← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 102

Sashe 14

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Around 5:02 ta tashi jin muryan Abba na kiranta, a firgice ta bude idanunta dasukai jajir dan kowani gaban jikinta najin kiran Abba ta kallai tanadan sassauke kai, babu alamun wasa kan fuskarshi yanuna mata kofa yace "wuce kije ki dauro alwala kiyi salla" gyadamai kai tayi ta tashi ahankali dan jiri take gani sosai bacci bai isheta ba, ganin tayi hanyar bayi yasa yajuya yafita dan sauri yake antada salla, bayin ta shiga ta wanko fuskarta tadauro alwala tafito tana kallon ko ina na dakin tadanji dama dama dan jirin yaragu sabida wanke fuskar datayi, wurin wardrobe din Mummy tayi tana kallon kofa da sauri tabude wardrobe din, hannunta tamika ganin hannunta baikai safe din dake chan sama ba yasa da tai wajen mirror, kujeran wajen ta dauko tahau kai ta tsaya hakan yasa takai safe din, password din da taga Mummy tasa jiya ta shiga sawa dan tana gani ta haddace shi tsaf akanta, bude safe din tayi jikinta har rawa yake, one bottle of codeine ta dauko gudun kar Mummy tagane sanan tasauko kara daya na wiwi tana waigen kofa, gyara zamansu tayi tsaf gudun kar mummy tagane sanan ta maida safe din tarufe tasauko tadau kujeran ta maida inda yake gaban madubi, sanan tadawo tarufe wardrobe din taboye abubuwan a jikin towel dinta sanan tabude kofa tafita tai dakinta, da sauri ta maida kofar tarufe jakar makarantan ta ta dauka ta zuba su aciki sanan ta rufe ta ijiye tana murmushi har wani murna takeyi kafin tai bayin ta, brush tayi sanan tai wanka tafito daure da towel, mai tadauka tafara shafawa saida tagama tsaf sanan tasake fadawa kan gado taja bargo ta lumshe ido ko minti biyu ba'ayiba bacci yasake awon gaba da ita.

Cikin bacci taji ana shafa mata fuska bude ido tayi da kyar tana turo baki ganin Mummy ne yasa ta mirgino ta daura kanta kan cinyar Mummy cikin muryan bacci tace "Mummmmm niban tashi ba" dagata Mummy tayi tace "tashi kafin Abban ki yakara tambayan ki, kinyi salla?" girgiza ma Mummy kai tayi ashagwabe, hakan yasa Mummy tace "toki barshi basai kinyiba, tashi ki shirya school, kinga yau zaku riga baban ku fita saisa naciro miki wanan abayan da gyalenshi ki saka banso kisa jean baban ku yahau miki fada" saukowa daga gadon tai da sauri tadau doguwan rigan da Mummy ke nunamata data ijiye kan kujeran mirror ta warware doguwan rigan tana daure fuska, hadadden doguwan rigane mai bala'in kyau na Dubai bakine complete babu kwalliya ajikinshi sai hannun doguwan rigan da aka bishi da wasu silver kullatai da akai musu design din flowers yay mugun kyau rigan. Cikeda rigima sosai ta kalli Mummy tace "Mummy nine zan sa kayan nan? Ni wlh bazan saba so ake zafi yakasheni eh" cikeda lallabawa Mummy tace "haba Auta na, Ke kinfiso ayita miki fada na yaune kawai gobe baban ki zaiyi tafiya yabar mana gida zakiyi yanda kikaga dama kinji" wurga rigan tayi chan wajen kofa tace "wlh ni banaso ni english wears zansa" dafakai Mummy tayi ta kalleta yanda ta zauna akan kujera ta juyamata baya tana kumbure kumbure, tasowa Mummy tayi takaraso har gaban madubin ta bayanta ta tsaya ta dafa kafadarta tana kallon fuskarta ta madubi tace "haba my fine princess, Princess Rahima na, yar lelen mamanta, duk gidan nan babu wanda zai nunamiki kyau wlh kai duk Abuja ma, beauty yar gidan Judge, yarinya inba dandan president ba sai rijiya adanmini murmushin nan mana" Mummy tadan chakuleta hakan yasa tafashe da dariya, ganin tafara dariya yasa Mummy tadauko rigan tace "imaza shiryo kici gayu kifito ina jiranki kizo kiyi breakfast kinji" gyadama Mummy kai tayi Mummy tawuce tafita.

