← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 102

Sashe 40

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Arude Mummy da isowarta dakin kenan tadafe kirji ganin Rahima tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un, Abban su! Sameer! menene wanan a hannun Auta na? Kwalaben meya wayan nan akasa? Wiwi, taba, Rahima, Auta na" tai cikin dakin da gudu tai kan Rahima fizge karan wiwin tayi tayar akasa cikin ihu kaman wacce tasoma zarewa tace "Auta kina haukane tarbiyan da muka baki kenan? Wanan wani irin abin kunya ne kikeyi agidan mahaifinki eh? Agidan mahaifinki kike shaye shaye?" ko kadan Rahima batasan me Mummy ke cewaba idanunta kan wiwi ta da Mummy tayar akasa yanaci harya soma kona carpet din wurin, da sauri tai rarrafe tai wajen wiwi kaman wata tsohuwar mayya zatasa hannu tadau karan wiwi jikinta har rawa yake wani irin zuciya ta kwashi Abba yaji karfi yazomai ya tashi daga jikin kofan dayake, cikin wani irin kunan rai daidai tadau karan wiwi zatakai baki yasa kafa yay wani irin kwallo da ita saida bayanta ya bugu da wardrobe din dakin wiwin yafadi akasa ta buga bayanta awurin, kaman wacce bataji zafiba, bude idanunta tayi ahankali dasukai jajir, kaman wata wawiya tasa hannunta akasa tadafa ta tashi tsaye da kyar tana kalle kallen kasan dakin tana neman wiwin ta tana layi, so kawai take ta cigaba da sha tana ganin sojoji nabama maman ta wahala, ganin bamata san ya daketa ba haukanta take tana neman wiwi yasa Abba yawani fizgota ya jijjigata tareda dauketa da Mari ya kwala ihun kaman zai fasa gidan yakirata da kakkausan murya. "Rahimaaa!" dafe kuncinta tayi dan wanan karan marin ya shigeta kafin tasa hannayenta ta shiga dirza idanunta kaman wacce idanunta kemata kaikayi sanan ta cire hannun tabude idanunta da kyar tana zaro idanun dan bata ganida kyau kafin idanun su washe ta kalli Abba ido cikin ido, turo baki tayi cikin maye tace "wlh ka kara dukana saina rama mugu kawai azzalumi, angayama yanzu dane, bana tsoron ta mutu balle tai tsami, nice owlet, and I am a pj mask, bari kaga Halloween wind" tawani daga hannu tana huroma Abba iskan bakinta adole zata dagashi sama ta yar kaman yanda owlet keyi a cartoon din, ganin bai matsaba yana tsaye agabanta yasa tafashe da dariya tanunamai muscles dinta duka biyun tana zaro mai idanu, cikin fushi Abba yasake jijjigata yace "Rahima bazaki dawo hayyacin kiba, Rahima, Rahima Allaahumma ajirni fi musibati w......." kabar da hannun Abba tayi daga kan kafadarta tace "leave me alone this man, I hate you wlh, dama kowa baya sona dukkun tsaneni nima na tsaneku, kullum kaita dauremin fuska ka kira su Ya Siddiqa, Ya Lubabatu, da Ya Zeenatu kan kujera kusada kai amma bakako kallona, nima I don't need you kaji old man, Mummy na kadai nakeso, ita kadai, only Mummy, only Mummy" tai maganan tana washe baki duka fararen hakoranta awaje tana layi tace "I love my Mummy, Mummy I love, zankai ki all the 7 continent damuke dashi in the world, Europe, Asia, North America, South America, Antarctica, Australia yayyyy oya give them Mummy zannnnku legg work" yashiga rawa tana zanku agaban Abba sanan ta tsaya tareda rike kwankwaso takawo fuskarta kusadana Abba tana kallon kwayan idanunshi har harshinta na gogan nashi tana busamai warin wiwi datake yi, cikin mugun fitsarin da shaye shaye kesawa tace "kaiko mugun, bakasona bansonka, I hate you! I hate you! I hate you" tai maganan tana turashi baya ta hanyar sa hannayenta akan kirjinshi ta tureshi da karfi, da sauri Siddiqa tace "Rahima!" dakuwa Rahima tamata tace "babu ruwanki dani jaririyar kunkuru tom" komawa baya Abba yayi yana kallonta kirjinshi nawani irin bugawa dabai tabayiba yana kallonta, biyoshi tayi tazo har inda yake tsaye kusada Sameer da yatsa tanuna shi tace "ka kara zuwa nan wlh saina zaneka ciki dabai, mugu kwai, wicked man, wlh bansonka" wani irin fadawa jikin bango Abba