← Book details Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 54

Sashe 8

Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

It's was a long journey though, stressful and very hectic, don hanyar tasu ba irin na turkey bane,titin bai yi smooth ba, akwai gargada but thanks to Allah and the driver too don yayi kokari, I really enjoyed the journey because haka na zauna ko bacci na ka sayi ina murnar yau gani a Nigeria, ba zan dena tambayar kai na ba *What so special about Nigeria* Da nake murna haka, i can't say but jiki na yana bani cewa akwai wani abu........then, idan mind
ina yana bani cewa akwai dalili to sai dai nace lets keep moving slowly, we will find something great for our selves readers.
*Lets all proceed no time for fun*
1:00pm
Karfe
aya daidai muna bakin gate
in estate
in Gidan Daura....haka kawai gaba na ya yanke ya fa
i, zuciya ta ta soma bugawa ba adadi yayin da tafiya mukeyi ganin taron mutanen ya sanya zuciya ta karaya, har muka iso bakin gate
in gidan Alhaji Mustapha Alkasim Daurawa, kaka na kenan.

Driver ya sauke mu yana nuna mana gidan, bayan ya sauke mana kayan mu, muka shiga shima kuma ya taimaka mana ya shigar mana da akwatinan mu gaban wani rumfa wanda muka ga jama'a maza sun zauna saman kujerar roba, wasu suna alwala za suyi sallah, wasu kuma zuna zazzaune.

Duk da cewa ba a san daga ina muke ba amma an mana iso cikin gida wani sashi mai kyau da tsafta, ni dai Anam na ce dama a Nigeria ma akwai wurare masu kyau kamar kasar waje?....Mun samu waje mun zauna saman cushion muna kallon mutane suna ta kai komo abin su, yayin da wata farar mace bazata wuce sa'ar Ammi ba ta nufo in da muke tana mana murmushi.

Maraba dai sannunku dai,ta kalle ni sai ta rungume ni tsam a jikin ta tana cewa "Anam
in Abhi kenan"
Ammi ma ta gya
a mata kai hawaye na son saukowa tana gogewa a hankali, matar ta
ago kai ta kalle ni sannan ta ce,"Did you know me?

Na gya
a kai ina cewa,"Yea off-cause i know you, Your name is Aunt Salima, Abhi's younger sister, Mummy khausar"
Mummy khausar ta kura min idanuwa tana mamakin yadda na
auko komai na Abhi, tun daga kan kamanni, fuska, salo, ego, kai harta magana, murya ma irin ta Abhi ce....muna a wannan yanayin ne sai ga wata tsohuwa ta fito tana cewa,"Wasu baki ne wai ake cewa anyi daga
asar waje, ina suke naji gida ya
auka da cewa iyalan Sulaiman sun zo..........turus tayi ta tsaya tana kare mana kallo ni da Ammi, duk dama ta hango tsantsar kamannin da nake yi da Sulaiman
in ta, mamaki bai hanata sake tambayar
ar ta tana cewa,"Shin su waye wa
annan?

Mummy khausar ta gagara magana, saboda tsoron furta cewa mu
in iyalan Abhi ne....Ana haka sai ga Baban Sulaiman ya shigo shima cikin mintuna kalilan
akin ya soma cika, kallon mu kawai ake yi ana ta tambayar daga ina muke ne, kuma wa muke nema?

Tsahon dakika goma
akin ya
au shiru babu mai cewa uffan ganin muma mun sunkuyar da kan mu kasa, muna jiran ko Allah zai sa Abhi ya shigo.....sai Baban Sulaiman ya daka mana tsawa kasancewar sa mutum wanda baya son wasa a al'amura sa, yana sake tambayar wa muke nema.

A wannan lokacin Ammi ta
ago kai idanuwan ta sunyi jazir, ta kalli kowannen su
ayan bayan
aya sannan ta ce, "Baban gida, Baba Huraira, Baban Sulaiman, Inna Mune, Mummy khausar na da
e ina jin labaran ku amma Allah bai sa zan yi tozali da ku ba tsahon shekaru goma sha takwas kenan, sai yau Allah ya kaddamar da cewa zan ganku".

Mun yi tafiya mai nisa, daga
asar Turkiyyah mu kayo tattaki don mu gabatar muku da kan mu a matsayin iyalan Dr Sulaiman Mustapha Daurawa....Ni nice matar sa wanda mahai
fiya ta ta bada amanata ga Sulaiman tun yana jami'a ajin farko, kasancewar she was rest in peace a lokacin sai Abhi ya aure ni saboda maraici na, kuma na amince na aure shi batare da na damu na san iyayan sa ba.....Tafiya ta fara tafiya muna zaman mu lafiya har ya kammala karatun degree
in sa na
aya, kafin ya
aura da master degree, cikin wannan lokacin Allah mahallicci mai bada kyauta a duk sanda ya so, Ya ba mu babban kyauta wato ya a zurta mu da
a macce SA'ADATUL ANAM SULAIMAN DAURAWA.

Ammi na kai wa nan ta dakata, tayi kasa da kanta duk da ma bamu san hukuncin da zai biyo baya ba.

Baban Sulaiman ya ce,"Ga dukkan alamu sun nuna Salima ta san da zaman ku kenan?

