← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 102

Sashe 24

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Magrib sukayi suka fito daga masallaci suka shigo cikin premises dinsuna dan tattaunawa, reception suka shiga wata mata suka hango sanye dawani bakin dogon riga dayaji stones tayafa wani mayafi milk color na manyan mata akai tarike wani handbag na LV tana magana da receptionist din wurin tana fada tace "ina kuka kaimin y'ata where is Rahima? Kubani y'ata natafi da ita shairi ake mata Rahima batashan komi saidai in wanchan yaron Chris shine ya koyamata taga yanasha ta dandana dan dama shiyay inviting nata to birthday party shi" cikin masifa Chris yace "No dey lie Madam, your daughter sabi everything so tey she dey carry for bag go school, no dey lie for my head ha'a see me see gbese o" cikin fushi Mummy ta juya zatai magana taga wani magidancin mutum tareda wani cikakken dogon bakin yaro dake sanye da jacket baki dabai ja zip dinba, rigan dayasaka mai ruwan toka ya bayana da kirjinshi hartana hango kwantaccen gashin kirjinshi baki sidik, dan girgiza kanta tayi ta saita idanunta kan Chairman kafin ta kalli wasu manyan hotunan frame dake jikin bangon reception din na president, da vice president saikuma hoton shi da aka rubuta chairman NDLEA, cikeda masifa tace "good ka iso Chairman, I guess you are the one I spoke to a while ago, ina y'ata take? Kubani y'ata natafi gida, shairi kuke mata Rahima babu abinda tasani, she is my last born, yaushe na haifeta duka duka da zaku kamomini yarinya daga taje birthday coursemate dinta kucemin shaye shaye take? How on earth is this possible?" anatse Chairman yace "Madam until your daughter's father is back and come here dakanshi I'm not releasing Rahima nor giving her to you" yana maganan yay hanyar office dinshi binshi Mummy tazo zatayi security suka tareta hakan yasa ta tsaya daga wurin, ganin bala'inta bazai yi komiba burinta shine tasamu su saki Rahima su koma gida asirinsu arufe batare da Abban su yasani ba amma taga ina wayan nan basuda mutunci hakan yasa ta shiga rokon security su barta taje taga Chairman sukaki.

