← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 102

Sashe 67

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda Sameer yahadu da Rahima yauce rana ta farko dayaji rayuwanta da ita kanta Rahiman ta mugun bashi tausayi, a mota ya zauna yana tunanin me zaiyi dudda dai bai basani ba for now abu daya dayasani shine zaman bazai kara bari tazauna da Mummy ba, and duk inda maman Rahima take aduniyan nan he will find her kiran magrib da aka fara yasa yafito yatafi masallaci, wuraren sha biyu ya shigo dakin yaga tadade daya in bacci bayan tasha fruits salad ta koshi.

Ranan bacci sosai tai da daddare bata tashi ba har sauda yatada ta da safe yace tai salla tai wanka zasu koma yau faduwa gabanta yayi shikuma yawuce ya sauka kasa dan zaiyi checking out and clear his bills, wuraren nine yadawo yaga tao wanka tana sanye da dayan doguwan rigan tai kyau dudda har yanzu da muguwa raman nan datayi hijabi yanuna mata yace "saka mutafi" dauka tayi tasaka tadau kayanta data hada a ledan suke suka fito sai kallon hotel din take tunda sukazo sai yau tasake fitowa sukai mota, gaba ta shiga shima haka hakanan saita tuna abinda tayi ranan wani kunya yakamata tada motan yayi sukadau hanya sai faduwa gabanta yake kaman akwai abinda zai faru da ita ahaka har bacci ya kwashe ta.

Saida sukai parking a hanya lokacin azahar yatada ta suka shiga wani masallaci kan hanya dudda na maza ne yasa ta koma chan baya tai salla shima yay nashi agaba sanan yasaya mata snacks suka koma mota bamata iyaci ba bacci yakara awon gaba da ita.
Horn dataji yasa tabude ido ganin suna kofar gidansu yasa ta gyara zama tana zaro ido gabanta nafaduwa Gate gateman yabude musu Sameer yaja motar ya shiga da ita ciki sai kallon motar Abba dayake a pake take sanan yay Parking yafito tareda kallonta, bude wa tayi tafito ahankali gabanta nafaduwa sosai sanan yafara tafiya tana biyeda shi, labewa tayi abayanshi yay knocking kofar sitting room dinsu, Zeena ne tafito tana sanye da atampa da dan kwali bamata lura da Rahima dake labe bayan Sameer ba dayake yanada tsayi, cikeda girmamawa tace "ina yini ya Sameer, Abba na nan amma Mummy taje sunan wata kawarta a Suleja gobe zata dawo...." "wa kika cikada surutu haka Zeenah" cewan Abba dake zaune a falo, da sauri Zeenah ta matsa tace "Abba Ya Sameer ne yazo abokin ka" da sauri Abba ya kalli kofan ganin Sameer yasa wani sahihin murmushi ya bayyana a fuskanshi yace "Lieutenant, bismillah, son shigo" ahankali Sameer yadaga kafa ya shiga dajin da murmushi kan fuskan shi hakan yabama Abba dasu Siddiqa daman ganin Rahima dake tsaye bakin kofan takasa shigowa kanta akasa sai rawa kafafuwanta suke sabida muryan Abba dataji, wani irin mikewa Abba yayi tsaye idanunshi kan Rahima saikuma ya kalli Sameer yace "are you together with this girl?" gyadamai kai Sameer yayi yace "Abba ka zauna is a long story" cikin fushi Abba na danne zuciyarshi yace "wani irin long story Sameer?" ganin yanda Abba ya harzuka he is not even ready yazauna and listen to him yasa yace "Abba sarkin garin dakakai yarinyar nan tried to molest her, he tried rape her, and she called naje and rescued her" cikin wani irin fushi Abba yace "try to rape her?" gyadamai kai Sameer yayi, dan shiru Abba yayi saiyadan yi murmushi kaman wanda yazare, kafin cikin wani irin masifa yace "finally tasami mashinshini" saikuma yay shiru kafin ahankali yafara walking hdown zuwa bakin kofan dakin inda Rahima take tsaye, sauka yayi duk su Sameer na kallonshi sun zaci magana zai mata kawai gani sukayi ya dauketa da mahaukacin mari yace "dan uwaki yau dinan ba gobeba komi dare aurar dake zanyi badai shaye shaye kika saka agaba ba zakiga hukuncin shaye shaye ya fizgi hannunta da sauri Sameer yafito kafin yafito Abba harya kaita motan shi yabude baya yajefata ciki ya rufe Sameer yagani, hannu Abba yadagama Sameer da zaiyi magana yace "quit son" Siddiqa data iso wajen da sauri tace "Abba dan Allah kaya...." shiga motan yayi ko kallonta baiyi ba ya danna uban horn, gateman yabude mai yafita.

53.....