yayi kaman wanda aka tura any kalman I hate you na Rahima nasa zuciyarshi bugawa, wani irin nishi ya shigayi da baki trying to control yanda numfashi ke fita daga kirjinshi yana kallonta yana bude baki dan kaman nostrils dinshi sunmai kadan wajen fitar da numfashi, ganin haka yasa Sameer da sauri yarike shi yace "Abba Abba, listen Abba calm down kaji, batasan metake cewaba, bata hayyacin ta, don't allow her words gets to you, muje kafita daga dakin he falo ka huta" hannu Abba yasa kan kirjinshi yana bubbugawa yana wani irin lumshe ido kaman wanda ke shirin mutuwa, da sauri Mummy tazo wajenshi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Alhaji" da sauri Sameer yadago kai ya kalli Zeenatu dahar tafara kuka duk suna kallon yanda Abban nasu yakeyi yace "kawomin ruwa" wani irin tari Abba yashiga yi yay kasa kafafunshi na lankwashewa zai fadi da sauri Sameer yatare shi tareda zaunawa yadaura kanshi kan cinyarshi yadan dago kafan nashi sama sabida mugun tarin dayakeyi, ruwa Zeenatu takawo da gudu tabama Sameer, karban ruwan Sameer yayi yabude yakafa abakin Abba yazuba ruwan, tari sosai Abba ya shiga yi ruwan na fitowa kafin ruf yarufe idanunshi kaman wanda ya mutu ko suma, ihu Zeenatu tayi tace "Abba, Abba, Mummy Abba na menene" da sauri su Siddiqa da Luba suka karaso suka duk tsugunna suka zagaye su suna kuka "Abba, Abba" tsawa Sameer yadaka musu cikin fushi yace "ku fita! Out! he need air ba mutuwa yayiba, he's under shock, just a mild heart attack, ku fita kutafi dakinku" da sauri Mummy dake tsaye kansu jikinta na rawa tace "kufita kufita kunji me yayanku yace baban ku needs air, Siddiqa ki dauko wayana kan gado ki kira likitan baban ku kice yazo yanzu he is sick" da sauri suka fita suka rufo kofar Mummy ta fashe da kuka sosai tadau pillow gadon Rahima tana kallon Rahima dake tsaye tana kirga silin din dakin da yatsun tana layi bamatasan me akeyiba, kaima Sameer filon tayi tana kuka sosai ta ijiye akasa tace "sakanshi anan Sameer ya kwanta" ahankali Sameer ya kwantar dashi yana kwancemai neck tie din wuyanshi, fashewa da kuka sosai Mummy tayi ta tashi tai kan Rahima kifa mata Mari tayi ta jijjigata tana kuka tace "sokike ki kashe babanki? So kike ki kaishi lahira tun kafin lokacin shi yayi, Rahima waya lalata ki haka eh?" ta kalli Sameer cikin kuka daya dago kai yana kallonsu tace "wlh Sameer dazu ina kitchen naga tafice tsakar gida I tot maybe tafita kwaso shanyan kayanta ne fita kikayi ko?" ta jijjiga Rahima cikin fushi tace "kananun samari nan dakike dashi da basu gama balaga ba su suka kawo miki kwayoyin nan ko Rahima wani kudi kika basu dan nasan bakida ko anini" Mummy tafashe da kuka kaman mai shirin shidewa tace "to kodai ciki suka miki?" da sauri Sameer ya kalleta, ta gefen ido Mummy taga yana kallonta hakan yasa tasan yes! She just hit the right spot, hakan yasa ta cigaba cikin kunan rai tace "I've noticed kwanan nan bakida aiki sai bacci, bacci, bacci, Rahima look at you, you are just 20yrs but kinmafi babban yarku Siddiqa komi na y'a mace, kinfi yayyunki cikan nono, hips da sauransu, zuwa kike maza na kama miki suna matse kiko, dama ranan da wata yar ajinku ta tareni danaje dropping naki a department dinku tacemin taganki agidan wani dan ajinku dake zama offkay kuna wasa yana kama jikinki taga ku shiga daki sai yamma kika fito sanye dawata riga daban dana wanda kika shiga dashi, nama yarinyar fada na karyatata na zageta dan nasan baki taba dawowa gida dawani kaya dabamu muka saimiki ba yasa ban yardaba, Rahima NDLEA suka kamaki still shima ban yardaba dannasan birthday party kikace min zaki na classmate dinku ashe kinyi irin bacin nan, kin lalace, bin maza, shaye shaye dukke kadai wani irin JARABTA (M Shakur book) dahar zaki iya kunna sigari ne ma ko wiwi agidan ubanki, gidan iyayen ki kinashaye shaye, innalillahi wa innailaihi raji'un, me kikeso mufadi ma Allah