Shiga office din sukayi daidai wayar chairman yahau ruri karasawa table din yayi yadau wayan ganin Mahaifin Rahima ne yasa yay picking yasa a kunne ya nemi waje ya zauna yace "good evening to you Sir, this is Alhaji Muhammad Mustapha Abdullahi Chairman din NDLEA, I've been calling you na sanar dakai wani muhimmin abu, mun kama yarka awani gida nan hanyar Kaduna kano express road ita da wasu yara maza da mata su talatin da daya da sunan birthday party tana shaye shayen miyagun kwayoyi da gwamnati tabada umarni duk randa muka gani yanayi mu kamashi sanan mu aika dashi rehabilitation centre, ganowa damukayi Rahima yarka ce mukuma dan matsayin ka akasar nan munkuma san yanayin matsaloli da fitintinu dazaka fuskanta in duniya tasan me ake ciki yasa mukace bari mu maka alfarman kiranka mu sanar dakai shima badan komi ba saidan labari dakuma yanda ake yabata akan aiki bisa gaskiya dakake yi ne" shiru Abba yayi na kusan minti takwas tunani yake Rahima shaye shaye, party da maza ahanyar wajen gari, shaye shaye, innalillahi wa innailaihi raji'un, Chairman ne jin shiru yasa yace "kana jina" ahankali cikin murya datai rauni sosai Abba yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un" saida yafada sau uku yasake yin shiru yama rasa maizaice, Murya chan kasa data nuna karara alamun bacin rai da tsantsan damuwa yace "Chairman banda abinda zan cemaka sai Allah nasaka da alkhairi, wlh bazan maka karyaba wutan kaina ta dauke dib I don't know wat to think, alfarma daya zakamin kawai yanzu zan kira mahaifiyar ta tazo ta dauke ta sutafi gida, first flight zan biyo nadawo garin nan gobe dasafe zanzo har office dinka nasameka zamuyi magana da kyau, nakumayi alkawari binciken case dinan da kyau nagode" ahankali Chairman yace "mahaifiyar yarinyar is already here badai mubata yarinyar bane daman munce dole sai munyi magana dakaine, yanzu kuma tunda munyi zamu sa abata ita sutafi gida" ajiyan zuciya Abba yasauke yama kasa magana hakan yasa Chairman ya katse kiran yana girgiza kai yace "rayuwa kenan saikaga a good man ya haifi boka, jarabawan Allah kanzo tako ina, please Lieutenant help me tell them sukaima matar yarinyar nan sutafi gida" tashi Sameer yayi yafita daga dakin ganin babu kowa a upstairs din yasa yay dining din dayake anan sama dama dining din yake yasaba zuwa NDLEA din so ba bakonshi bane babu inda baya shiga saidai in baisoba, bude kofan dining dinyayi tana zaune kan kujera ta kifa kanta kan table tana kuka ga takeaway din rice da stew dinta agefe ko kallonshi batayi ba, hannayenshi yazuba a aljihun wandonshi yay wani irin tsayuwa irin na sojojin nan yace "Ke!" da kakkausar muryan shi da sauri ta dago kanta gabanta na faduwa sabida yanda ya kirata, dauke kai tayi daga kallonshi ganin wanan mugun bakin sojan nanne daya mata wankan ruwa dazu. "zoki fita ur Mum is waiting at the reception" dawani irin mugun sauri ta juyo tareda ware jajayen kumburarrun idanunta tace "Mummy na kace?" shiru yayi bai amsata ba sai zubamata manyan idanunshi masusa mutane shakkan shi dayayi yana kallonta, dawani irin sauri ta tashi gabanta nafaduwa ta taho tana dingishi tabi ta gefenshi tafita da sauri tai hanyar stairs, ahankali yajuya yafito shima ya tsaya a daidai bakin benen har lokacin hannayenshi na cikin aljihun wandonshi yana kallon yanda take tafiya tana dingishi da sauri tana sauka, saida tagama sauka daga benen sanan tafashe da kuka sosai tana yarfe hannu kafin ta kwalama Mummy data juyama stairs din baya tana waya kira. "Mummy!!!" da sauri Mummy dake waya tajuyo ganin Rahima ga bandeji a goshi tabi tai daka daka kaman ba yarinyar data bar gida fess fess ba yasa ta zare wayan daga kunnenta tana kallonta, dawani irin gudu Rahima ta taho tana dingishi takarasa tawani fada jikin Mummy tareda fashewa da kuka sosai mai tsuma zuciya, bayanta Mummy ta shiga shafawa tace "ya isa, ya isa, am here now stop crying" dagota tayi tasa hannu tana sharemata hawaye tareda shashafa goshinta inda taga bandeji tace "maiya sameki anan maisa kike dingishi" cikin kuka tanuna Chris ashagwabe tace "wanchan matsiyacin ne Mummy mai kama da jaririn kunkuru shine ya fesamin goshi" wani mugun kallo Mummy tamai batason tai magana dan tasan yariga yasan few things gameda Rahima batason ya tona musu asiri hakan Yasa tace "barshi yama kanshi, let's go" security ne suka tare musu kofa bazasu barsu su wuce ba, Sameer dake gaban stairs a sama yana kallon komine cikin husky voice dinshi yace "let them pass" da sauri Mummy ta dagokai tareda juyowa hada ido sukayi da Sameer wani wawan faduwa gabanta yayi, chak ta tsaya tana kallonshi harsaida Rahima ta kalleta cikin muryan kuka tace "Mummy mutafi" ajiyan zuciya ta sauke takalleta tace "okay Auta muje" fita sukayi daga wurin security zasu maida kofan su rufe takara juyowa ta kalli Sameer daya fara tafiyan shi nan dai dai yay office din Chairman.
[7/7, 9:02 PM] +234 816 822 7336: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫

