← Book details Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 102

Sashe 63

Bin Abinda Zuciya Ke So Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ahankali Mu'az yace "good morning Ya Sameer" anatse Sameer yace "morning kiddo, why are you disturbing Ummi?" kaman zaiyi kuka ashagwabe yace "Ya Sameer nifa kudi nakeso tabani waidan nace tabani Atm card dinta shine wai ina damunta bazata bayarba zan emptying account dinta" ahankali Sameer yace "tome zakai da kudi?" ashagwabe yace "aski zanyi fa, sanan da gyaran farce" gyadamai kai Sameer yayi yace "alright will transfer money for you, but kadena damun Ummi at her age bata bukatan damuwa sai kwanciyan hankali daga wajenmu, karka bari takara kawomin irin wanan complain din am I clear" gyadamai kai Mu'az yayi kafin ya saramai ya buga kafa akasa yace "Crystal clear Sir!" da sauri Ummi tace "wlh kafasamin tiles saika kawo kudin gyaran su" daga tachan bangaren Sameer yace "bama Ummu wayan" da sauri ya kaima Ummi wayan ta amsa ta kara a kunne yace "okay Ummi namai magana, inya kara damunki just let me know" hararan Mu'az din daya daura kanshi kan cinyarta tayi yana daddanna waya abinshi tace "balm din kafafu na yakare Soja, na aika su Noor da Muhammad basu samomin ba wlh, duk pharmacy dazasu babu" gyadamata kai yayi yace "idan zan dawo zan tahomiki dashi" murmushi tayi tace "shikenan nagode, Allah yay albarka, kome zakayi kadinga yi tsakani ga Allah kaji, abinda akayi tsakani ga Allah, Allah yafi sanya albarka cikinshi, Allah yay muku albarka gabaki daya, Allah ya tsaremin ku aduk inda kuke yakare min ku" ahankali dagashi har Mu'az dake kwance sukace Ameen sanan yace "saina kira anjima Ummi bye" "bye Son" katse wayan yayi yatashi daga Garden din yawuce cikin hotel din. Dakinsu yabude ya shiga kwance yaganta kan gadon tana bacci hankali kwance ta lulluba da bargo, tray da aka aiko musu abinci kusada gadonta yabi da kallo, tsugunnawa yayi yabude yaga ko kadan bata taba rice dinba sai bowl na fruits wanda yaga gane na fruits ne sabida chunks of pineapples dayagani acikin bowl din da fork kenan shi kawai tasha, maida rice din yay yarufe yatashi yasa hannunshi ahankali yadau kayan shi daya saya a boutique din dake hade da nata yabude bathroom din ya shiga ya maida kofan yarufe, wanka yayi yacire uniform dinshi ya kwashe farin riganshi da jacket dinshi datai hanging abayin yajefa cikin wani dan mini basket sanan yay wankan yadade yana wanka ya gama tsaf ya shirya cikin jean da rigan daya saya da suka mai kyau sosai sanan yafito rikeda basket din, yadau wayanshi, wallet da prescription note din yasaka a aljihu yadau car key yafita, saida yabiya laundry hotel din yabasu uniform din nashi dan su wanke mai sanan yafita ya shiga mota ya kunna wani gidan mai yafara zuwa yasha mai sanan yafito ya shiga gari dudda baiwani san kan gombe sosai ba gaban wani shago ya tsaya dayaga ana dinka hijabi yasai guda daya maroon mai hula da hannu sanan ya koma mota yacigaba da tafiya saida yaga wani babban pharmacy sanan yay parking ya shiga yasa yo duka magunguna ciki harda na wanda zata shafa a inda kuraje ya feso mata da kuma reddish din allergies din sanan yafito ya shiga wani super market another set od cloth yasaima kanshi da takalmi itama yasai mata takalmi sanan yawuce yakoma mota ya ijiye komi sanan ya shiga wani masallaci that is at the road side yay sallan la'asar yafito ya shiga mota yaja awani eatry ya tsaya yaci abinci sanan yaja mota yakoma hotel din, har lokacin tana bacci ajiye komi yayi yadau kayayyakin sawa su yasa a wardrobe din hotel din sanan ya zauna ya cicciro magungunan daya siyo mata yana karanta leaflet dinsu, maganin maleria ne dakuma na allergies din sai multuviate dazai bata apatite yakuma sa taci abinci, aijiyewa yayi yatashi yafita..

49&50

Bayan sallan magrib suka shigo Hotel din tareda Dr din sunadan taba hira, knocking Sameer yayi tana zaune kan gado rike da rice din dazu data kasaci mugun yunwa takeji but dukta yanda taso ta chusa abincin acikin tane takasa sai kallonshi take akan kafafunta knocking da akayi yasa ta dago kanta batare datace komiba dan batada karfin magana bata dade da tashi daga baccin bama, bude kofan Sameer yay ahankali suka hada ido ahankali ta saukar da kanta kasa duk in suka hada ido sai gabanta yafadi juyawa yayi ya kalli Dr yace "come in" shigowa Dr yayi yana kallon Rahima yace "iyye patient ke kadai wanan delicacy din ba tayi?" dan murmushi tayi batare data dago kantaba yakaraso gaban gadon yace "to kishi abincin mana" girgixa mai kai tayi tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata ahankali tace "nakasa ci" cikeda damuwa Dr yace "ahh sorry bakida apatite ne, don't worry tunda yanzu kin tashi akwai magun gunan dazaki sha zaki sami apatite nan da zuwa gobe zaki warke ok, mezakici yanzu?" murya chan kasa kaman wata marainiya tace "sliced fruits" dan juyowa Dr yayi ya kalli Sameer dayay kaman baya jinsu yace "call the kitchen officer akawo mata fruits, she can't take those drugs on empty belly" landline Sameer yadauka ya shiga kiran su shikuma Dr yajuyo ya kalleta yace "ban hannunki ruwan yakare nacire miki" mikamai hannun tayi ahankali yacire mata sanan ya shiga dubata temperature ta yasauka sosai ba kaman dazu ba, knocking akayi Sameer yabada izinin shigowa fruits din aka kawo mata acikin wani bowl da aka daura akan tray aka rufe takawo har gaban Sameer da hannu yanuna mata Rahima takaimata tareda mata sannu da jiki ganin batada lpy sanan tajuya tafita Dr yace "farasha" farasha tayi ahankali shikuma Dr yajuya yaje wurin Sameer ya karbi magungunan sanan ya ballo wanda zatasha yadau bottle water yace "gashi sha" karba tayi gabanta na faduwa watsawa tayi abaki sanan tadau ruwa tasha tana tabe fuska Dr yace "good gurl, shanye fruits din to" cigaba da sha tayi bata wani bata lokaci ba ta shanye tass, Dr ya karbe plate din yadaura kan tray sanan yadau balm din tube din da Sameer yasayo a pharmacy yace "kinga wanan maganin kije kiyi wanka sanan ki shafe duka jikin ki dashi duk wanan kujeren da kaikayi da tashi da tsigan jikin ki keyi zai dena saikizo kiyi bacci, in sha Allah nan da gobe da safe kin warke tatas saidai cigaba da shan maganin harsai kin shanye dan ba'a wasa da maleria dose", gyadamai kai tayi yajuya yahada kayan shi ya kalli Sameer yace "to officer saikuma idan nazo dasafe inhar babu wani matsala da safen shikenan nagama da ita saidai kuma tacigaba dashan drugs dinta" tashi Sameer yayi suka fita daga dakin tare.
Chapter 63 · 0% Book details