← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 102

Sashe 53

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Awa takwas yadauke su suka shigo garin Gombe, Habu nata nunamai hanyar kauyensu, suka dau wani hanya wacce itace hanyar kauyen, kauye da yadauke su kusan awa biyar sanan sukakai wani daji, ahankali Habu yace "dole zamu ajiye motan anan Alhaji mu karasa da kafa dan babu hanyar motar kuma, kauyen mu chan bayan dajin nanne saisa bama asan damu ba a Nigeria nan" saukowa Abba yayi batare daya damuba Habu ma yafito boot Abba yabude yaciro akwatinta yabama Habu yace "rike wanan" akai Habu yadaura sanan Abba yabude baya yajawo kafafun Rahima dake narka uban bacci, kuka tahauyi cikin Bacci tace "sakeni" kota kanta Abba baiyiba ya kulle motar yarike hannunta gam yahau janta bacci take dan taki bude ido bin Abba kawai take luuu kaman zata fadi tsabagen karfin mix din data sha tafiya kawai suke, har dare tamusu ahanyan nan amma ko darr Abba baiji aranshi ba, sunyi tafiya kusan na awa daya akafa sanan Abba yafara hango haske hasken fitilu Habu yace "mun iso, ga kararkaran mu chan" karasawa sukayi dudda darene amma all abubuwan da Abba ke gani shine bukkoki kusan hamsin ko dari azagaye, baiga ginin gini ba saidai ginin kara dasu bukkoki, sai gaishe gaishe Habu yake dayan kwararrun mutanen dake waje kafin yakarasa chan gaba wurin wasu bukka guda biyu da bishiya ke tsakanin su, sallama ya kwada. "Assalamu Alaykum mutan gidan nanan" daga ciki aka amsa. "muryan wa nikaji kaman mai gidana" dan dariya Habu yayi saiga wata mata tafito da daurin zanu a kugu babu riga ajikinta sai wani yaro agwai data rike akan cikinta yanshan dogon nonon ta dayakai cikin ta tsabagen tsawo dayan kuma yaron na wasadshi da hannu yana surutu irin na dadin nonon nan da yara keyi, bata da kiba sosai sai tsayi da gashin kanta data tufke kaman na yar bararoji, an kitse na gefe da gefen gaban kanta guda biyu jelar gashin har wajen kirjinta, saiga wata yarinya dazata fi Rahima tsayi itama rikeda fitila tana dagawa tana haska fuskokin su ganin Habu yasa matar da saka uban tsalle nonon na lilo da sauri dan karamin yaron ya saki nono ya juyo jin maman shi ta daka uban tsalle yana kalle kalle, matar tace "wayyo Allah na mai gida kadawo, Mairo kufito ga babban ku yadawo" wasu yarane suka dinga fitowa daga bukkan Abba ya saukar da kanshi kasa ganin babu riga a jikin matar, dudda baya ganin fuskokin su da kyau sabida darene bai hanashi ganin yaron dake shan mama ba, tsalle sukahau yi har wasu mutane suna fitowa daga bukkoki su suna lekowa, ganin haka Habu yace "bamu asabari muzauna magana zamuyi ba dawowa nayiba" da sauri ta kalli yarta tace "Mairo dauko as abari babbanku yazauna" da sauri yarinyar ta shiga ciki ba'a jimaba tafito da asabari ta shimfida Abba na kokarin zaunar da Rahima ta kwanta tana bude idanunta tana kallon kowa, zama matar tayi takalli yaran dasuke tsaitsaya suna kallon baban nasu duk maza gabaki daya kansu daya kaman yan shidda ta haifa, sai wani babba da yake sanye da kayan fulani da tsayinshi daya da Mairo wacce take itakadai ne mace ayaran, sai wanda ake bama nono shima namiji yakama yara Tara cib cib, yaran kaman bakwaini, anatse Habu yace "kinga wanan shine Alhajin danake fadamiki daya bani aiki a binni" da sauri takama baki tace "laaaaa shine baka gayamin ba ke Mairo kawoma Alhaji fura dan Allah yasha" da sauri Abba batare daya dago kai ya kalleta ba yace "a'a kibarshi nagode, magana nazo nayi dake dan yanzun nan zamu koma" da sauri ta gyara zama tace "to to ina jinka" Ahankali Abba yanuna Rahima dake kwance kusadashi databude idanu tarr tana kallon kowa awurin yace "nakawo miki y'ata ki rikemin ita na tsawo wata shida ne, kisamata tsaro bana wasaba, banda haka zan biya ki kinji, sanan zan aiko muku da kayan abinci gobe, dan Allah zaki rikemin ita?" da sauri tace "Alhaji harda su biya? Nawa zaka biyani to dan kaga yar bukkan mu tamana kadan nida yara Tara gakuma ta goma ta kawomana, dole sai....." da sauri Habu yace "Ladi" hannu Abba yadaga mai yace "barta, nawa ake Gina bukka anan?" ahankali tace "sun karamai kudi da muttala hudu ne yanzu muttala goma ne wlh wasuma har muttala shadaya suke karba" bandir din yan dubu guda biyu Abba yaciro yamika mata yace "ga dubu dari biyu agida bukkan na block amuku ginin sanan sauran kudin ki rike, ki kulamin da ita, gatanan gakuma kayanta intai ba daidai ba ki gyara mata, amana nabaki ita dan Allah kar wanda yanuna mata hanyar barin garin nan nasan ko zata shekara bazata taba ganewa ba" rudewa kam Ladi tarude karshen rudewa ma ganin uban kudaden da Abba yabata kaman a mafarki, dama sune yan gayun kauyen nan sabida Baban su Safara dake aiki a binni yanzu kuma ga wayan nan kudin ga yarinyar binni ai bakanta, da sauri tace "wlh, wlh, wlh na dauka zan kula da yarka na rantse da Allah, amana na dauka halak" ta kalli Habu tace "kagayamai komi kan kauyen ko?" kafin Habu yay magana Abba yace "ya sanar dani kuma dama irin kauyen nan nakeso ta zauna aciki, kome yataso ayi badamuwa wlh nan da wata shidda zanzo na dauketa" murmushi tayi tace "masha Allah, Allah yakusan bamu jika kenan" murmushi Abba yayi dan baigane hausan nata sosai ba yace "to mun tafi, Habu tashi mutai" wani irin zabura Rahima tayi ta tashi tsaye tana kallon Abban daya tsaya yana kallonta tace "Abba ina zaka ka barni anan? Su waye wayan nan?" ko kallonta Abba baiyiba dan baimaso yay magana da ita tsabagen haushin ta dayakeji yace "Ladi ariketa karta biyomu muntafi" mikama Safara yaron hannunta matan tayi takama Rahima gam tarike hakan yasa Rahima ta shiga kokawa da ita amma takasa koda fizge hannunta dan kashin Ladi yafi na rodi karfi, ganin takasa kwatan kanta yasa ta fashe da kuka tana kwalama Abba kira. "Abba meyakawo ni nan? Su waye wayan nan? Abba ina zaka ka barni eh? Ina mummy na Abba? Abba kaima ka tsaneni kaman mamana ko? Ka kaini chan wani wuri da bansan su ba yauma kasake kawoni wani wuri daban San kowa ba? Abba waime namuku da babu wanda kesona? Abba katafi ka barni kuma? " Abba yanajin duka kalamanta dudda sun mugun tabashi amma yadaure ko juyowa baiyiba har suka bace mata daga gani yanaji tana kuka tana kwalamai kira har suka shiga daji yadena jin kukan ta. .

40.
Chapter 53 · 0% Book details