← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 102

Sashe 64

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Tadade zaune awurin tana sauke ajiyan zuciya, sosai taji dadin jikinta dan yan ciwuwwukan datakeji sun ragu, sanan kurjewan datayi sun dena mata zafi kaman an zare zafin, yanzu burinta kawai ta ganta a jikin Mummy ta, tashi ahankali tayi dan fitsari takeji ta rike maganin da Dr yabata ta shiga bayi, brush tayi sanan tasake wanka da ruwan zafi kaman wata mai jego sanan ta goge jikinta duka da towel ta bude balm din ta shiga shafawa, tass ta shafe ko ina na jikinta dashi sanan tadau rigan data cire tasaka tafito daga bayin ta zauna kan gado tana kallon wayan Sameer daya bari kan kujera kaman taje ta dauka takira Mummy but tsoro take yakamata ahaka har gyangyadi yadan soma dibanta, bude kofan da akayi yasa tadan firgita tabude ido hada ido sukayi da Sameer daya shigo, maida kofan yayi yarufe sanan yajuyo babu ko digin wasa kan fuskarshi yace "kinyi salla?" yanda ya tsareta da idanu yasa ta girgiza mai kai ahankali batare datai magana ba yace "tashi kidauro alwala" ahankali ta yaye bargon datadan rufa dashi ta mike tsaye hartakai bakin kofan bathroom din saikuma ta tsaya ta juyo ta kallai hada ido sukayi da sauri ta saukar da kanta tana wasa da yatsunta cikin siriruwan muryanta tace "unnnn ai banda hijabi" batare daya kalleta ba yace "akwai hijab, jeki dauro alwala" bude bathroom din tayi ranta ko kadan ba dadi ta dauro alwalan sanan tafito taga harya shimfida mata dadduman daya dauko daga cikin motanshi ya fuskanci gabas shikuma yana zaune kan kujera daga zaune yanuna mata wardrobe yace "there's hijab inside" ahankali take tafiya kaman wacce kwai yafashe mawa aciki ta wuce shi tabude wardrobe din taga hijab ko sabo fil maroon, dauka tayi taciro daga ledan tazura yay mata kyau sosai gashi har kasa yakai mata yanaso yamata over yawa ma wani abu tahadiye sanan ta maida wardrobe din tarufe tajuyo tazo ta gabanshi zatahau kan dadduma remote yadauka ya kashe TV duka dake kara dan inda TV ke kallo ne gabas baison TV yay distracting nata, ahankali tahau kan dadduman, ahankali yace "turn around" dan juyowa tayi duktai zuru zuru ta kallai yace "daga sallan zuhur zaki fara, ahh kinyi subhi?" ya tambayeta without an atom of joke a magananshi, girgiza mai kai tayi hakan yasa yace "okay dana subhi zaki fara, kiyi zuhur, asir, magrib da isha'i" wasu hawayen bakinciki datake kokarin dannewa ne yazubo da sauri ta share sanan ta juya takabbarta tai subhi sanan ta tashi tai azahar da kyar kaman yasata aikin duniya gabaki daya takeji, sallamewa tayi tajuyo ta kallai hada ido sukayi dan yanabin yanda take sallan ne daki daki sallan ma akwai kuskure ciki sosai, hawayen daya cika idanunta ne ta share da hijabin sanan ta janye hijabin daga kan fuskarta ta kallai cikin irin muryan wanda ya cika yay fam gab take da fashewa dinan tace "nai sallan asuba da azahar dan Allah inbar sauran gobe sainayi? Kaga banda lpy" without any sign of remorse ko alamun yaji tausayinta yace "stand up kicigaba" fashewa tayi da kuka kaman dama jira take ta tashi tsaye ta kabbarta tana salla kuka, haka tai sallolin har isha'i kuka take tana sallame isha'i zata cire hijabi yace "remaining shafa'i da wuturi" jitayi dama wajen Wugugaga yabarta dayafi mata da uban sallolin nan dayake sata haka tai shafa'i da wuturi sanan ta sallame ta tashi tacire hijabin tai wurin wardrobe din tana goge kwalla sanin zai iya magana yasa ta linke hijabin tasa acikin wardrobe din tarufe tana share hawaye tazo tahau gadon takifa kanta kan gadon tana kuka ahankali, yana jinta bai kulata ba takai almost 1hr kuka take sanan yajita shiru bacci yay awon gaba da ita.

Wuraren shadaya yatashi bathroom ya shiga wanka yayi ya chanza kayan jikinshi zuwa wani pyjamas daya sayo yay brush shima dan baya iya bacci batare dayay brush ba sanan yafito yana kallon yanda take bacci, gashin kanta ba dan kwali sai kyalli yake dudda ba gyara, yariga yay shafa'i da wuturi a masallaci hakan yasa ya kwanta kan kujera inda ace yanatare da system dinshi dayay wasu ayyuyyuka da yawa amma babu, kujeran yamai kadan tsawo hakan yasa ya saukar da kafafun shi kasa dan yatsine fuska yayi yaja pillow case din kujeran ya wuwwurga akasa sanan ya sauko kasan ahankali ya kwanta tareda yin addu'an bacci ba'a wani dau lokaci ba bacci yay awon gaba dashi ance jiki da jini dole akwai gajiya.
Chapter 64 · 0% Book details