← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 102

Sashe 66

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

Bude kofan tayi jin bai budeba yasa ta murza key kofan yabudo ahankali tace "good morning" batare da Dr ya shigoba tace "morning patient, ina Soja? Inata kiranshi in cemai am coming very early bai daukaba" kallon dakin tayi tace "ga wayan chan bayanan" gyadamata kai Dr yayi yace "akwai any ciwon dakikeji?" girgixa mai kai tayi tace "shikenan, Allah kara sauki ki cigaba da shan maganin ki kifadamai nazo zai kirani inya dawo" gyadamai kai tayi ta maida kofan ta rufe ta dawo ciki tana sake bin wayan nashi da kallo sanan takoma kan gado ta zauna bude kofan bayi taji anyi da sauri ta dago kanta Sameer ne yafito sanye da kaya ajikinshi da karamin towel a hannunshi yana share gashin kanshi cikeda mamaki tabishi da kallo dama yana nan, agaban wardrobe ya tsaya sanan ya juyo ya kalleta da sauri ta sauke kanta kasa gabanta na faduwa tace "ina kwana" batare daya amsa taba yace "go and shower kiyi alwala kizo ki salla" tashi tayi ahankali tabude bayin dataji yana kamshi Sameer din ta shiga koda tafito bata ganshi adakin ba babu kuma wayanshi sai Dadduma daya shimfida mata shiryawa tayi cikin wani black doguwan riga tai salla tana zaune room services sukazo suka gyara dakin tsaf suka mata yajiki sanan suka kawo mata breakfast kaman yanda Sameer yabasu izini dan fita yayi.

Around 4 Sameer yadawo Hotel din rike da dan wani box a hannunshi kaman na working tools, knocking yayi sanan yabude dakin nasu ya shiga tana zaune kan gado tana murmushi ita kadai da TV, carton take kallo ta sanya daga daga cikin dogayen rigunan daya sai mata daya mata bala'in kyau kanta babu dan kwali, daidai da ciwon kai bataji taji sauki sosai jin anbude kofa yasa ta dago kai da sauri ta sauke kan tuna abinda taitayi jiya ahankali tace "ina yini" bai amsata ba sai wani mahaukacin daure fuska dayayi yadawo sojanshi tsaf ya maida kofan yarufe tareda murda key yazaro key yajefa a aljihu ya shigo dakin ko takalmi bai cireba, karasawa gaban gadon yayi yasa hannu yadau remote din TV data ijiye a wajen ya kashe TV, ahankali tadago kanta ta kallai dan faduwa gabanta yayi ganin yanda fuskan shi yayi yau babu ko dingo rahama, gaban bayi yaje ya kulle yacire key yasa a aljihu tasake binshi da kallo sanan kujeran dakin ya jawo yay kwana dashi kujeran ya fuskanci gadon datake kai, da yatsa yanuna mata kan kujeran yace "sit here" wani irin faduwa gabanta yayi ahankali ta tashi ta zauna awurin da yanuna mata tsakiyan kujeran tana kallonshi kaman tasami tv, aljihu box din yayi kan gado sanan yabude kadan yajawo wani seletep yamayar ya rufe sanan ya juyo kanta da jajayen idanunshi ya kalleta da sauri ta tashi jikinta narawa tace "Yaya Sameer wlh nai salla fa, me zakamin eh?" cikin wani black voice yace "sit" komawa tayi ta zauna sanan ya tsaya akanta ya warware seletep din yazo ya manne bakinta bam dan baiso tamai ihu kafin yakoma kan gadon yabude box din da kyau, set din wasu miyagun wukake ne da bamata taba ganin irinsu ba sharpness din bakinsu datagani yasa tagane wukake, wata gajera yadauko yajuyo ya kalli Rahiman kafin ya zauna abakin gadon har gwuiwan su nataban juna yadau wani paper Hotel ya kyasta wukan ta yanka paper sanan yakawo wukan saitin fuskanta yunkurin magana ta shigayi