Dafe goshi cikin masifan fushi Sameer yayi ya shiga motarshi kafin gateman yarufe yafice yabi Abban dayaga motarshi yamai nisa danhar yahau kan titi, sosai Rahima ke kuka tace "Abba dan darajan iyayen ka karka maidani kauyen nan, Abba dan Allah, wayyo Mummy na" ko sauraronta Abba baiyiba ranshi tafarfasa kawai yake duk in yatuna shaye shaye Rahima keyi sai yaji he can go to any limit to discipline her, dawani mahaukacin gudu Sameer ke binshi saida sukai nisa sosai saida Sameer yaga babu motoci sosai a express road din dudda yasan wat he is about to do is risky sanan yay wani irin over taking Abba kafin yay kwana yasha gabanshi motar Abba dat was on high speed yataka wani mummunan birki da saida Rahima ta kwala ihu dan tazaci mutuwan tazo kiris yarage baufi tsayin finger ba da motar Abba tadaki ta Sameer, Sameer bai damuba yabude motar yafito shima Abba ya kashe motar yafito yayo kan Sameer cikin fushi yace "so kake na kashe ka Son?" Sameer baimabi takan tambayan da Abba kemai ba cikin fushi yace "where are you taking Rahima to?" sosai zuciyar Abba ke tafarfasa yay pointing motarshi yace "Sameer that girl Rahima shaye shaye take, babu namijin kwarai dazai yarda ya aureta tariga tama rayuwanta illa, Sameer inhar Rahima tasami wani dake kokarin mata fiyade alamun sonta yake kenan, tunda dai sarkin musulmi ne kuma magidanci zan maidata kauyen, nace mai ni mahaifin tane he don't have to rape her gani nan nakawo ta nabashi aurenta ko karfe nawan dare nakai gombe saina daurama that stubborn girl aure da sarkin nan" Abba yay maganan yana kumfan baki kaman baisan meyakeyi ba, dawasu red eyes Sameer ya kalli Abba yace "Abba kariga kace am your son, kabani amanan not just Rahima your last daughter but your whole entire family, and you call Siddiqa, Lubabat, Zeenat and Rahima my sisters, as a Son, kasan Son can stand up to mahaifan su su nuna musu sunyi kuskure, Abba you are blind today, ka makance da fushi da anger, children smoke children take illicit drugs but this you are doing will push them suyi drugs din more" yy shiru sanan ya kalli Abban dake kallonshi babu ko tsoro yace "there's no way am going to allow you marry this gurl off to a rapist, kasan hukuncin mutumin nan kuwa, metayi? Wani laifi tayi dazaisa kamata wanan hukuncin dat will affect her life forever, just because of shaye shaye? Eh? Eh" yay ma Abba ihu cikin fushi kafin yakama hannun Abba yadaura kan saman kanshi yana kallon Abba a ido yace "Listen Abba! I Lieutenant Sameer Simran swear to you I will marry her, tunda dai aurar da ita kakeso kayi zan auri Rahima Abba, just give me from now zuwa anjima, I will meet my parents da zancen meanwhile I take her back to rehab centre, anjima around isha'i nida da yan uwana zamuzo muje masallaci ka daura min aure da ita, you will see how I will change the Rahima dakake kokarin wulakanta rayuwanta ayau sabida tana shaye shaye to Rahima da tadena shan komi tadawo that dream daughter da u always picture Rahima to be, and I swear to you, swear to you, wlh, wlh baxaka taba aurar da kanwata to that man ba, you are a judge kafin kowa sanin hukuncin shi amatsayin na mutumin dake raping underage, that pervert of a man, a pedophile but u are too blind da fushi yahanaka gani kana kokarin bama yarka auren shi, as am talking to you now that man is under hot hot interrogation while the whole village government have evacuated them, babu kowa on that village, yaran dayama ciki sama da 15 are under serious check ups, you can check the news channels television news sun dau rahoton komi and see the work of the man u are trying to get your daughter married to, dats all am going to tell u" yawuce shi cikin fushi yaje wajen motan Abban yabude back sit Rahima yagani takife kanta kan cinya kuka take kaman zata shide, hannu yasa yadagata yakamaa hannunta yarike yafito da ita daga motar sukazo suka wuce tagaban Abba taba kuka sosai yabude motarshi yasata ciki ya shiga mazaunin direba yaja motar yay kwana yabar wajen a zuciya batare daya kalli Abba ba.

54 & 55

Abba yadade tsaye kan titin nan ko motsin kirki yakasa kalaman Sameer kaman sunyi resetting brain dinshi, he can't believe what he just heard, uban horn da ake dannamai ana Malam lafiya sabida yanda ya kashe mota yafito shikadai ya tsaya kan titi tareda rungume ciki kaman wanda yasoma zarewa, horn din suka dawo dashi daidai hakan yasa yajuya da sauri yay cikin mota ya kunna yabi u turn yakoma gida haryaje gida yaran namai magana kasa amsasu yayi sai dakinshi kawai yawuce yarufe tareda zama, ko Allah yasan yana cikin wani farin ciki da mugun mamaki ne abu biyu atare, Sameer, Sameer this well mannered yaro, baligi dakeda cikakken hankali, da yasan yakamata, yakeda aikinyi, wanan babban mutum dinne zai auri Rahima yasake tambayan kanshi heart dinshi na racing, saikuma yace "ahhh haladai kawai yafada ne dan karna maidata kauye yakaita rehab" wata zuciyan yacemai karka yarda harsai kaga sunzo anjiman shida yan uwanshi da isha'i sunzo adaura auren sanan saika yarda, tayaya ma mutum kaman Sameer zai auri Rahima, haka Abba yazauna ya kwance ya kulla ya kwance ya kulla shi kadai yakasa yarda cewa Sameer zai auri Rahima.
Chapter 67 · 0% Book details