya bata is too transparent yace "put this on" sanan yafito daga motar babu riga ajikinshi yabude boot din motarshi kasan cewa baya rasa kaya a Booth dinshi yasa yabude wani leda wata white t shirt yaciro yasaka yamaida boot din yarufe ya zagayo ta inda take har lokacin tana kuka gashin kanta yay busu busu yace "wipe those tears and come out" share hawayen tayi tafito ahankali yabi yagaggun crock shoe din kafarta da kallo wani irin bala'in tausayi yaji tabashi he wish Abba zai ganta ahaka yaga irin halin daya jefa yarshi da kanshi ciki, maida kofar motar yayi yarufe yace "follow me" yay gaba tana biye dashi abaya, ahankali take tafiya dan kaman zata fadi takeji she is totally unwell ne, reception din ya shiga yanuna mata wani kujera yace "sit here" gyadamai kai tayi ta zauna ahankali tareda kwantar da kanta kan hannun kujeran juyawa kawai yayi yay wajen receptionist din yamusu booking daki ya karbi key yadawo inda take yana kallon yanda ta lumshe ido ahankali yakira sunanta yace "Rahima" ganin bata bude idoba yasa yadanyi tapping hannunta, bude idanunta dasukai jajir tayi ta kallai ganin she isn't well at all idanunta sunyi ja sosai yasa yamika mata hannu yace "let's go" ahankali tamikamai hannu ya riketa ta tashi tsaye da kyar sukai stairs har zuwa dakin dayakarban musu, bude dakin yayi ya suka shiga, dakin hadadden gaske gawani makeken gado dayaji farin bargo mai shigen taushi, hannunta yakama har zuwa bathroom yabude ya shigar da ita ciki har zuwa wajen wanka yace "shower I will be right back" gyadamai kai tayi yawuce yafita tareda rufomata kofan ya sauka kasa yaje wajen receptionist din yace "I need a Dr please, call Dr for me, and do you have any boutique around?" gyadamai kai tayi tace "yes sir, third floor boutique din yake, will call d Dr for you right away" lift ya shiga yatafi 3rd floor wani babban boutique ne hakan yasa ya shiga wasu fine dogayen riguna yasaimata guda uku sai simple gown mai spaghetti hand guda biyu, daya orange daya black ash color, yadau mata cream, sai takalmi da kai tsaye yasaimata 37 dan yaga batada kafa, sanan shima yasai t-shirt da wando, yabiya kudi akamai packaging nasu yafito sanan yakoma dakinsu, har lokacin tana bayi bata fitoba, kayan ya ijiye mata kan gado sanan yawuce yafita daga dakin yakoma motarshi ya zauna, hannunshi yamika yadau wayarshi ya shiga saka wasu nambobi kafin yay dialing number, kusan ringing uku aka dauka, cikin wanan voice din nashi na nuna babu wasa aciki yace "This is Lieutenant Sameer Simran Sameer I want to speak to Governor of Gombe state please" yay shiru kafin ya janye wayan daga kunnenshi, ko minti biyar ba'a daukaba same number daya kira yakirashi back hakan yasa yay picking.....

Takai almost 15 minutes wanka take da ruwan zafi da sabulen data gani a bayin wanda hotel ya ijiye musu, tadau shampoo da hotel din ya ijiye musu ta jujjuye akan kitsontadaya tsufa sosai yafara warwarewa dan dama dogayen kalabane dudda bata wani iya wanke kaiba tarage dauda kan sanan tasake wanka tai brush data dade bata samu tayiba dan hotel sunyi providing nasu da new brush da tooth paste sanan tadau towel ta daura akirji tadau wani karami ta daura akanta dan ya tsane ruwan tafito tana sauke ajiyan zuciya kanta najuyawa, dan kadan tabude kofa ta leka ganin babu kowa adakin sai TV dake aiki shi kadai yasa tafito dasauri tsigan jikinta na tashi, ledan data hango akan gado da bakin kaya yadan leko haka data gani akan gado cikin leda yasa tabude kofan tayi kan gadon, ledan tadaga ta zazzage kayan wanan mai spaghetti hand din orange color idanunta suka sauka akai dan bazata iya saka sauran manyan dogayen rigunan ba, da sauri tadauka tasaka babu komi acikin jikinta rigan kawai tazura kaman ya aunata rigan yamata kyau sosai yakara haska fatarta, anan kasan dakin ta yarda towel din data cire dan batada karfin komawa bayi ta ijiye gawani mahaukacin sanyin dataji tafaraji sosai hakan yasa tahau kan gadon taja bargo ta kudundune sosai tana sauke ajiyan zuciya ko minti daya ba'ayiba bacci yay awon gaba da ita mai nauyin gaske.
Chapter 61 · 0% Book details