ta mike tsaye yamata wani mugun kallo yace "sit" zama tayi yace "kinsan sunana ko Lieutenant Sameer Simran Sameer, wayan nan wukaken dakika gani legal knives dina ne duk wanda na yanke dasu ko na kashe kaman na kashe banza ne, zan iya kashe ki anan babu wanda yasani babu wanda kuma zai taba sani, bana wasa da yara Indomie generation irinku, u always say bakison kimutu yanzu, inhar you want to live to dole ki natsu and say the truth, dan rayuwanki yau depend on gaskiyan da kika fadi ko karya and try me and see" yay maganan babu wasa yana kallon idanunta datake zarowa tsabagen tsoro kaman zasu fadi akasa hawaye nabin idanunta, yace "one more thing, ko tari kikamin anan not just ihu I will shock you Rahima, zan baki mamaki" yay maganan tareda tashi ya cisge seletep din bakinta ta runtse ido sabida azaba batare datai koda tari ba tana sauke ajiyan zuciya, sanan ya zauna yace "clean those tears" da sauri tasa hannu ta sharesu kirjinta dukan a shirin a shirin kawai suke tsabagen tsoro ita dama harga Allah batawani yadda da abokin Abban nan wanan sojan ba tasan mugune, gyara zama yayi yace "are you ready?" gyadamai kai tayi tana hadiye hawayen dake shirin zuba, yana kallonta right into the eyes irin kallon I dare you to say lies dinan yace "ranan da mukazo gidanku da magrib nida Abban ki, baki fitaba, after basketball Mummyku tace min duk bacci kukayi kece kadai suka bari adaki baki riga kin tashi ba, ya akayi a ina kika samo 3 bottles of codeine da weed dat u were smoking ranan?" wani irin racing heart dinta ya shiga yi zata fashe da kuka yace "this is the last time dazan fada miki karkimin kuka, cry kika idan ban fasa miki tear bags dake cikin idanunki ba" hadiye kukan tayi tai gum tana kallonshi kaman zata cinyeshi da ido yace "answer me!" gyadamai kai tayi da sauri tace "a....kagako..." takasa magana tsabagen yanda kirjinta ke bugawa bakinta kerawa sosai ya tsareta da wasu irin mayun idanu yace "am listening" tace "wlh ina tashi daga bacci na shiga bathroom nai brush na wanko fuska na nafito shi....ne" tai shiru yanda yamata wani kallo yasa tace "shine na gansu akan bedside drawer dina su uku da weed guda uku, wlh baruwana bani na ijiye ba na rantse da Allah" tai maganan bakinta na rawa tana shirin kuka amma yanda ya tsareta da ido da wukake yasa ta hadiye kukan, sosai yake kallonta yasha interrogating criminals so yanada knowledge inhar yama tambaya ka saki karya zai sani kana fadin gaskiya zai sani kuma yasan tambayan nan iyakan gaskiyan datasani tafadi mai hakan yasa yay shiru, puzzle questions zai mata dashi ne zai bama kanshi da kanshi final amsa din, yace "how did you escape from rehab?" rawa bakinta yafara da kyar ta danne kukan tace "ranan I was bathing in the morning all of us muna bayi shine one woman tafado bayin nakusan ihu shine tarufe min baki......" nan tabashi labarin har inda suka kwana da abinda suka bata duka tai maza ta share hawayen daya zubomata gyadakai yayi cikeda gamsuwa yace "who was that Chris your boyfriend me hadinki dashi?" fashewa tayi da kuka kallon daya mata yasa ta hadiye kukan da sauri tace "wlh wlh ba boyfriend dina bane, ajimu daya a vet, kagako ni banda ko kawa daya a school dinmu, I don't talk to anybody a class dinmu shine kullum kullum yayta kallona yanamin magana wlh bantaba cemai komiba, ranan damuka zo school