_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔

✍️ M Shakur

1️⃣9️⃣

Mota suka shiga Mummy taja motar suka tafi, saida suka shiga titi Mummy tace "what kind of matsala kika sani Rahima yanzu? Yanzu wani irin karya zan shiryama baban ki dazai yarda eh? Mezan cemai, kai! Innalillahi wa innailaihi raji'un, wanan Chris anyi dibabben yaro mai bakin jini da badluck mtsww" taja tsaki tana gudu ahanya, Rahima ba tace mata komiba gabanta faduwa kawai yake babu abinda take tsoro aduniya yanzu haka kaman haduwanta da Abban ta ahaka suka kai gida, su Siddiqa duk suna daki, dakin Mummy suka tafi direct wanka Mummy tasa tayi tabata abinci, kasaci tayi tace "Mummy bazan iya ciba, in Abba yadawo gobe kasheni zaiyi ko Mummy?" zama Mummy gefenta kanta takama ta daura akan kirjinta ta rungume ta tace "Hey am ur Mum ko, so kibar komi a hannuna, now eat ko kadan ne saiki sha paracetamol dinan karkiyi zazzabi kije ki kwanta kinji" gyadama Mummy kai tayi tasa chokali cikin abincin zata kai baki ta yatsine fuska tadago kanta ta kalli mummy, murmushi Mummy tayi tace "ina zuwa" tashi tayi tai wurin safe ta bude kara daya na wiwi ta dauko tazo ta juyemata a abincin juyawa tayi ta shiga ci da sauri dan yunwa takeji rabon ta da abinci tun rana, tana gamaci Mummy tabata paracetamol tasha ta kwanta ba'a wani dau lokacin ba bacci yay awon gaba da ita, tsayawa Mummy tayi tana kallonta barinma goshinta dake sanye da bandeji har lokacin da kafadarta dayadan kumbura sabida kulkin da matarnan tabuga mata sai wrist din kafarta, wani irin murmushi tayi ta tashi daga inda take tadau kulan tajuya tafita daga dakin.

Sai wuraren 10 yakoma gida sabida tsareshi Chairman yayi sai hira yakemai, shidai chairman arayuwanshi starting from rana na farko daya fara ganin Sameer yake bala'in sonshi, gabaki daya yama maida Sameer din wani abokinshi dudda ya girmeshi amma yana son yaron, jan Sameer din yayi har zuwa gidan shi sukai dinner mai rai da lafiya sanan wuraren 10 Sameer yamai sallama yarakoshi waje saida ya shiga motarshi yafita daga gidan sanan yakoma cikin gida yana murmushi.

Wuraren 10:30 ya isa gidansu Gate aka budemai yay Parking yafito, flat dinshi yawuce direct dan yasan Ummi tariga ta kwanta, sabida hawan jini dakuma matsalan kafanta yasa Dr yace tadinga kwanciya da wuri, yasan ta kwanta saisa bayason yaje yatadata, part dinshi yawuce ya shiga ya maida kofan ya rufe bathroom ya shiga yayi wanka yafito daure da dan towel a waist sanan yadawo falo agogo ya kalla so yake yakira Mu'az he has been busy da tubda yadawo daga zaria baisamu ya kirashi ba, sanin yay bacci yanzu yaja ya kunna laptop dinshi ya shiga yin some work da yakamata ace yayi, almost 1hr yabata sanan ya kashe ya ijiye agefe yay addu'an bacci ya kwanta.

Aka'ida dama ana kiran sallan asuba yake tashi, tashi yayi yashiga bayi brush yayi yay wanka tareda dauro alwala yafito jallabiya yasaka ya feshe kanshi da turare yafito, mai gadinsu yatada sanan yawuce masallaci.
Chapter 24 · 0% Book details