akan tarbiyan da muka baki, mahaifinki ya killaceki yahanaki zuwa school, yahanaki fita ashe jira kawai kike yabar gida na sakan daya kiyi abinda ranki keso, dama baccin karyane eh Rahima? Ban taba dukanki ba amma yau kinyi kuskure wlh saina zaneki Auta, saina zaneki auta" Mummy tai maganan tana rufeta da duka tako ina Rahima na tureta tana turo baki kaman ma batajin dukan, Sameer na kallonsu baice ko uppan ba ko kyafta ido bayayi Rahiman yake kallo, daddaggewa Rahiman tayi ta tura Mummy cikin maye Mummy tai baya da gangan tawani irin fada kan jikin Sameer dake shafama Abba ruwa a goshi, unexpectedly yajita kanshi before you know it Mummy tafashe dawani mahaukacin kuka sosai tana kara shiga jikin Sameer din, tunda take aduniya tsawon shekaru hamsin da hudu zuwa hamsin da biyar kenan bata tabajin kamshin turare mai dadi kaman irin kamshin da Sameer keyiba, chusa kanta tayi awuyanshi kaman sabuwar vampire tana kuka tana goga fuskarta a thick neck dinshi tace "zan mutu Sameer Rahima zata kashe iyayenta da bakin ciki, innalillahi wa innailaihi raji'un" tureta Sameer yayi daga jikinshi da sauri cikin wani irin yanayi yatashi tsaye da sauri yana kakkabe jikinshi hakan yasa Mummy kaman wacce hankalinta ya gushe ta kwanta warwas akasa tana kuka harda birgima kaman irin bama tasan me tayiba dinan, fashewa dawani mahaukacin dariya Rahima tayi tafara rawa tana juya jiki kaman wacce taje dancing school, motsin da Abba yayi yana kokarin bude ido yasa da sauri Sameer ya tsugunna akanshi yarike hannunshi tareda kiran sunanshi. "Abba, Abba am right here open your eyes" tsagaita kukan Mummy tayi ta taso da sauri tazo dayan side din Abba, hannunshi takama tace "Alhaji gani nima katashi kaji" ahankali Abba yabude ido tareda sauke wani irin ajiyan zuciya, idanunshi ya sauke akan Rahima dake rawa sosai kaman an kunna disco, da yatsa yanuna ta cikin muryanshi da bata fita sosai yace "s....s......son t.....a" yakasa karasa maganan yay shiru sabida yanda numfashi kemai mugun wuya duk wanda ya ganshi yasan yana bukatan oxygen, cikin kokartawa da jarumta yace "he......her......take......her t......to.....re.....hab....." ganin yakasa karashe maganan yasa Sameer ya girgiza mai kai yace "stop talking Abba you need rest, nakaita rehabilitation centre?" gyadamai kai Abba yayi ahankali yace "n.....n..." da sauri Sameer yace "now?" gyadamai kai Abba yayi da sauri, ahankali yace "okay calm down" tashi yayi batare daya kalli Mummy ba yace "Mama stay with him har Dr shi yazo, bari na kaita" yana maganan yay kan Rahima dake rawa kaman an mata wahayin rawa, fizgo hannunta yayi cikin fushi ihu tayi. "ahhhhmmmm, saken maye, saken" tadaga dayan hannunta zata bugamai ya hada biyun yarike azuciye jijiyoyin kanshi na fitowa ya fizgeta, ganin ko dan kwali babu akanta ga jelar kitson gashinta dake lilo yasa yasake ta hijabin daya gani tare da dadduma gaban mirror yaja yasake fizgota da hannu daya tana kokawa dashi yasaka mata sanan yajata tareda bude kofa, kafa bakinta tayi kan hannunshi cizonshi tayi ya fita daga dakin da ita amma ko gexau baiyiba yay falo da ita su Siddiqa duk suna zaune sunyi zuru zuru, tausayi suka bashi hakan yasa yace "kuje ku zauna da mamanku am coming" yabude kofa yafita da Rahima dake ihu tana tirjewa tana fada dashi sosai, ganin turjemai takeyi yasa yawani dauketa kaman yadau kara yadagata sama yay motarshi da ita bayan motar yabude ya jefata ciki ya maida kofan ya kulle ya shiga gaba yarufo motar duka yaja motar gateman yabude mai yafita daga gidan, ihu kawai Rahima take a motan tana tsalle, hijabin ta zare ta yar a kasan motan ta shiga tsalle, saikuma tafara hauka takama kan kujeran gana tace "pitttt pittt pitttt, motana motana mai take kawunan kunkuraye, jiiinnnn, burundun dudundundun vuuuuuuuuwwuuuuuu" tana haukan tana tsalle cikin motan tana wasu yare na mahaukata.
Chapter 40 · 0% Book details