← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 102

Sashe 72

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana zaune a office dinshi har yamma baimasan a ina zai kwana yauba dan yan interior company nan nagidanshi a auna nan a auna chan anata kawo kaya, he is so worried akan Ummi dake fushi dashi, knocking kofarshi akayi hakan yasa ya kalli kofan tareda rufe system dinshi yace "common in" bude kofan akayi Noor ne da Muhammad suka shigo duk sunamai murmushi saikuma yaga matayen su rikeda yaransu a hannu sunci gayu hakan yasa yatashi kafin yaga Mu'az ya shigo rikeda wani cake da aka rubuta happy birthday ajiki da happy married life ga uban balloons, dan zaro ido yayi like wats all this, maida kofan Nabila tayi tarufe Mu'az yakaraso ya ijiye fine cake din kan table dinshi tareda kunna fireworks din hakan yasa dukansu sukahau mai waka. "happy birthday to you, happy birthday to you, Happy birthday to Yayan mu, happy birthday to youuuu, hip hip hurray" sukahau tafi, murmushi yayi yazagayo hannu yasa yakarbi Princess daketamai dariya Nabila tace "ina yini Ya Sameer" ahankali yace "lpy lau" sanan ya kalli jaririyan Fadila ya shafa kumatun ta yace "babygirl you came to my office today" duk dariya akayi Fadila tace "happy birthday yayan mu, ina yini" ahankali yace "Alhamdulillah" sanan yanuna musu dogon kujeran office din yace "ku zauna" sanan ya kalli Noor da Muhammad dake tsaye yace "ku zauna" zama sukayi kan kujeran dake gaban table yanunama Mu'az stool yazauna shima kafin ya koma kan kujera ya zauna rikeda princess yay murmushi tareda kallon cake din yace "I've forgotten yau birthday dina ma" yasake murmushi sanan ya kalli Noor yace "thank you guys" akadanyi shiru, ahankali Noor yace "Yaya Sameer, I came here we all came here not just for this" ya nuna cake, yace "Ya Sameer tun ina dan karami I watch how you live your life akan gaskiya dayin abubuwan gaskiya, one thing dana sani kanka haryau har gobe shine you don't just do things anyhow kome kayi I know akwai reason behind it, Ya Sameer ko prostitute today kace zaka aura I will support you dan nasan kasan me kakeyi, I trust my brother and I stand with you in every step you take, worry not okay, Ummi zata sauko itama I assure you this" ajiyan zuciya yasauke yana kallon cake din kafin ahankali yace "there's more to wat am doing ku kannai nane dole ma sanar daku, banso iyaye susan maganan dan ba hurumin mu bane mutona mata asiriba is left for Abban su should find out dakanshi" labarin Rahima yashiga basu tatas, duk dakin dama Fadila da Mu'az sune masu saurin kuka saida sukayi, Sameer yace "I just see Rahima kaman kanwar mu su Asiya and Yusra, I look at the whole case like look at Princess, ga babygirl all of them are children nobody knows tommorow, lemme save this girl dan nima inada kannai da y'ay'a mata, and if by saving her from that wicked is by marrying her am ready to do it, shikenan" tasowa Mu'az yayi da sauri yafada jikin Sameer yahau kuka, ahankali Sameer yay patting bayanshi yace "kaga nahanaka kuka u see princess namaka dariya" dagokai yayi ahankali ya kalli yayan nashi yace "Ya Sameer I want to be like you when I grow up, u truly have a heart of gold" kanshi Sameer ya shafa yace "stand up jeka zauna awurinka" tashi yayi yakoma yazauna, Muhammad ne yace "to yaushe zakaje ka daukota daga rehab? Inyazo ta dinga zuwa as an outpatient saisu dinga bata appointment" ajiyan zuciya Sameer yasauke yace "Ummi tace nadaukota but yau ana zuba funitures, am planning gobe zan daukota" gyadakai Muhammad yayi da sauri Nabila tace "Ya Sameer ni banma gantaba but Allah yadauramin sonta already and I promise you zamu riketa as a sister kuma amana batare any stigmatisation or abu makamantan hakaba ko Fadila" gyadamata kai Fadila tayi tana share hawaye, Nabila tace "but inaso ka daukota da safe, ka kawota gidana ko Fadila, we call mai lalle da saloon agayara mata kai, da daddare saimu kaita dakinta, we have to make it special I think we should throw a party ko baby" ta tambayi Noor, kafin yabata amsa Sameer yadan yatsine fuska yace "No banson party, banson anything noise" tasowa Fadila tayi tazo wajen Yaya Sameer din tace "bamu kudi, we need to get kayan dazata sa ready gobe" Nabila najin haka ta taso itama tazo tace "yauwa kin tunamin yarinya ranan bikin ta bazata saka tsofaffin kayaba, Ya Sameer akwatinta fa" dariya Noor yayi yace "yauwa ku damai dan yayanmu zai iya ya share komi babu ruwanshi" yanda sukamai chaa aka yasa yadau wallet dinshi yabude yaciro Atm card yamika musu yace "gashi, pin 5474" ihu duk akayi cikeda murna Noor yace "ehen let's cut cake and feed yayan mu is his birthday" yanda sukamai hayaniya a office yasa yace "wai ya akayi aka barku kuka shigo Barrack dinan?" da sauri Mu'az yace "cha musu mukayi we are lieutenant Sameer Simran Sameer family and today is your birthday we are giving you a small surprise" girgixa kai yayi suka shigo gutsuro cake suna bashi har yasamu da magrib ya tarkatasu suka tafi.

