← Book details Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 54

Sashe 16

Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Successful aka fito da shi, aka kai shi VIP ward, ana bashi kulawa yadda ya kamata....bai farfa
o ba tsahon kwanaki.

Aiman ne ke kwana da shi, yana matukar jin sa tamkar mahaifin sa, yana kula da shi sosai, baya matsawa daga gefen sa, sai idan lokacin sallah yayi, masallacin Avenue
in yana nesa da su anan ciki yake alwalan sa yayi sallan sa, dama ya taho da alkur'anin sa, yana yawaita karatun alkur'ani.

Nigeria
Daura, Katsina state
4weeks later
Na fara zuwa aiki gidan
an yarbawan nan na tsahon sati hu
u babu ruwa na da shiga damuwan
an gidan, duk da na gano cewa Hamdalat Gaddafi ce ka
ai a gidan, Mijin ta Allah yayi masa rasuwa, sai
an ta
aya a duniya.
*Sharafaddeen Gaddafi*
Sharafaddeen, Saurayi mai aji, matashin saurayin ya kai akalla talatin da
ori, ya ta
a aure in da ya auri ka
bilar Ibira daga garin Kogi state, rashin kamun kanta da natsuwarta shi ya hanata zaman gidan sa, har suka rabu ta koma garin su.

Mutum ne wanda baya son hayaniya ko ka
an, bai cika magana ba balle ma kaji sautin maganar sa......tun daga ranar da ya biyo ni kitchen
innan ranar farko har yau ban sake ha
uwa da shi ba.

Turkey
Istiklal Hospital
3month later
Abhi ya na ta samun sauki, cikin kankanin lokaci, Abhi yayi waya har Nigeria, Abuja,Ba tare da da sanin AIMAN ba Abhi ya nema masa aiki a
aya daga cikin kotun dake Abuja wato *Supreme Court Abuja*
Ana jira ya kawo Cv
in sa ne kawai a yi masa Interview.

Aiman da shi da
ayan likitan suka koma Nigeria akan ida ya gama zai dawo Turkey....sun bar Abhi saboda likitoci suna kula da shi yadda ya kamata.

Da sallama ya shiga gidan su mai kofar buhu, ya samu Inna tana ta daka gumbar gero, tana yi tana waka abin ta, ya nufi wajan kai tsaye yana mata amshi.

Ba zato babu tsammani Inna ta ga mutum ai sai tsoro ya kamata ai kawai ta sa ihu tayi cikin
aki tana sumbatun kiran sunan Umma,"Aaaa-Saaaa- Maaaaa- Uuuuuuuuu ki tahoooo gizooo yake min Aimanuuu.

Umma wacce take cikon kewaye, jin Inna ta razana, alamar wani abu ya tsorata, ta hakan yasa tayi saurin fitowa tana gyara zanin jikin ta tana cewa,"Aimanu kuma, a ina kika gano min shi"..........Tayi tozali da Aiman tsaye cikin shiga ta kamala, ya kara kyau duka duka watan su
aya amma sai taga yayi kiba yayi haske yayi kyau kamar ba Aiman
in ta ba.

Inna kam sai ta kama zage zage ganin ashe Aiman
inne da gaske, daga bisani kuma ta nufo inda yake tana cewa,"Aimanu na ina jallabiyar dakayi min alkawari"
Aiman ya sheke da dariya, yayin da yake wanke hannayen sa yana kokarin cin tuwon jar dawa, ha
e da miyar karkashi mai wake a ciki wanda kamshin daddawa dana Man shanu ne ke ta mishi welcome tun ma kafin ya sa tuwon a bakin sa.........Ya dubi Inna yace,"Inna bari na gama cin Tuwon duk zan ba ma kowa tsarabar shi"
Inna kam barin abin da take yi tayi, tayo wajan Aiman, ta zauna tana kare masa kallo, yana cin tuwo cen tace,"Aiman man bleaching ka fara shafawa ne??

