← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 102

Sashe 20

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Tashi yayi yawuce bedroom dinshi ranshi abace wasu kananun kaya ya dauko, Black jean yasaka sai wata Ash color riga short sleeve mai gajeren hannu yasaka, rigan nada V neck daya bayyanar da kwantaccen gashin kirjinshi, rigan ta kamashi sosai, kaman rigan zata barke ajikinshi sabida yanda ta bayyanar da kiranshi na full packs man, Black jacket yadauka yadaura kan rigan yasaka wani boot baki yadau car key dinshi, kana ganinshi kaga soja yafito daga flat dinshi yaso ya shiga wajen Ummi but no Inya dawo yaje, he don't want to waste anytime, motarshi ya shige yaja tareda danna horn mai gadi ya budemai gate yabar gidan.

Tashi Ummi tayi daga jikin window bayan taga taga fitanshi jikinta ya mugun yin sanyi takoma kan gado ta zauna ta buga uban tagumi cikeda damuwa ta daga hannayenta sama tace "wanan wani irin jarabawa ne Ya Allah meke damun Sameer ne dako kadan mace bata gabanshi?" tai dan shiru tasa hannu tai maza ta goge hawayen dake shirin zubomata, tasowa Nuru yayi yazo kusada ita yabata side hug cikeda damuwa yace "Ummi kidena damuwa okay, kidinga mai addu'a in sha Allahu har jikokin shi zaki gani nan bada jimawa ba kuwan" fuskar Nuru ta kalla tace "anya? Kaduba pa am sure sabida maganin dana gayamishi Baffa shi yakawomai ne yau da safe yasa yaki shigowa dan baisoma yasha, Noor ya zanyi da raina eh? Yayanku fa Noor duk ya girmeku nesa ba kusa ba, yabaka almost 8yrs but look at you now da Nabila batai having miscarriage ba da kanada yara biyu aduniya, I tot yanda na kawo maganan Asiya he will accept da gudu sabida cousin dinshi ce kuma naga suna shiri yarinyar na sonshi sosai, bazai wani sha wuyan neman aure ba dan da gudu Baffa zai bashi ita amma kalli abinda yama" ahankali Nuru yace "Ummi kibar maganan Asiyan nan, it won't work, ai dama tun kafin kiturani na gayamiki kice Yaya Sameer ya auri Asiya ai kaman kin kara koranshi daga zancen auren ne, Yaya Sameer dason girma tsiya inya auri Asiya ai kaman ya yankin ma kanshi ticket din raini ne, ni nasan dama bazai taba koda da wasa he will not accept maganan nan, kawai kiyitamai addu'a Ummi what goes around comes around, Yaya Sameer zaiyi aure one day one day" cikeda damuwa sosai Ummi tace "Ya Allah, Ya Allah kadubi lamarin nan nawa, Ya Allah ka karkata zuciyan Sameer zuwaga wata mace, Ya Allah kahadashi da wacce zaiso sosai, Allah ka aurarmin da yaron nan badanni ba badan halina ba" tasake share hawaye daya zubo mata rungumeta Nuru yayi yace "is okay Ummi ya isa hakanan" haka yacigaba da lallashinta har Muhammad shima yadawo duk suka taru suna bama maman nasu baki harsuka samu ta dawo normal tadan wartsake tabiye musu sunata hira.
Chapter 20 · 0% Book details