Shiryawa tayi cikin dogon rigan tadau gyalen ta yane kanta dashi tadau wayarta tajefa cikin jakanta sanan ta giya jakan tabude kofa tafito tai falo, zaune taga duka yan gidan nasu a dinning, tunda tafito Abba ya tsareta da idanunshi dake cikin fararen glasses hakan yasa takaraso ahankali tayi kusada Mummy, da hannunta shiga wasa kafin murya chan kasa tace "ina kwana Abba" tea Abba yakai baki ba yabo ba fallasa yace "lpy" juyawa tayi ta kalli su Siddiqa da suma duk sun shirya zuwa makaranta dan hararan su tayi ta gefen ido sanan tace "ina kwanan ku" Siddiqa ce kadai ta amsa dan sauran basuda lokacin dan iskan gaisuwanta. "kin tashi lpy Rahima" ko amsawa batayiba tazauna kusada Mummy suka faracin abinci, tea kawai ta iya tasha dan ko kadan bata iyacin abinci inba Mummy ta samata abinda tasaba samata ba, batajin dadin cin normal abinci saida suka gama tsaf sanan suka tashi, 5k Abba yaciro daga pocket yamikama Siddiqa yace "gashi nan dukanku, adawo lpy" sanan ya kalli Rahima da nugayen ido yace "kibari akawomin karanki kiga abinda zai faru yau, kuwuce kutafi" wucewa sukayi suka fita, gaba Rahima tayi fuu tabarsu tana zuwa tabude gaba ta shige ta rufo kofar da karfi, da sauri Luba tace "iyye Ya Siddiqa bakene ke zama agaba ba, bari naje nafadama Abba" hannunta Siddiqa tarike da sauri tace "kubarta, muje inada hot presentation this morning, banda lokacin Rahima yanzu" duk shiga bayan motan sukayi direba ya shiga yajasu har zuwa University of Abuja, Siddiqa yafara saukewa agaban department dinta na Accounting tana 400 level, dubu dai dai tabama Zeena da Luba, duk suka mata godiya sanan tajuya tagaba tabama Rahima nata 1k din ta hanyar ajiye mata akan jiki, cikeda tsiwa Rahima tadau kudin ta jefar ta window tace "mezanyi da kazamin kudin ku? Mummy na tabani ☓2 of your chicken change, 10k dan haka banso" cikin tsananin fushi Siddiqa ta kalli kudin data jefo mata akasa tace "ni kika jefa da kudi Rahima?" "baki fasamata baki bane saisa har yanzu take mana iskanci" cewan Luba, ganin abin na neman zama rigima yasa Idris direba yace "dan Allah ayahakuri, bakuyi fada agida bane zakuzo kuyi a makaranta gashi anata kallonmu, kinga Siddiqa wuce ajinku kiyakuri yarinya ce" cikeda tsiwa Rahima tace "wlh ka kara cemin yarinya saina katsama mari hala nama kala da yarinya" bude marfin gaban motan Siddiqa tayi ta fincikota waje ta bala'in tsorata hannu tadaga zata wanketa da mari da sauri tarufe fuskarta tafashe da kuka jikinta na rawa tace "wlh kika dekeni saina gayaki da Mummy" sakinta Siddiqa tayi ta matsar da ita gefe ganin duk yanda ta tsorata sanan ta kalli direban tace "kaisu Lubabatu department katafi tajama kanta da kafarta zata taka tundaga nan har Vet wlh" tai maganan tana rufe marfin motan, direba yaja yay gaba, buga kafa ta shiga yi akasa tana kuka sosai Siddiqa tai tsaki tace "sai girma ba hankali, katuwa dake kina kuka cikin makaranta gashinan sai kallonki ake, ki kwana anan" juyawa tayi tai tafiyanta cikin department dinsu tabarta awajen sai kallonta ake.

Sauke jakanta tayi daga baya tana kuka tabude ta ciro wayarta ko tsayawa rufe jakarma batayiba tarike adayan hannun ta shiga neman layin Mummy, horn taji an danna mata da sauri ta daga kanta da idanunwanta dasuka rine da hawaye, kallo daya tamishi ta dauke kai wani shegen yaron ajinsune Chriss sunanshi Christian ne dayasamata ido, ajinsu daya shima Veterinary medicine yakeyi, duk inya ganta saiyace Hi beautiful amma ko kulashi batayi, fitowa yay daga motan da sauri hadadden guy ne yaci gayu sosai da wandonshi dayay ass down gawani hadadden sneakers akafarshi da katon sarkan cross yakaraso gabanta, cikeda damuwa yace "Hey Beautiful what happen? Why are you crying like this? Who was that Goddamn gurl that drag you out of the car?" yay maganan cikin fushi, daure fuska tayi tasa hannu tana share hawayen daya gama wanke mata fuska, cikin bala'i tace "is none of your business, leave me alone" "noo I can't, I can't leave you alone, u don't look good beautiful, let's go we have class by 9, and is to 9 now" kallonshi tayi da dara daran eyes dinshi, murmushi yamata yadan daga mata gira daya tareda cije lips dinshi yace "please beautiful let's go, I know u can't walk from here to our department, so let's go okay, plsss her majesty, plssss " yawani ja please din, dauke kai tace "okay" murmushi yayi cikeda jin dadi yana bala'in son Rahima tun rana na farko data fara attending lectures, batama uban kowa magana a ajin dudda yanda kowa yake shigemata gashi sai mahaukacin kokari da inba kaga tana amsa tambaya ba baxaka taba cewa tanada kokarin ba. Hannu yamika yace "lemme help you with the bag beautiful" murmushi tadanyi dan haka takeso ana treating dinta kaman sarauniya ta mikamai karba yayi da sauri yataho yabude mata shiga tayi sanan yarufe yazagaya ya shige shima yatada motar.
[7/7, 9:02 PM] +234 816 822 7336: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫

_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔

✍️ M Shakur

1️⃣2️⃣ & 1️⃣3️⃣
Chapter 14 · 0% Book details