← Book details Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 54

Sashe 3

Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bana manta Abhi ya kan zo mana da KUKA da KU
EWA har da wani black spices wai Daddawan kalwa...lol, all powdered , ya ce wai Kakan shi ce ta ha
a masa wai ya samu wacce ta iya girki ta rinka sarrafa mi shi, Da fari ni da Ammi duk bama so, amma daga bisani dana kware wajan girki da su har da spices na gargajiya sai ya zamana da duk zuwan Abhi nijeriya sai na sashi ya taho min da su.
abi'u na sun banbanta da halayyan
asar turkiyyah kasancewar ni mace ce wacce bata son hayaniya, mace mai natsuwa da kamala.....idan nace hallayyah ina nufin shigar su.

Wasu daga cikin
an matan kasar suna shigan banza kuma halayyan su kenan, wasu kuma
abi'ar su ce su sanya kananan kaya su fita amma basa harkar ban za.....likewise me ko wacce irin shiga ina yi kuma na fita amma bana halayyan ban za idan ban manta ba ko saurayi bani da shi kuma ban ta
a son wani
a namiji ba tun da Ammi ta haife ni na fara girma ni ban ga namijin da yake burge ni ba a duniyar nan, kawai ni rayuwa ta nake yi babu ne babu ne kawai.

To kunji na muku takaitaccen bayani a kai na.
______________________________________
NIGERIA
DAURA, KATSINA STATE
Gidan daurawa estate
aya daga cikin manya manyan gidajen dake cikin estate
in, gidan *Bishir* wanda ake ma lakabi da *Baban gida* baban kowa da kowa kenan... shine kuma wan Kakana.

Da alama kamar meeting suke kasancewar yadda gidan ya cika da
a da jikoki kai har da tatta
a kunne, kowa yana sha'anin sa, wani babban falon *Baban gida* wanda manya ne ka
ai a ciki.

Kaka na Mustapha wanda ake kira da *Baban Sulaiman* sai Baba Huraira, da Matayen su, sannan sai
an su har da Mahaifi na (Sulaiman) da kanwar sa Salima wanda ita ma tayi aure tana da yara biyu...duk yaran ko ince jikokin suna waje kowa yana damuwan sa.

Baban gida yayi gyaran murya ya ce,"Mu bu
e taro da addu'a"
kowa ya
aga hannu alamar ana addu'a daga bisani suka shafa, Sai Baban gida ya kalli Kaka Mustapha ya ce,"
an uwa bisimillah"
Kaka na wato Baban Sulaiman yayi gyaran murya ya ce,"Assalamu alaikum warahmatullah"
"Wa'alaikumus-salam warahmatullah" duk suka amsa masa sallamar sa.

Ya ce,"Alhamdulillah, muna godiya ga sarki Allah da kara bamu aran rai da aran lokaci har ya kai ga mun zagayo karshen wata muna wani meeting
in batare da mun rasa kowanne daga cikin agalin mu ba"....ya cigaba da cewa,"Nayi mamaki kwarai abin kuma yana cimin tuwo a kwarya wai ace har yanzu Sulaiman ka kasa fito mana da matar da zaka aura, duk cikin
an matan da muke dasu kace basu maka ba, sa'anninka duk sun yi aure gasu nan duk yaran su daga mai shekara ashirin da shida sai me shekaru kasa da haka, dayawa daga cikin yaran ma an aurar da su, amma ka gagara aure Sulaiman idan boko ne ka gama boko, ka gama duk tara ku
in da kake so ka tara ka gina tsararran gida da babu irin sa a estate
innan, har yau babu kowa a ciki, mun maka magana, mun koma mun zuba maka idanu, kullin sai kace mu baka lokaci" shi lokacin har yanzu bai yi ba, To ba ni ka
ai ba har ta sauran uyayen ka sun gaji da wannan
abi'ar taka.

Daga nan kuma Baban gida Ya ce,"Shawaran da zamu yanke Baban sulaiman, dama ga lubabatu kanwar Asma'u,
an Baba huraira,....Lubabatu tun da Anas (
an Baban gida) ya rasu bata sake aure ba tana zaune a gida....me zai hana a ha
a su aure da Sulaiman
Charaf Lubabatu ta ce,"Kuyi hakuri Baba wallahi na tsaida mijin aure, Zakariyyah zan aura (
a ga Baban gida)
Baban gida yayj caraf ya kalli Zakariyyah ya ce,"Wai haka?

