← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 102

Sashe 29

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

4- حفظ النسل kiyaye zuri’a ko
Dangantaka like ( wane Dan gidan wane ko jikan wane) wanan duk abun kiyayewa ne cikin shari’ar musulunci, duk wanda yaje yay shaye shaye like shan giya ko sauran kwayoyi da suke bugarwa yayin da hankalinsa ya pita daga jikinsa zai iya zagin duk wanda ya gani yaci mutunci duk wanda ya ga dama yayi ma duk wanda yaso kazafi yace wane dan zina ne ko wane ba Dan gidan wane bane, wanda hakan a shari’ar musulunci zai jawo ayi masa bulala tunda yayi ma wani kazafi ba tare da gaskiya ba kuma duk shaye shaye nasa hakan. Cikin سورة البقرة Allah yana cewa ولا تلقوا بأيديكم إلى التهلكة kada ku jefa kawunanku zuwa ga halaka wanda duk me busa hayaki yana cikin wanan layin dan suna jefa kansu ga halaka ne, likitoci sun tabbatar suwa suna basusan iya adadin da suke mutuwa duk shekaraba ta sanadin busa hayaki,
Allah mai girma yana cewa cikin;
سورة الإسراء ( ولا تبذر تبذيرا إن المبذرين كانوا إخوان الشياطين )
Kada kayi Almubazzaranci, hakika masu almubazzaranci sun kasan ce yan uwa shaidanu ne.
Allah mai girma cikin
سورة النساء yana cewa ( ولا تقتلوا أنفسكم )
kada ku kashe kawunan ku, wanda duk yake busa hayaki yana kashe kansa ne a sannu sannu.
Akwai hadith daga Annabi mai tsira da aminci yana cewa
( من شرب سما فقتل نفسه فهو يتحساه في نار جهنم خالد مخلدا فيها أبدا)
Atakai ce hadisin yana nupin wanda yasha Summu ( Abinda zai kashe mutum like fiya fiya ko crack yayan cociene) zai zama yana cikin wutar jahannama kuma yana me dawwama, dawwamar da babu pita cikinta.
Akwai hadith d yake cewa ( لاضرر ولا ضرار ) ba’a yarda ka cuta ko a cuceka ba wanda duk yake shaye shaye yana cutar da kansa hakuma mutanen da suke kusa dashi ta hanyar busa musu hayaki da sauransu wanan duk haramun ne a shari’ar musulunci, akwai hadith da Annabi yake cewa "duk wani abu maisa maye giyane sanan duk wani abu maisa maye haramun ne. So mesa zakizo kiyi going against your religion and its teaching kan dadin da is not everlasting eh?.
[7/7, 9:02 PM] +234 816 822 7336: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫

_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔

✍️ M Shakur

2️⃣2️⃣

Not edited

Fitowa yayi daga masallaci ya shiga motarshi ganin wayarshi daya bari na kuka kan kujera yasa yadauka ganin Chairman ne, murmushi yayi yakara akunne yace "Sir" daga tachan bangaren Chairman yace "My Friend kana inane ina jiranka fa, Judge yakira yaji komuna hanya yana jiranmu" dan sosakai Sameer yayi yace "yanzu nagama daga aiki natashi, I think katafi karyayta jiranmu mu duka ba dadi, am right behind u zanje gida nai wanka na shiryo nazo just go Sir" dan shiru Chairman yayi kafin yace "shikenan Lieutenant Sameer dina, saikazo" katse wayan yayi yatada mota zuwa gida da ya shirya.....