Mamaki yasa Umma juyowa adai dai lokacin da take matse mishi ruwan rake a karamin injin
in matse ruwan rake na gargajiya, tasani Aiman na matukar son ruwan rake, ta kirawo yaro ta bashi naira hamsin tace ya ruga ya siyo mata ruwan kankara na hamsin a gidan masu sai da kankara....yaran ko ya falfala a guje........Umm ta kalli Inna ta girgiza kai, ta kalli Aiman sai tayi murmushi sosai bata kula Inna ba don ta sani idan ta kula ta zata ja ma kanta abin magana.

Hakan yasa tayi gum da bakin ta suna ta magana da Aiman na dariya tayi dariya na shiru tayi shiru, idan tayi dariya sai Inna ta kalle ta ta ce,"Munafuka, har yanzu dai halin kin na nan na munafurci, to kisa baki a ayi dake mana, sai wani dariyar munafunfun kike yi"
Ai tuni Umma da Aiman suka sake kwashewa da wata dariyar adai dai lokacin da yaron ya kawo Kankarar, Umma ta kar
a ta sanya su a cikin kulan ruwan sanyin ta, sannan ta fasa
aya ta sanya mishi cikin ruwan raken ta mika mishi ya sha ya kar
a yana cewa,"Na gode kwarai Umma na" Allah ya bani ikon kula dake wata rana kamar yadda kike kula dani nima"
Umma ta shafa kan shi, tana murmushi ta ce, "Ameen Aiman
ina"
Ranar raba dare yayi yana baiwa Umma labarin
asar Turkiyyah, cewar mutanen basu da damuwa suna da kirki sosai, suna da addini, abin birgewan ma shine suna da karamci......Yayi deep breath a daidai lokacin da ya tuna da kyakkyawar surar da yayi tozali da ita a babban hoton dake manne jijin bangon corridor
in shiga
akin Abhi.....A hankali ya furta *Anam*.....ya furta sunan a dai dai lokacin da ya ta
a fuskar Umman sa wacce take kwance saman kafafuwan sa tayi matashi da cinyar
an na ta.

Ya tuna wasu shekarun baya da suka shu
e lokacin yana makaranta, sam bai yarda yayo budurwa ba, ya tuna yawan
an matan da suke bibiyar rayuwar sa, kasancewar sa Gifted a school....right from his secondary school zuwa institution, Wato jami'ar ABU, School of Law.

Ya rasa ya akayi zuciyar sa ta yi saurin amincewa da yarinyar da bai ta
a yin tozali da ita ba, bai ta
a zaton soyayyah haka take shiga jikin
an adam ba, shikam bai ta
a kwatanta son wata
a mace a duniyar nan tamu ba tun bayan shigan shi boko da islamiyyah.

Ya girgiza kai yana cewa wata kila ma soyayyar jini ne, saboda Anam jinin sa ce kuma dole yaji son
an uwan taka a tsakanin su.....gyara ma Umma kwaciya yayi saboda a
akin Umma ne, sai shi kuma ya haye saman gadon ta dama wani lokaci yakan shigo ya kwana saman gadon shillon ta......Juyi yayi tayi bacci ya gagari idanuwan sa, ya sauko saman shimfi
in Umma ya kwanta a gefen ta, tuni bacci
arawo ya sace shi yana baccin sa peacefully ko minshari/gwarti babu.

Washe gari daya tashi cikin shiri da karfe shidda da rabi ma ya samu mota, tuni don yana bukatar ya isa Interview
in da wuri, Da misalin bakwai da rabi ya isa Abuja ya tari taxi aka kai shi *Supreme court Abuja*
Kai tsaye kiran lambar da Abhi ya basa yayi, Mutumin yayi directing
in sa zuwa offishin da ake jarabawar neman aiki.

Ya shiga, ya tarar da mutane guda hu
u shine na biyar, ya zauna a kujerar da suke zaune layi guda.....ba da jimawa ba aka kirawo sa cikin offishin.