zamu fara sauke ya Siddiqa a accounting department su Yaya Siddiqa da Luba da Zeena sunata xagina, shine direba wai sudena biyemin ni yarinya ce, shine fa naji haushi nace yakara cemin yarinya saina marai shine Yaya Siddiqa ta daddakeni ta fizgoni ta yardani akasan wajen" tafashe da kuka, mugun kallon daya mata yasa tahadiye kuka tace "Ya Siddiqa tacema direba yatafi yakaisu Ya Luba tunda rashin kunya nakemai nai trekking to department dina kumafa duk yafi nasu nisa chan karshen school dibfa muke, shine tai tafiyanta tabarni natashi ina kakkabe jikina saiga Chris ya tayani daukan jakana yace nazo muje da kyar na shiga damuka je har an shiga lecture shine saiyaga Codeine ajakana saiyace......." tabashi labarin tsaf harda yanda Mummy saida tamaga Chriss din tace su tafi, Sameer baice komiba harta gama yana sauraronta yace "Rehab Dr ki ya sanar dani you have been taking drugs 8yrs ago, jikin ki yabasu dat record" ya kalleta kaman yanda take kallonshi yace "your Dad told me baki dade da shiga 20yrs ba, bari namiki simple mass, subtract 8 daga 20" da sauri tace "12" gyadakai yayi yace "you've been into drugs tun at the age of 12, yaran 12yrs bama susan me drugs ba, basusan akwai wani abu shaye shaye aduniya ba, children of 12yrs ko balaga basuyi ba basu mallaki hankalin suba, bama Susan menene duniyan nan ta kunsa ba, listen Girl" ya gyara zama yace "idan kika kawomin any gargada akan wanan tambayan zan baki mamaki, I need answer tell me ya akayi kika fara shaye shaye at the age of 12, ranan farko and everything" faduwa gabanta yakeyi bana wasaba Mummy tasha fadamata kar wanda yaji tsakanin su, koma menene karta sake ta kira sunanta mutane da society sun dauka shaye shaye is bad but is actually fun, da dadi su basu sani bane. "Rahima!" Sameer yadaka mata tsawa tareda kai wukan kasan wuyanta yasa tafara wani nishi kaman mai shirin mutuwa duka jikinta moving yake yawani zaro red eyes dinshi yace "tell me how did you start doing drugs, who the hell introduced you to drugs at 12yrs old, who! Yasaka mata wani mahaukacin tsawan da batasan lokacin datace "Mummy! Mummy na! Mummy nane!!" kallon kwayan idanunta Sameer yayi kafin yadan koma baya saikuma ya zauna yana kallonta bai bari yanuna mata anything ba, hawaye ta share da sauri saikuma tafashe da kuka tace "Ya Sameer dan Allah karka fadama Mummy, wlh tace duk randa nafadama wani daga ranan zata dena sona tunda ni ban rike sirrin ta amana ba please kaji, dan Allah wlh zan fadamaka amma karka fada kaji" wani mugun kallo yamata shiru tayi tace "kaga ko Ya Sameer duk duniyan nan wlh babu mai sona kaman Mummy tana sona dama dasu Ya Siddiqa data haifa, kaga su Ya Siddiqa kullum suyi ta dukana da ina kwana a dakinsu Mummy tacireni daga dakin tasa home decor tazo aka tsantsaramin dakina yafi nasu kyau, kuma kullum da daddare a dakinta nake kwana dan bana iya kwana ni kadai, kaga bayan Mama na ta karyani tabar gida nadinga ciwo zafi ko ina yakemin anata karyani ana mayarwa mummy in anamin dauri harsai Abba yakoreta dan kukanta harya kanfi nawa sabida yanda take tausayina mu dawo gida inta kuka bana iya bacci wata rana tazo da Abba yafita sallan magrib su Siddiqa basa daki ta zauna tareda rugumeni tana tofama hannun karyan addu'a tacemin zata bani wani abu dazaisa nadaina jin zafin hannun amma karan fadama kowa inaso na