Sashe 68
Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Har cikin Rehab din ya shiga sanan yafito yana kallon yanda take kuka har lokacin, ya zagayo yabude mata kofa yace "come out" fitowa tayi tana goge kwalla dasuka kasa saina zubowa yace "idan kikai mistake din sake guduwa daga nan wlh sainabar mahaifinki ya maidake kauyen" girgiza mai kai tayi cikin kuka da sauri tace "wlh bazan gudu ba, dan Allah banso na koma kauyen nan" tasake rishewa da kuka, dauke kai yayi yace "follow me" office din likitan dayamata registration receptionist takaisu likitan na ganinta yay dariya yace "oyoyo our run away patient, munsan zaki dawo all your things are intact, gadonki ma haka" yana maganan ya kwalama Asabe kira. "Asabe" da sauri Asabe ta shigo sanye da kayan security dinta, Rahima yanuna mata dake gefen Sameer tana share hawaye yace "take her, let her change to uniform" shigowa tayi tai wajen Rahima tareda kama hannunta tace "mutafi" binta Rahima tayi tana waigen Sameer da yabisu da kallo tana kuka sosai mara kara Asabe tarufo musu kofan, kallon Dr Sameer yayi yace "hope babu wani matsala and she's not too late?" da sauri Dr yace "not at all Lieutenant, babu wani matsala ai patient naguduwa haka is not new, adawo dasu and we continue with the treatment, burinmu subar shaye shayen kawai" gyadakai Sameer yayi yace "take extra care of her please, asamata ido sosai, like I don't even mind nai extra payment inhar zaku sata on 247 watch" ahankali Dr yace "you can count on that, basai ka biyaba, normally wayanda suka gudu aka dawo dasu anama chanza musu daki, dakin daza'a mai dasu bazama su dinga fitaba all treatment nasu anan ake musu sunda bayinsu awajen and security da nurses dake kula dasu basa barin wajen, karka damu I assure you baxaka ji bad news din da kaji da ba" gyadakai Sameer yayi tareda mikamai hannu suka gaisa yace "thank you Dr, I'll be on my way now" "alright Allah kiyaye hanya" wucewa yayi yafita tareda shiga motarshi yarufe yafita daga rehab din yadau hanyar dazai kaishi gidan Baffa shi gabanshi nadan faduwa, wayarshi yaciro while driving yay dialing number Baffa yakara akunne, ringing daya Baffa yadauka cikeda girnamawa Sameer yace "barka da rana Baffa" daga tachan bangaren Baffa yace "barka da maraice dai Sameer, abinda yay karfe biyar da rabi ai yay dare" gyadamai kai Sameer yayi kafin ahankali yace "Baffa kana gidane ko wajen aiki inaso nazo na ganka" cikin yanayin magana na manya Baffa yace "too ni gani a gidanku nazo nemanka kaima kana nemana, kazo nan gida kawai ina jiranka, gani nan tareda mahaifiyar ka da kannenka shigowan su kenan ma sun taso daga wajen aiki" ajiyan zuciya Sameer ya sauke yace "to gani nan zuwa" kara gudun motarshi yayi harya shigo anguwarsu dake nan sabuwan GRA, horn yayi aka budemai mota tun kafin yay parking Mu'az yafito dagudu yazo wajen parking space din ya tsaya, parking Sameer yayi murmushi kan fuskarshi yabude motar yafito da gudu Mu'az yazo yace "oyoyo Ya Sameer" yafada jikinshi, kanshi Sameer ya shafa yace "how you?" dagowa Mu'az yayi ya kalleshi ashagwabe yace "fine Yayan mu, Yayan mu I miss you wlh tunda nadawo kai tafiya bakanan, ya hanya?" ahankali Sameer yace "lpy lau" sanin Mu'az cikashi zaiyida surutu yasa yace "Baffa na falo ko, let's go"