← Book details Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 54

Sashe 1

Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Default Paragraph Font
Normal Table
No List
AL'ADARMU
_STORY, WRITTEN & EDITING BY_
FADILA IBRAHIM{DielaIbrahim}
PUBLISHED 2023-2024
_GARGA
BAN YADDA WANI/WATA YA CANJA WA MARUBUCIYA AKALAR LABARI BA,KO DA KUWA AMFANI DA LABARIN A WANI WAJEN DA BA DA IZININ MARUBUCIYA BA, ZAI FUSKANCI HUKUNCI BABBA.
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
_Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al
alaminmu
ancinmu._
https://www.facebook.com/106494781436168/
*AL'ADARMU*
Page 01
Bismillahir rahmanir rahim
(DA SUNAN ALLAH, MAI RAHAMA, MAI JIN KAI)
_____________________________________
ASAR HAUSA
DAURA
AL'ADARMU, al'ada ta kasance cikakkiyar hanyar rayuwar mutane a karkashin yaran su da maban ban ta al'adu, addinin su, muhallin su da kuma zamantakewar su.

Al'ada dai na da matukar muhimmanci musamman ma a cikin yaren mutane, ko wanne yare yana da na shi al'adan da kuma banbanci tsakanin wani yare da wani yaren, a hausan ce al'ada na nufin abin da aka gada daga kaka da kakanni.

Al"ummar hausa dai, al'umma ce dake zaune a arewa maso yammacin tarayyar Najeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. a al'adance mutane ne masu matukar hazaka da baiwa iri da kala ta fannin al'adu da kirkire kirkiren abubuwan al'adu.

DAURA jiha ce ta addini kuma ta taka muhimmiyar rawa a fannin gargajiya a arewacin Najeriya, kirarin da aka fi yima ta shine "Daura ta ABDU tushen hausa"
GIDAN DAURA haka kowa yake kiran gidan mu, mafi akasarin mutanen garin suna mana lakabi da Daurawa saboda zumunci da son
an uwan junan mu, Sunan ya samo asali ne tun daga kan Kaka da Kakanni kuma suka kafa tarihi mai karfi a cikin zuriyar gidan daura wanda tarihin ya jima yana tasiri a zuciyoyin al'ummar dake gidan.

Kakannin mu su suka kafa wannan zuri'ar sa'annan sun ta
a mulkan garin Daura a zamanin baya kafinnan mulkin ya fita daga hannun su, sai suka kafa nasu ahalin da tambarin sunan gidan wato Gidan Daura.

Babban estate ne wanda a kalla ba'a kasari ba ya kunshi gidaje ashirin koma fiye da haka, ban da yawan adadin filayen dake ajiye gefe guda ana noma idan damuna yazo, haka zalika duk wanda zai yi aure a zuri'ar gidan Daura anan ake yanka masa fili a ba shi kyauta shi kuma ya gina da gumin sa.

Alkasim Muhammad Daurawa shi ne Kakan mu na karshe wanda yai mulki a masarautar Daura, kuma daga kan sa mulkin ya fita a hannun sa, ba laifin sa bane amma da yawa ana kawo chechekuche akan cewa da ha
in bakin gwamnati aka fidda gidan mu daga cikin masarauta, Alkasim Muhammad Daurawa matar sa
walli
aya_Murjanatu ta haifi yara uku, Namiji biyu, sai mace
aya.

