← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 102

Sashe 17

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Wani top dinta na Dorothy perkins white and sky blue ne shima long sleeve tazaro daga hanger tasaka, rigan yadan saukar mata dan yarufe mata bombom, wani long fashion necklace tasaka daya saukar mata kan rigan, sanan tadau veil dinta white zata yafa da sauri Mummy tace "no kiyi wanan hadadden daurin nan dakika iya" murmushi tayi harda dan gudunta takoma gaban madubi ta zauna ta shiga daurin, tsaf tai daurin dayadan bada v shape ta gaban goshinta ya mugun mata kyau, wani takalmi mara tsini sosai Mummy ta dauko mata white karba tayi tace "laaaa Mummy na ya akayi kikasan shi zan sa" dariya Mummy tayi tace "I know your dressing humor" murmushi tayi ta shiga saka takalmin Mummy sai kallonta take harta gama ta mike tsaye Mummy tabita da kallo ba karamin kyau tayiba kaman wata celebrity, ita kanta jikin Rahima na mugun burgeta batada wanan girman jikin, she looks small, batada wani tsayin kirki bata da kiban kirki but her organs are so full, bumpy and super package, tanada hips da boobs bana wasaba gatada yar karaman kafa, ga karamin jiki, irin matayen nanne da ake kirada too perfect yan charass chass, wayarta ne yay ringing hakan yasa Mummy tadauko wayan dake kan gado tana kallon screen din tace "gashinan ya iso, yi sauri feffesa turarukan ki" fesa turare ta shigayi masu bala'in kamshi sanan ta karbi wayan daga hannunta ta sa akunne. Cikin wani murya mai dadi Chris yace "Hi Beautiful, am outside" ayangance tadan murguda baki tareda juya ido tace "okay am coming" baki Mummy takama tace "Autaaaa" fashewa da dariya tayi tafada jikin Mummy, Mummy tace "kinga shida tamiki agidan nan dudda yau Abban ki baya gari amma dai kidawo da wuri kinji, muje narakaki nima naga Chris dinan da babyna ketamin maganan shi tun jiya" tana rikeda wayanta suka fito tareda Mummy, mayafi Mummy tadauko afalo sanan suka fito tare su Siddiqa na falo binsu sukayi da kallo barin Rahima dataci shegen gayu kaman zata gasan kyau tana balla musu harara, har wajen Gate Mummy tarakata da hannu tanuna ma Mummy motar Chris dake pake a gab da gate dinsu karasawa sukayi ganinta tareda wata yasa Chris yabude mota yafito yaci gayu na bala'i dan gemunshi da ajiyan tagani bakine yau taga yakoma dark blue yama gemun tiri kalan sneakers din kafarshi yasa wani crazy wando daya babbarke gawata shegen sarkan Cross awuyan shi yayi askin nan dakalin shaidan yana dan tauna cingum yana murmushi, hannu yamikama Mummy yace "watsupp Mummy, afternoon" gyadamai kai Mummy tayi ta rungume hannunta akirji kaman mai shirin salla tace "sannu Chris birthday boy, see my daughter, you guys should have maddd fun okay, but bring her back before 6" wani irin dariya Chris yayi harda dan juyawa ya kalli Rahima daketa kallonshi yace "your Mummy is a sabi woman, alright Mum we will have fun Chris promise you that" kashemai ido Mummy tayi batare da Rahima ta luraba dan kallon Chriss take, murmushi yayi ya kalli Rahima yace "let's go beautiful muje nabude miki ki shiga" gaba ta shiga yana biyeda ita hakan yabashi daman juyowa shima ya kashema Mummy ido tareda lashe lips dinshi, saida yasata ciki sanan ya zagayo yana dagama Mummy hannu ya shiga ciki ya kunna motar yaja duk sunama Mummy bye, ajiyan zuciya Mummy ta sauke sanan tajuya takoma cikin gida da Siddiqa taci karo awurin Gate idanunta sunyi jaaa sosai tsabagen fushi, babu ko alamun tsoro tace "wlh Mummy saina fadama Abba duk abinda kikeyi, keke bata Rahima bakowa ba, yanzu Mummy ba abin Rahima takawo miki katon arne, arnen ma wanan dan iska ne amatsayin saurayi ki fatattake shiba shine zaki barsu yafita kinsan inda zai kaita? Mummy mufa matane, Rahima mace ce, very fragile ma kuwa, batada hankali wat if yamata wani abu? Wat if yay raping nata? Me zaki cema Abba eh? Mummy! " takirata da karfi looking so pain, wani banzan kallo Mummy tamata tace "ki rubuta ki ijiye duk randa zaki gayama baban ku wlh wlh aranan kika fita daga sahun y'ay'ana na cikina saidai kije kinemo wata uwar" tai tsaki tawuce tabar wajen.
Chapter 17 · 0% Book details