← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 102

Sashe 43

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Dr sukabi har zuwa wani daki datake cikin ward din, dakin gadaje guda biyar ne ciki anbata wani gado dake kusada windo, tsayawa yayi akanta yana kallon karin ruwan da ake mata tana sharban bacci Dr dake kusada shi yace "tai bacci sabida amayar da komi na cikinta damukasa tayi dazu, as for visit dinta tunda kaika kawota signature dinka mukedashi you can come anytime kaduba ta, banda kai kuwan babu wanda zai iya zuwa dubata unless ita tai requesting wani nata yazo, saikuma idan tana 5th phase na treatment dinta zamu gayyaci yan uwanta suzo su ganta, karka damu in sha Allah sister ka ta kusan dena shaye shaye har abada" hannu Sameer ya mikamai yace "thank you so much Dr, zan wuce dare yayi" gyadamai kai Dr yayi yace "yeah, gud night Lieutenant" gyadamai kai yayi yajuya batare daya kalli patients din wajen ba yawuce yafita, marfin motarshi yabude zai shiga wata nurse daya daga cikin wayanda suka gungurata zuwa ciki tafito da sauri tace "Sir wait please" harya bude kofan motan ya tsaya juyowa yayi da sauri ya kalleta, karasowa wajen tayi tana murmushi tace "Sir actually naga baka kawo sister ka da komi ba, and normally I am the one incharge of kayan su da abubuwan amfani su" anatse yace "I tot kuna basu uniform me kuma take bukata?" yay maganan da zuciya daya dan baisan me kuma suke bukata ba, murmushi nurse din tayi tace "actually yes bama bukatan kaya dan uniform suke sawa, but yakamata adan taho da jaka dake dauke dasu pants, bra, singlet, pad kasan mace ce she needs all of this" dan lumshe ido yayi dudda maganan yazo mishi bazata amma saiya danne yace "ohh kuna sayarwa ne anan?" wanan karan kyalkyacewa da dariya nurse din tayi ta girgixa kai tace "a'a bamu sayarwa, but in kafita across the street akwai wani super market that sell all ladies wear hakanan, sai ka karo mata hardasu toothbrush da cream dinta da toothpaste, sabulon wanka, sponge da kuma hijab sabida salla, but most importantly karka manta da pant and bra sai pad this 3 things she can't get them here" dan gyadamata kai Sameer yayi batare daya kalleta ba ya shiga mota yatada yaja aka budemai Gate yafita daga gidan yafita daga Street din har zuwa shagon datamai kwatance, parking yayi agaban shagon ya shigo yana kalle kalle, breziyoyi ne da panties kala kala ashagon, tsayawa ma yayi chak batare dayasan wani abu zai daukar mata ba this is the first time in his life dayake sayan pant bra da pad toshi baida kanwa ko Yaya bama ataba aikanshi irin abun nan ba, ganin yanda ya tsaya chak yasa madam din shagon wacce take bayerabiya ta taso tazo inda yake tace "what can we get for you young man?" ajiyan zuciya ya sauke yace "aahhhmmm" yama kasa magana dan for real sunan kunya yakeji inzai fada, ko gane hakan matan tayi tace "we have different breziya for your wife, sisters, cousins and girlfriend, we also have panties, normal pant, g-string, lace and shorts, we have disposable pants you know, ladies use it during their monthly period is easy" da sauri yace "give me normal pant and bra, and the last one you mentioned, disposable pant" da sauri matan tace "okay okay, what size kakeso?" dan kallonta yayi to shi wani size zaice mata yay shiru ganin haka yasa matan tace "okay I get baka san size dinba, what's the age of the lady?" ahankali yace "20" da sauri tace "okay oka, is she bobby? Ko batada girman nono sosai hakan nan?" dan kauda kai yayi yama rasa mezaice mata da kyar ya tattaro yan kalaman bakinshi yace "ammm Big, I.....g...guess" da sauri matan dake kallonshi tace "okay manyan nono kenan takedashi?" gyadamata kai kawai yayi batare daya kalleta ba, section din breziyoyi tawuce tana surutu tace "nagane irin yaran nanne dasuka taso sunada girman nono" tai maganan tana ciro wasu fine manyan breziya masu bala'in kyau lace dinsu hadaddu ta dagomai su tace "kaman wanan zasu mata ko dan kace she is 20, wanan ne daidai size din irin yara yan 20 dinan masu manyan nono" da sauri yadauke kai batare daya sake bama bra din second look ba tareda gyadamata kai, hakan yasa tace "gudanawa zansa?" rasa mezaice yayi yace "just put plenty" dariya matan tahau yi dan tasan wanan bakon siyan breziya ne hakan yasa tasaka dozen guda 12, pant kuma due to age datai amfani dashi tasamata yan daidai 2 dozen guda 24 kenan, tasaka different design na singlet 7, sai disposable pant tasaka 30, tasa mata short guda hudu, saida tagama hadawa tace "Sir i have pad o in kanaso oyinbo pad, daga kasan waje aka kawosu no matter yanda sister ka keda heavy flow this pad zai jure, is very fine, and cotton ne to make mai amfani dashi more comfortable" batare daya kalleta ba yace "add it also" saka kwali bakwai tayi sanan ta kawomai, ya kalleta yace "do you have cream, shower gel da toothpaste da sauran