Maza biyu ne sai macce
aya zaune saman kujera tare da dogon teburi da kuma abubuwan rubutu a gaban su....Na farko dai kallon ban za sukayi ma Aiman, sannan suka bashi wajan zaman....daga bisani kuma suka fara jero masa tambayoyin da suna tsammanin Aiman ba zai iya amsa koda guda
aya ba....damiwan su shine ya kasa amsawa su kuma su sallame shi don dama suna jin haushin yadda ogam su yake ta ririta Aiman
in wai dole ma su bashi aiki.

Fadila Ibrahim
Comment, Vote and Share
AL'ADARMU
Page 12
Da mamakin su kuwa, a daidai lokacin da ogan na su ya shigo, Aiman ya soma ansa duk wata tamaya da sukayi masa daki bayan daki, har da karin bayani akan abin da basu tamabaya ba......ya kure musu lissafin kwalkwalwar su, yayin da Ogan ya rungume Aiman yana cewa, Graduate from ABU right?

Aiman ya ce,"Yes sir"
Ogan ya sake cewa,"Sulaiman Yusuf Zaria wanda yazo na biyu a gasar ilimi ta Nigeria baki
aya, ko ba kai bane????

Aiman ya ce,"Am the one sir"
"I knew it was you, na san akwai ranar da zan ha
u da kai, na ta
a jin speech
in ka a time
in da kuke defence a school"
Aiman ya ce,"Kwarai kuwa, amma tun bayan lokacin dana gama school of Law Zaria, ina ta kokarin neman aiki amma ban samu ba, sai yanzu Allah ya bani nasaran zuwa Supreme court.......Aiman ya tsagaita jin maganganu sun yi yawa daga wajan lauyoyin da suke hall
in Interview
Mutumin ya na cewa, "Kaga matsalar Nigeria kenan, ya kamata yanda aka baka Scholarship right from secondary school, bai kamata da ka gama karatu shuwagabannin mu su juya maka baya ba" cewar mutumin......Ya cigaba da cewa saboda kune leaders of tomorrow"
Aiman yayi murmushi yana sosa keya, don tabbas lokacin da ya gama school baya mantawa sunan shi GIFTED tsananin kwakwalwar da Allah yayi masa, da baiwar karatu da Allah ya bashi lecturers ma neman sa sukeyi yana musu solving
in problem
in su.....tabbas Scholarship aka basa tun secondary school har jami'a.....saboda wata gasa da yaci tun yana primary....amma baiyi tsammanin duniya ta sanshi haka ba....ya tsugunna yayi sujuda ga Allah sarkin da baya bacci, ya gode ma Allah...sannan ya koma wajan ogan yana jiran yaji feedback
in manyan lauyoyin dake wajan.

DAURA, KATSINA
Da karfin da Allah ya bashi ya yi saurin sanya hannayen sa biyu ya kamo nawa hannayen ha
e da kulle idanuwan sa adaidai lokacin daya ke gode ma ubangijin sa, cikin yaren su na yarbanci....yana da
a leken tiles
in don tabbas da ya barni na fa
i kasan tiles ba karamin buguwa zanyi ba......Ni kai na ina kara juyawa ne ina leken wajan, a lokacin kuma na tuna irin karfin daya saka ya kamo ni ba tareda bata lokaci ba, wanda ya cece ni daga sulewan danayi niyan yi.....idanuwa na suka sauka cikin nashi with out thinking otherwise na sakankance wajan kallon da yake min.....tsahon mintuna goma sha kafin nayi saurin motsa jiki na ina kokarin kwacewa daga ainahin rikon da yayi min.

Da kyar *Sharafaddeen* Ya iya sakin ta, ya jima yana kare mata kallo kafin ya fita kai tsaye sashin mahaifiyar sa ya nufa yana mai kwala kiran sunan ta wato *Momma"
"Momma"
"Momma where are you?
Chapter 16 · 0% Book details