Murjanatu ta haifi Bishir, Huraira sai Mustapha wato kakana, ma'ana mahaifin Babana shine
anta na uku, daga nan kuma Alkasim wanda ake masa lakabi da *Daurawa* Allah ya wadata shi da dukiya mai tarin yawa, shi ya siya estate
in da muke ciki sa'annan ya ha
a kan family guda har yar sa HURAIRA A estate
in ya basu gida ita da mijin ta kasancewar shi mijin nata
an uwa ne...abu dai a hankali ya fara yawa.....ya kashe ma
an sa ku
i sun yi makaranta boko da islamiyya sun yi jami'a, Bishir na aikin banki, aka ha
a sa aure da
kanwar Maman su(Murjanatu), shi kuma kaka na, Mustapha shi yayi gadon sarauta, duk wani hali na
an sarki da gidan sarki to fa kakana Mustapha ya gada, kasaitaccen mutum ne mai fa
a aji, kuma
aya cikin dubu mai basirar ha
a kan mutane da taimakawa talakawa fa jama'ar sa, tun kuruciya har girman sa, duk da sarautar bata dawo gidan mu ba amma Kakana Mustapha ya fanshe duk wani cin mutunci da butulci da akayi wa mahaifin sa Alkasim Daurawa.....Mustapha ya karanta politics fannin siyasa hakan yasa yai fice yayi suna domin har honourable na garin
aura sai da yayi a wancen lokacin kuma yayi senater a garin katsina sa'annan shima Allah ya dafa masa, Allah ya sa ma hannun sa albarka dukkan abin da zai yi sai Allah ya albarkace shi....duk wani matashi babba da yaro mai neman shiga takara sai ya biyo ta hannun kakana Mustapha kafin ake samu.

Mahaifin su Alkasim Daurawa shi ya kafa Al'ada mai tsauri a gidan Daura wacce har yau har gobe da tsoffin al'adu ake anfani.

Ya sanya doka kuma al'ada mai tsanani akan cewa babu mai auran bare sai na gida daga kan maza har mata, bai yadda wani ko wata jika ya kawo mata miji ko mata daga waje ba idan ba na cikin gida ba.

Wannan Al'ada ko ince doka yayi tsauri amma hakanan kowa yake bin umarnin sa, saboda samar da zaman lafiya a Zuriyar Gidan Daura.

Mutapha
ar sarkin Daura ya aura mai mulki a wannan zamanin, kuma dole aka basa, duk dama Daurawa ya so ya hana auran amma hakanan ya hakura kasancewar matar mutum kabarin sa kuma
ar aminin sa ce babu yanda ya iya....amma tun daga kan Kakana babu wanda ya sake fita waje neman aure.

Bishir ya haifi yara bakwai, maza biyar mata biyu,
Huraira ta haifi yara goma maza shidda mata hu
u, duk suna estate
in mu.

Sai Kakana Mustapha da
ar sarkin
aura mai suna Maimunatu fulanin katsina ce ita, Allah ya azurta su da yara biyu Mahaifi na (Sulaiman) sai kanwar mahaifi na (Salima).

A lokacin da aka haifi mahaifi na, Alkasim Daurawa ya rasu ya bar wasiya mai karfi na kar wanda ya kuskura ya rusa al'adar Gidan Daura, haka suka tafiyar da rayuwar su kamar yana raye....in da Mahaifi na (Sulaiman) ya girma yayi karatu mai zurfi a
asar turkey ya zama kwararran likita sai da yayi shekaru goma sha biyar a
asar turkey kafin ya dawo Najeriya daga nan kuma asibitoci daban daban suka rinka tura masa appointment wannan ya bashi damar zama International doctor, yana zuwa gari daban daban,
asashe daban daban domin yin aikin sa, yayi fice a sako da lungu na garin Daura ko ince garin katsina babu wanda bai san Dr.

Sulaiman Mustapha Daurawa ba.
______________________________________
Istiklal Avenue
TURKEY
aya daga cikin rantsastsun gidajen dage jere a birnin tarayyar turkiye, gidane na alfarma kuma na gani na fa
a, gaban gate
in black color irin trasparent gate
innan mai karafuna dogaye wanda kana iya hango kashi hamsin na dukkan abubuwan dake kunshe a barandar gidan , Sunan mai gidan ne
aro
aro wato DR.SM DAURAWA.

Cikin jerun
akunan hutawa na cikin shiyyar gidan muna zaune ne muna tattauna wa, gaba
ayan mu mun dukufa mun mai da hankali akan abin da mu keyi.