Wanka Rahima ta shiga tafito, zama tayi agaban madubin ta dudda gatanan gatanan ne she is feeling sick sosai amma saida ta daure tai hadadden makeup kaman zataje biki tasa wani nude lipstick tasaka kwalli idanuwanta sukai shegen kyau, tashi tayi tabude wardrobe dinta wani black dogon riga ta dauko mai hannaye baby pink tasaka dayake tai shaping rigan ya bala'in mata kyau sanan tadau dankwalin takoma gaban mirror ta zauna kan kujera tana kokarin daura dan kwalin aka bude kofar dakinta, dagakai tayi ta kalli kofar, Lubabatu ce itama taci gayu tasa doguwan rigan atampa ja yay mata kyau sosai, ta yafa jan veil hakan yasa ta ballamata harara tace "baki iya sallama bane malama" hararanta itama Lubabatu tayi tace "sabida baki koyamin ba saisa banyiba, kuma malama kifito Dady yace sun iso kowa na falo, stop trying ki daura gyalen nan akai, better learn how to yafa gyale da shegen kananun kitson kanta dasukai tsufa" tamata gwalo tasowa tayi cikin fushi tabiyota Lubabatu takwasa aguje tana dariya tai falo ganin haka yasa tai kwafa takoma daki turare ta dauka ta fesa sanan ta yafa gyalen akanta tawuce tafita tai kyau kayan daidai ita, daga Mummy saisu Siddiqa a falon kowa yay kyau Mummy tasaka wata doguwan riga brown irin na manyan matan nan tai kyau sosai ta yafa mayafi na alfarma, zama tayi kusada Mummy kaman zatai kuka tace "Mummy kinga Ya Luba tazo har dakina tana neman tsokana na ko" hannunta Mummy ta shafa tace "yakuri anjima zan mata hukunci, kinga yanzu bakin Abbam ku sun riga sun iso yafita shigo dasune kiyakuri kinji" gyadamata kai tayi daidai Dady ya kwada uban sallama, amsashi Mummy tayi ta tashi daga zaunen datake ganin Chairman mutumin jiyane yazo yasa tace "ahh Chairman kaine, marhaban dasu lale barka da zuwa" cikida fara'a Chairman yace "barka dai Hajiya, kingafa haka Allah ke hada zumunci komi da sanadi" dan dariya Mummy tayi tace "hakane, bismillah ka zauna, a'a kai kadai ne ina dayan?" kafin Chairman yay magana Dady yace "yana hanya bai dade da tashi daga wajen aiki bane yanzu muka gama waya dashi yace gashinan zuwa" cikeda fara'a Mummy tace "ayyah to Allah yakawo shi lpy" Siddiqa ce tafara gaidashi tace "barka da zuwa Abba ina yini" kafin ma ya amsa sauran suka gaidashi. "ina yini Abba" ahankali Rahima dake gefen Mummy tace "ina yini" murmushi yayi yace "sannun ku yarana, ya karatu?" atare sukace. "Alhamdulillah" Abba ya kalla yace "what a nice family you have Masha Allah, Allah ya rayamana" ahankali Abba yace "Ameen Ameen" Chairman yace "yaranka nakama dakai sosai wlh, Rahima ce kadai batai kama dakaiba" yanuna Rahima dake gefen dadi dan itakadai ce fara a yaran as auran duk black beauties ne, murmushi Abba yayi ya kalli fuskan Rahima yace "Rahima auta" dan dariya sukayi Mummy tace "Alhaji food fa is ready akawo ne?" da sauri Chairman yace "No no madam abarshi bayan isha'i lokacin Sameer ya iso, sai ayi komi by then in sha Allah" hira suka cigaba dayi kafin akira isha'i suka tashi sukai masallaci su Siddiqa kuma sukai dakin dan zuwa yin salla, wayan Chairman dana dasuka bari akan kujera dan zuwa salla ne ya shiga ringing, ahankali Rahima tace "Mummy ana kiran wayan abokin Abba" gyadamata kai Mummy tayi tace "eh" ganin wayartai shiru na Abba yadau ruri yasa Mummy tace "bani wayan nan Rahima ingani" tashi Rahima tayi tadau wayan takawoma Mummy karba tayi ta kalli wayan Lieutenant, da sauri tace "ina ganin abokin Baban ku dazaizo ne yakira wayan Chairman yaji shiru yakira na baban ku, tashi kije kidubo waje Rahima inkinga bako ki shigo dashi kar abarshi a tsaye" gyadama Mummy kai tayi ta tashi daga kan kujeran tawuce tafita, slippers dinta dake bakin kofa tasaka tai hanyar Gate tana turo baki yau ko kadan bata hutaba, ahankali tabude Gate dinsu ta leko wani black mota Bentley tagani pake akofar gidansu gawani mutun tsaye jikin motar da bata ganin fuskarshi dan yabata baya fuskarshi na kallon hanya rikeda waya a hannunshi yana dannawa yana sanye da skyblue shadda bugaggiyar gaske tundaga Gate din takejin kamshin dayake yi, fitowa tayi daga Gate din gabaki daya ta tsaya daidai Gate dinsu tadan daga zazzakar muryan ta tace "kaine ke neman Abban mu?" wani irin juyowa Sameer yayi hannunshi daya sanye cikin aljihun wandonshi daya kuma yana rike da waya faduwa gabanta yayi sosai dan taga fuskarshi sabida hasken wuta dayazagaye kofar gidansu, kaman yanda ta zuba mai ido haka ya zuba mata ido, daure fuska tayi ta dauke kai daga kallonshi sabida yanda yawani cikamata ido tace "me kazo gidanmu?" daure fuska yayi yace "are you talking to me?" juyawa tayi batare data kalleshi ba tace "ance kashigo" tabude Gate dinsu ta shiga, ahankali yabiyo bayanta ya shigo gidan yana kallon yanda take tafiya kaman zata tashi sama har zuwa gaban flat dinsu ta tsaya ta juyo tareda kallonshi dan tasan inta shiga batare dashiba Mummy zatace mata ina bakon, kallonshi tayi yanda yake tafiya daidai hannunshi har lokacin a cikin aljihu dayan kuma yana daddanna waya yana tafiya ahankali, ashagwabe kaman zatai kuka dan ta gaji bacci kawai takeso tayi tace "ni kayi sauri kona tafiyata wlh na barka anan" dagokai yayi ya kalleta jin anbude Gate yasa ta kalli Gate da sauri ganin Abba ta ne yasa da sauri ta taho inda yake jikinta har rawa yake ta kallai tana satan kallon Abba tace "uhmm sannu dazuwa, ance ka shigo ciki" "Lieutenant" yaji Abba ya kirashi hakan yasa yajuya da sauri ganin Abba ne da Chairma yasa yakarasa suka hade ya mikamusu hannu cikeda girmamawa yace "welcome sir" cikeda farin ciki Abba yace "yaushe kazo Lieutenant?" ahankali yace "just now sir" kallon Rahima dake tsaye Abba yayi yace "what are you doing outside Rahima?" ahankali tace "Mummy tace naje na shigo dashi taga yakira wayar ka ne" cikeda fara'a Abba yace "Allah sarki sorry masallaci mukaje munbar wayan mu aciki, kumuje ciki" da sauri Rahima tai gaba suka biyota abaya suna hira.
Chapter 29 · 0% Book details