Ammi tayi shiru don batayi tsammanin salima ma ta san da zaman suba, sai ranar da ta kira ta a waya, hakan ya sa ta girgiza kai, amma sai Baban Sulaiman ya daka ma Salima tsawa mai firgitarwa
"Dake nake magana, ba ita ba, kin yi min shiru"
Mummy khausar jikin ta har rawa yake yi, muryan ta na rawa ta ce,"Ya sanar da ni bayan sallan nan kafin ya yi tafiya zuwa Turkey"
Baba Huraira kam, tsoki ta ja mai sanya zuciyar yara da jikoki bugawa, da tsoratarwa, yayin da Baban Sulaiman bai iya cewa komai ba, tsabagen takaicin ace yana da rai da lafiyar sa, da mulkin sa amma
an sa bai bashi hakkin sa ba na nema masa aure, ya yi aure a
oye, kuma ma ya haihu yana da
a babba kamar Khausar amma bai ta
a nunawa ba, to wai ma meyasa ya
oye ma duniya cewa yana da iyalai.....maganar sa ta karshe ce ta fito fili.

Mummy khausar ta ce,"Saboda yana tsoron rabuwa da dangin sa, kuma yana tsoron yin nesa da zuri'ar sa kamar yadda ya faru da Asma'u, Yaya Sulaiman ya sha fa
amin cewa, "Da yardar Allah sai ya dawo da Asma'u cikin dangin ta, sai ya nemo
ar uwar sa da aka kora saboda tayi auren bare, despite he knows that shima yana da wannan laifin sai ya
oye nasa, har zuwa lokacin da burin sa zai cika......amma dayake kana naka Allah na nashi, sai Allah ya sauya masa lamarin sa"
Ran Baban gida yayi dubu ya baci, ya ce "Kar wani daga cikin ahalin gidannan ya kula su, har sai zuwa sanda aka gama bincike"......Yana kai wa nan zai fita sai Baba Huraira ta sassauta murya ta ce,"Ranka shi da
e abinci fa, a musu rangwame"
Har ya kai bakin kofa sai yace, "Abinci kawai" yasa kai ya fita ranshi a
ace,
da ka
an da ka
an mutanen
akin suka fara raguwa suna watsewa.

Muna zaune dai a wajan har ma muka dena jin
uriyar mutane kowa damuwan sa ya keyi, sun ma dena shigowa
akin balle ma har su gan mu suyi mana magana ko muyi musu magana.

Daga baya kuma Mummy khausar ce tazo ta
auke mu, muka bi bayan ta ta kai mu cen karshen gida da
an nisa da inda mutanen cikin gidan suke rayuwa, wasu
aku na ne tamkar boys quarters ajere guda shidda, guda
aya aka bu
e,kaman ma akan fi shekara ba shiga
akunan ba, duk kura da yana.....Baban Sulaiman na tsaye yana hararan Mummy Khausar ganin ta nemi gu ta zauna, hakan yasa ta tashi sumu sumu ta bar wajan.....ya tako kafa ya ce mana,"Ku gyara
akin da kan ku" yana kai wa nan ya bar wajan.

Duk
an aikin dake gidan babu wanda yazo ya taya mu haka muka shiga cikin kurar nan, muna tari muna sneezing, mun galabaita kafin mu gama gyara
akin.....Doguwar kujera ce, sai 10inch bed mai kyau, da mini rug a tsakar
akin akwai 52inch LG T.V strong, duk dama kallo bai dame mu ba in ba a laptop ba, sai toilet da ke cen karshen
akin babban toilet ne har wanki zakayi a ciki ma akwai washing machine da sauran su.

Zama mukayi muna mamakin yadda muka tsinci kan mu ranar farko a Nigeria, da gatan mu bawai bamu da gata ba......

Haka nan muka tashi muka yi alwala muka jero sallolin mu, muna cikin Sallah sai muka ga an kawo mana cololin abinci har guda uku....wacce ta kawo yarinya ce kamar ni ta kalli Ammi ta tsugunna har kasa ta gaishe ta cikin girmamawa.

Ni kuma ta kalle ni tai min murmushi, ni ma kuma na bita da kwatan kwacin murmushin da tayi min, ta ce, "Nice to meet you sister, am khausar"
"Parrot"
Mu kayi saurin waigawa, Mummy khausar ce, tana mata rankwashi a kai, ta cigaba da cewa,"Abinci kawai aka ce ki kawo ba wai ki zauna kina surutu ba" common ta shi kada Inna ta zo ta kama ki, kin san ba zaki ji da da
i ba.

Tana fa
ar hakan, Khausar ta mike tana zumbure baki tana sosa kai alamar taji zafin rankwashin, ta juya ta kalle ni ta ce,"Sis zamu ha
e kinji"
Ni kam dariya tabani ina da
a kwa
aituwa na kara sanin wasu daga cikin
an uwa na don wallahi naji da
in yadda Khausar ta kar
e ni.

Na dawo da kallo na zuwa ga Mummy khausar ta ce,"Zan so na
an muku bayani ko ince dalilin da yasa na kira ku a waya nace ku zo Nigeria.

Alkalamin Diela
AL'ADARMU
Page 07
FADILA IBRAHIM
Mummy Khausar tayi having deep breath sannan, ta kalle mu cikin kulawa ta ce,"Hakika zaman ku a cikin gidan nan zai zame muku cikin kunci da tsangwama, zan so ace kun koma turkey don ku sama wa kanku salama, saboda a yanzu haka babu mai sauraron ku a gidan nan....kowa haushin abin da Abhi ya aikata yake ji.

Ammi ta ce,"Where's Abhi?
Chapter 8 · 0% Book details