Sashe 8
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Vertical align emblem of cross sword and baton Marshal yadauka akan tray dawani soja yarike da aka shimfida red yafi haka akai, sai a star and Eagle duk ruwan gold ya makalamai su on both shoulder nan wasu sojoji sukahau busa trumpet na alamun ban girma, hawaye Ummi ta share tana murmushi she wishe his father was alive to witness this day jibi yanda ake karrama dansu, sai hotuna ake dauka ga yan news line awajen, an busamai sarewan na kusan minti biyar sanan aka gama, a ka'ida dama ana gamawa sojan da aka karama girman zai tafi yakoma wajen zamanshi yazauna, anatse cikin tafiyan shi na maza yafara tafiya zai tafi Marshall yace "not so fast Lieutenant, one more surprise for you" tsit kakajin Hall din, Ya Muhammad yace "Ummi kumu zauna ance akwai one more suprise" zama sukayi duk suna kallon stage din kaman suna kallon film. Anatse Sameer yakoma kan stage din tareda sake sarama Marshal ya kame, gyara microphone din bakinshi Marshal yayi yace "let's put our hands together for Alhaji Muhammad Mustapha Abdallah the chairman of NDLEA in Nigeria" Wani magidancin mutum ne sanye da bakaken suit sojoji biyu biyeda shi abaya suka taho sai tafi akemai yahau kan stage din yazo kusada Marshal ya mikamai hannu suka gaisa suna murmushi, Marshal yace "Muhammad Mustapha Abdallah was born November 13, 1954 in Hong, Adamawa State, He is a Nigerian Professional Security Officer who currently serves as the Chairman and Chief Executive Officer of National Drug Law Enforcement Agency after he was appointed into the post by President Muhammadu Buhari on January 11, 2016. He didn't just come here to grace this occasion No, he came for something even bigger amma karku manta ance waka abakin mishi tafi dadi ko" aka shiga tafi Marshal ya matsa gefe mutumin yana dariya yahau wajen tareda gyara 🎤 din yay gyaran murya yace "bakomi yakawo ni nan ba saidan muzo muyabama integrity, honesty dakuma jarumtar wani soja ba, da bai discrimination ta hanyar cewa ni soja ne wanan ne aikina wanan ba aikina bane a'a baya wanan, mutum neshi dat feels duk wata matsala data shafi kasarmu Nigeria inhar yagamu da ita zaiyi abinda yadace batare dayajira wasu ba ko ma'aikatan kan abinba, soja ne dat always put his country Nigeria first kafin kowani Al amari, soja ne daya tak amma tamkar sojoji dari, soja da sabida ayyukan shi ayau Nigeria zata buga kirji tace rate din production din kayan maye, kayan shaye shaye da yan shaye shaye sun ragu dakusan 30%, soja ne daya tak worth sojoji miliyan, I am here to present an honourable award of honor and recognition to non other soja than man of honor, man of the moment, man of integrity, a man that live for his country, can we all stand for Lieutenant General Sameer Simran Sameer!" yawani fadi sunan da karfi wani irin ihu aka dauka a hall din su Mu'az, Muhammad, Nuru da matayenshi tsalle suka shiga yi Ummu dai handkerchief tadaura akan idanunta tana share uncontrollably hawayen farin ciki dasuka shiga zubo mata non stop.