Washe gari!
Daren jiya bakaramin fada Mummy da Abba sukayi ba, tun yana ganin abin nata shirme harsaida yace mata waito me danna auramata Sameer me eh, shima yamata kacha kacha ganin ya shareta hakan kuma zaifi jawo mata olla dan tanason jin information daga gareshi yasa tasameshi safiyar yau tabashi hakuri sanan ta tambayeshi ya ake ciki yanzu, yace mata kampanin interior sungama saka mata kaya duk wani kayan bukata data sani tundaga kan kitchen dining labulalye da sauran su sun saka, dama quotation din dasuka min nakomi was 11.9m, nabasu 8m, to inaso anjima zan basu sauran kudin, Sameer yacemin zaije Rehab Centre yadauko ta da daddare zanje gidan nafadi mata dakaina na aurar da ita" da sauri Mummy tace "zamuje tare nai kewan yarinya na" dan shiru yayi kafin yace "no tafiyan namiji daban naku na mata daban, idan uba yatashi zaije gidan yarshi shi kadai yake zuwa" shiru Mummy tayi kafin ta gyadamai kai tace "shikenan gobe ni naje naduba gida idan da gyare gyare nayi" kudi Abba yaciro dayawa yabama Mummy gashi kimata siyayya sanan yafito tareda kwallama Siddiqa kira tafito yace "yauwa kije dakin Rahima ki tattara yan kayanta zan kawo miki babban trolley na, da school books dinta kihada komi kikai motana, make sure u pack anything dakikasan tanaso fa" da sauri Siddiqa tace "to Abba" ta shiga dakin shikuma Abba yashiga dakinshi yafito dawani babban jakan Lv yashiga dakin yabama Siddiqa tahau aiki, ganin batasauri yasa yashiga tayani gwanin ban sha'awa Abba is just so happy, jiya harda sallan dare dan gani yake Allah gata yamai daya bama yarshi dake shaye shaye kamilin namiji irin Sameer.
***

Wuraren 11 na safe yay parking motarshi agaban rehab din batare da security sun bari yay parking acikiba ya leko yace "Sir sorry, we are celebrating 20yrs anniversary yau saisa kowa anan yake parking you can come in sir" kashe motar yayi yafito Mu'az dake taredashi shima yafito yana sanye da kananun kaya, shikuma Sameer na sanye da uniform yay wani irin asirtaccen kyau ko mesa oho, sai kamshi yakeyi, rufe motar yayi suka shiga ciki shida Mu'az dake biyada shi, compound din yagani an gyara anyi decorating da balloons black and golden, ga tables da chairs da aka zuba awajen all patient dinsu maza da mata zazzaune suna shan drinks wasu nacin abinci wasu kuma nacin snacks gawani soft music natashi, all the patients looks very happy sai hira ake, dan the only thing dake joining maza da matansu is sport randa za'ai sport other than that kuma babu saiyau da aka fitoda kowa sabida 20yrs anniversary da Hope Rehabilitation centre ke celebrating, ahankali yake tafiya yana kallon koina kaman eyes dinshi is searching for someone, chak ya tsayar da tafiyan dayakeyi hango Rahima dayayi dake zaune itada wani fair guy da naman idanunshi kenan so black tsabagen shaye shaye, tana sanye da uniform dinta na rehab saidai kanta babu kodan hulan nan data saba sawa kuma anbata taki sawane sabida an mata tsifa an wanke mata kan dama ance mata yau za'a kawo mai kitso tamata, an mata parking gashin aka bata wani pink ribbon takama gashin dashi tasaki jelan gashin dayakai har tsakiyan bayanta bakin dukya kanannade abinku da coily hair, bakaramin kyau tayiba sabida gashin mutane dayawa maza da mata anata mata magana sabida yanda tai kyau tai kaman wata little angel irin yaran yan gayun nan, tai mugun kyau, damasu biyune kadai a table dinsu tana rikeda cocktails a cup da straw keciki tana zuka shikuma yagama cin rice yana goge baki yana kallonta dan yarinyar ta masifan burgeshi kaman yasace ta yakeji yasakin mata murmushi yace "finally yau munsami normal food munci, amma kullum aita bama mutum abincin magani ewwww" yatabe baki, kyalkyacewa da dariya tayi ya mugun bata dariya dudda batasan guy dinba ita kadai ke zaune yazo yasame ta yazauna ya ijiye abincin shi yana shi yahau mata surutu.

Wani irin abu Sameer yaji yadaki kirjinshi ganin yanda take hirada wani daketa kallonta kaman zai hadiye ta kanta ba hula iska na kada gashinta, ahankali yashiga dunkule hannu kirjinshi namai wani irin zafi.

58.

Agurguje
Chapter 72 · 0% Book details