su?" da sauri ta gyadamai kai takoma tahado duka sanan ta kawo tamai bill almost 55k dan pant da bra masu tsada ne tasaka mai komi aleda ya karba tareda biyan kudin yafito yana kalle kalle ko akwai shagon dazai samu yasai jaka, ganin babu wani shago yasa yabude boot din motarshi wata babban bagpack na sojoji ya ciro ya ijiye ledan kayan agefe, zage zip din jakan yayi ya zazzage abubuwan ciki wanda suke yan tarkace ne sanan yadau ledan kayan yatura ciki ta shiga sanan yazage yadau jakan ya rataya a kafada ya rufe boot din sanan yadawo motar ya ijiye jakan adayan kujeran yatada motan yakoma wajen yana shiga a reception yaci karo da nurse din bata jakan yayi yace abata tamai godiya sanan yajuya yafito ya shiga mota yabar wurin saida yahau kan titi sanan ya kalli agogo karfe shadaya da kusan minti shabiyar, wayarshi yaciro yay dialing number Abba dan bazai iya komawa gidan ba dare yariga yayi saidai da safe ringing biyu aka dauka muryan Mummy yaji tace "Lieut ka kaita kana dawowa ne?" batare daya bata amsaba anatse yace "ya jikin Abba Dr yazo yaduba shi?" cikin sheshekan kuka Mummy tace "yazo anamai karin ruwane bacci yake har yanzu" gyadakai yayi yace "alright will come in the morning kafin nawuce office, gud night Allah kara sauki" da sauri Mummy tace "Lieut" amma harya katse wayan, wuraren 12 ya iso gidansu aka budemai Gate ya shiga, fitowa yayi daga motan yana kallon flat din Ammi dayaga haske alamun bata riga tai bacci ba kenan that's strange dan yawanci tara Ummi ta kwanta, karasawa yayi har flat din Ummi yabude kofa ahankali ya shiga da sauri Asiya dake zaune kan kujera tana sanye dawani dogon rigan bacci ja daya wuce mata guwiwa tana kallon wani Indian film rikeda remote a hannunta tajuyo, ganin Sameer ne ya shigo yasa ta tashi da gudu tazo inda dake daga bakin kofan batai wata wataba tafada jikinshi cikeda murna tace "oyoyo Yayan mu, Yayan mu sai yanzu kadawo" tai maganan tana fita daga jikinshi tana kama hannunshi tarike gam kaman batason akwace matashi tana kallon fuskarshi, gyada mata kai yayi yace "yes am just coming back" yana shiga cikin falon yana magana, zama yayi kan kujera ta zauna kusadashi har lokacin tana rikeda hannunshi, juyowa yayi ya kalleta yace "ina Ummi?" ahankali tace "tana dakinta tayi bacci tuntuni" dan murmushi yamata ganin yanda take bala'in murna ganinshi yace "what about you mesa bakiyi baccin ba? Kina kallo ko?" da sauri ta girgiza mai kai tace "a'a wlh yayan mu, kainake ta jira kadawo, sabida karnai bacci ne yasa na kunna kallo inayi" dan gyadamata kai yayi yace "get me something to eat am hungry, no fara kawomin ruwa cus am thirsty" da sauri ta takeshi ta tashi taje fridge bottle water tadauko tai kitchen tadauko tray ta cup sanan tafito falon tadau bottle water ta daura akan tray din tadawo falon ta ajiye mai kusada shi kan kujera sanan takoma kitchen tadauko plate da spoon dawani tray tazo dinning dama abincin shine kawai a warmers din wajen, biryani rice akayi sai cowhead pepper soup da zafinsu sabida warmers din dasuke ciki tasamai spoon akai sanan tamaida warmers din tarufe duka tadauko tray din tazo falon tajawo center table zuwa gabanshi tadauramai tray din akai tace "gashinan yayan mu" hannu yamika yadau plate din abincin from tray ahankali yace "thanks little sis", tray din bottle water dayadan sha tacire tadaura kan center table din sanan tazauna kusada shi tana kallon film dinta bini bini tadago kai ta kallai saitai murmushi tacigaba da kallonta wani irin dadi da mugun burgeta yake in yanacin abinci, komi nashi anatse, ayangance kuma duk dadin abinci anatse yakeci, ahaka harya gamacin abincin kallonshi take, yaci sosai kadan kawai yarage dan once yakoshi baya iya tursasa kanshi yaci abinci kuma, ajiye plate din yayi kan tray yadau ruwan shi dake cikin glass cup yakarasa shanyewa sanan ya ijiye yana kallon film din India daketa aiki dan tuni bacci yay awon gaba da Asiya dake ta kallonshi, cikin bacci ta daura kanta ahankali kan kafadar shi hakan yasa yajuyo ya kalleta ganin tai bacci yasa yadaga kanta daga kafadarshi. "Asiya" yakira sunanta, ahankali tabude ido ta kallai yace "go and sleep" murmushi tayi tana share idanunta da bayan hannu tace "Yayan mu nifa ba bacci nakeji ba" daure fuska yayi yace "go and sleep is late already" tashi tayi ahankali zatasa hannu tadau kayayyakin dayaci abinci dasu takai yahanata yace "don't worry, jeki kwanta nizan kaisu kitchen dakaina" gyadamai kai tayi kaman zatai kuka tace "gud night" gyadamata kai yayi batare dayace komiba ya jingina da kujera yana kallon TV tunani ne fall a ranshi, yakai almost 15 minutes zaune shi kadai afalon sanan yatashi ya kwashe su plate din yaje ya ijiye a kitchen sanan yafito ya kashe su TV da wutan dakin yarufo musu kofa yatafi flat dinshi wanka kawai yayi yay shafa'i da wuturi ya kwanta sai bacci.
Chapter 43 · 0% Book details