Lallausan hannun Ammi na shi ya dawo dani daga trance
in dana shiga ina kara gyara littafin da nake rubutu akai ina rubuta daidai gwargwadon abin da Ammi take zayyana min akan labarin dangin mahaifi na wanda ban ma san su ba ina kwa
ayin ha
uwa da su, ina son ganin su, ina son sanin dangi na, ina son sanin yadda suke
abi'un su, da al'adar su kamar yadda Ammi ta zayyana min duk da itama bata ta
a ganin su ba, asalima babu wani daga cikin dangin mahaifi na da yasan da zaman mu a turkey.....mu ka
ai muke rayuwar mu, sai Abhi idan yazo duba mu duk bayan sati uku yake zuwa wajan mu.

Alkalamin Diela
Wannan book
in free book ne bana ku
i bane.

AL'ADARMU
Page 02
Copyright
FADILA IBRAHIM
Al'ada ta kasance abu mafi banbantuwa a tsakanin yare daban daban da kabilu daban daban.

Zaria, Kaduna state
4:00pm
Tsugunne take gaban wutan murhu,an
aura tukunyar lamba goma sha biyar, sai dai wutan bata ci dalilin daya sa sai ta heta wutar da maficin kaba wanda aka kera shi da asalin kaba, tana yi tana hura wutan murhun da bakin ta....Da alama itacen ma
anyu ne don ko rabin kamawa ba suyi ba sai uban hayaki wanda tuni ya turnuke gidan ma gaba
aya.....cikin wannan yanayin ne wata macce wacce ta kai saba'in a duniya bakar fata ta fito sanye cikin shiga ta kamala shigar atampha....tayi matukar kama da matar bahaushe...irin wadan
a suka ci zamanin su tun kaka da kakanni.

"Haba Asma'u ki duba yadda ki ka turnuke mana gida da hayaki, ni wallahi bani son haka, ke kullu yaumin idan zakiyi girki bazaki nemo itace masu kyau ba sai ki nemo itacen da zaki ta cutan mu kina samu hawayen dole.....Tayi kwafa cen kuma ta cigaba da cewa,"Ni wallahi bani son irin wannan abu billahillazi haka kawai"
Ta karasa maganar tana neman waje saman tabarmarta wacce kullin take jikin bangon katangar gidan na su, tana mai tsirta yawu
abi'ar ta kenan.

Asma'u dattijuwar mace ce, tana ta damuwan ta har ta samu itacen suka kama da kyar ta taso ta nufi wajan randar ruwan su wan da yake manne cikin kasa ta
iba ta wanke fuskar ta sannan ta kwalkwali ruwan daga bisani ta koma gefen murhun ta zauna tana mai goge fuskar ta wacce tayi ja saboda hasken fatar da take dashi kaman na zabiya ida nuwan ta kuma sun sha hawaye har sun gode ma Allah...tana zaune saman kujera gefen murhun da take sanwa....sai a lokacin ta bu
e baki ta ce,"Inna kiyi hakuri yanayi ne na damuna yanzu itace ba a samun busassu"
Inna ta buga uban tsoki kafin ta cigaba da mulmula daddawar ta tana shanyasu saman buhu wanda ta shimfi
e shi a inuwa jikin wata bishiya....tana cewa "Asma'u don rainin hankali irin naki na gama magana tun
azu sai yanzu kuke amsa min, ko dayake ba laifin ki bane...Allah sarki Yusuf,
a na Yusuf ai wallahi da yana raye da ba zaki rinka min wannan iskan cin ba...sai kawai Inna ta fashe da kuka wai Asma'u ta mata rashin kunya....kuka wiwiwiwiiiiii tsofai tsofai da ita wai Asma'u take ma kuka.

Sanin halin Inna sarai kuma ba yau ta saba hakan ba, shiyasa ko gizau illah kawai ta waiga ta kalle ta, sannan ta bata hakuri ta ce,"
"Kiyi hakuri Inna wallahi ban yi hakan da nufin rashin kunya ba, kawai na kagu naga wutar ta kama ne.........
Chapter 1 · 0% Book details