gyadamata kai tace kuma abin zai dinga sani farin ciki na manta da mamana muguwa my mum is wicked but she is here now, she is my Mum she loves me more than her banga bata taba dukana ba kuma bata tababa so ma manta da ita zatamin komi, tasa na kulle idona nabude baki ta naji dai wasu kwayoyi guda uku tasamin sanan ta zubamin wani ruwa mai daci nasha, ta kwantar dani ajikinta tanamin tatsubiya nai lamo ina jinta ahaka nai bacci sai washe gari natashi aiko hannuna babuma inda kemin ciwo I was so happy nadinga murna ina tsalle ina rawa itama ta tayani, dazaran naji zai fara zafi zanje dakinta nace tabani abun tacemin nabari da magrib kullum da magrib take Bani lokacin kuma saina rufe ido nadena rigima harnazo na girma, tacemin nai browsing uses of weed nayi, kagako Ya Sameer Mummy duk wani abu dazai amfaneni takemin bamatama yayanta, naga weed na bude brain hakama shisha dan akwai nikotin aciki tundaga ranan tace kullum zata dinga samin a abinci saisa in babu shi a abinci ban iyaci danna saba kuma ko nafi duka su Ya Siddiqa brain because of weed 9As nafito dashi a Waec jamb kuma naci 362, Mummy ko tsinke bata bari na daga anything dazaiban wahala bata bari nayi bana aiki nan shara ban wanki ban girki kuma insu Ya Siddiqa sunkai karana ta dakesu, su kadai keyin aikin suyi abinci su kawomin har kan gado, ran Saturday da Sunday kawai take sani nabisu islamiyya shima sai in Abba na nan sabida karya mata fada amma inhar bayana van zuwa sabida duka akeyi, su Ya Siddiqa kadai ke zuwa, in kanwar Mummy taje dubai ni kadai zatasa ama tsarba kaya dan nine autan ta, kaga yawan kayana yacika wardrobe dina some kayana ma a wardrobe dinta suke, takaini saloon kullum dani take fita, in Abba yadaken taita fushi, insu Ya Siddiqa suka daken takamatsu tace inzo in rama kaga bata bari aci zaluna, batason ta ganni cikin bakin ciki duk wani abu dazai cireni a damuwa zata bani, Mummy na bala'in sona tacemin that my wicked Mother ta taba sata tai bari bayan ta haifi Luba wai mamana tasata tai barin cikinta na boy amma bata riketa da hakaba yasa taci zaluna ba kota lalatamun rayuwa ba saidai ma tasoni sama da yanda taso nata yaran, kuma bata taba bari Abba kosu Siddiqa sun gane ba da daddare take bani nasha nai bacci, kuma Abba shi yawanci a studyroom yake kwana yana aiki sai tsakar dare yake dawowa kuma wani zubin a sati baufi yay 3daya a gida ba sauran yay tafiya saisa duk basu saniba sai ranan shima nasan Mummy ta ijiyemin ne kawai dantaga bana cikin farin ciki to tazaci da daddare zansha shine nikuma na dauka nasha alokacin nai mistake" tai shiru tana kallonshi kaman yanda yake kallonta, jikinshi yay mugun sanyi jikinshi yay sanyi, all he sees a idanun Rahima is yarinta da mugun rashin wayau, akwai yaran 20 da hankalin su is intact but Rahima kam Mummy tai brainwashing yarinya da bama tasan different between right and wrong ba, tadawo da brain din Rahima a fool, ajiyan zuciya ya sauke ahankali yan abubuwan dayagani couple of times dayaje gidansu nadawo mai, maida wukan yayi cikin box din yarufe box din yana kallon Rahima dake kallonshi har lokacin gabanta na faduwa tace "ai ba zaka fadaba ko" gyadamata kai yayi yadau box din yatashi yafita daga dakin binshi tai da kallo saikuma tafashe da kuka takoma kan gado ta kwanta duk zuciyanta yaki natsuwa.
Chapter 66 · 0% Book details