Zakariyyah ya gya
a kai, yayin da matar sa *Salima* Kanwar Sulaiman idanuwan ta sukayi ja, za ai mata kishiya kishiyar ma kanwar kawar ta wato Asma'u ce kawar ta, lubabatu kuma kanwar Asma'u.

Baban gida ya cigaba da cewa ko ya kuka gani, kowa yayi na'am tun da Zakariyya da Luba sun aminta da juna, dama a tsarin al'adar nasu basa ma kowa auran dole, abin da yasa sukayi zaman nan saboda
an su da suka rage basuyi aure ba, gashi jikoki suna ta aure, sai suke kokarin suka sun gyara abin tun daga kan manya kada yara yaran jikokin su fara kokarin rushe al'adar tasu.

Baban Sulaiman ya ce,"Sulaiman you are too old for that art, kabar yara yara suyi borin da kakeyi, idan zaka natsu ka je gidan Baban gida ku daidai ta sauran
an matan, kana jina, wallahi idan ka bijire min sai na saba maka, duk cikin ku nan na san kun san hukuncin da muka yanke ma Asma'u, yanzu ko da wasa bata isa ta taka kafar ta ta dawo cikin wannan zuri'ar ba.

Kai ma kuma ina mai tabbatar maka idan ka bijirewa al'adar mu to zan sallama ka Sulaiman, ka duba ka gani ka manyan ta shekara Arba'in da
ori wasa ne?.....tashi ka bani waje.

Sulaiman ya tura baki, ya mike ya tashi yabar falon ranshi a bace, bai san tayaya zai fara sanar dasu cewa shi fa yana da zuri'a
ar sa ma har ta isa aure...bai san ta yaya zai nuna musu cewa Ammi da Anam sun jima a cikin rayuwar sa ba, Ba zai yu ya cigaba da
oye truth
in sa ba is either ko ya fa
a wa
an uwan sa, ko kuma ya
auko su Ammi ya kawo su Nigeria duk abin da zai faru sai dai ya faru....don bai shirya zama da mata biyu ba, yana ganin idan yayi haka ya ci amanar Ammi tun da kullin tana rokon sa da ya kai ta Nigeria, kullin tana fa
a masa ya dena
oye ma iyayan sa cewa yayi aure saboda halin yau da kullin.

Alkalamin Diela
Wannan book
in free book ne bana ku
i bane.

AL'ADARMU
Page 03
Copyright
FADILA IBRAHIM
ASAR HAUSA
Idan kuka ji ance
asar hausa tunanin ku da hankalinku zai baku wata
asa ake magana?

Asalin kasashen hausa wa
an da Bayajiddah ya kafa kuma ake kiran su HAUSA BAKWAI sune Kano,Katsina,DAURA, Gobir,Rano, Garun gabas da ZAZZAU a cikin ta bakwai wa
annan sune
asashen hausa.

Kamar yadda kuka sani a kowacce bikin sallah
asashen hausa suna gabatar da al'adun su bisa yadda addini ya tanadar.

BIKIN SALLAH
Hausawa na cewa "Sallah biki" "
aya rana" ma'ana , Sallah dai wani lokaci ne na biki duk da kasancewar rana
aya ake yin ta a kowacce shekara sau biyu Musulmai, yare daban daban suke gudanar da wannan shagulgulan.

Sallah ibada ce da addinin musulunci ya sunnata, wanda a duk shekara ake yi sau biyu babba da karama...To amma
asar hausa ba ibada ka
ai suke yi ba suna ha
awa har da lamurori na biki, Abubuwa da dama hausawa na gudanar dashi lokacin sallah wanda da yawa mutane sukan
auka kamar addini ne alahali kuwa AL'ADA ce.

Sallar layyah kowa ya sani Addini ya tana
ar da sunna babba ta idan mutum yana da hali to yayi layyah da dabba mai kafa hu
u....idan kayi layyah kayi sadakan nama ga wa
anda basu yi layyah ba.....hakan na da nasaba da abin da yazo a koyarwar islama.

Wannan kenan
Kowani gida suna ta ha
a ha
an zuwa sallar idi wanda ake gabatarwa da karfe 9:00am wato tara na safe, a yayin da Gidan daurawa, ko wani gate na gidajen kakanni da iyaye da kuma
a an fito da motoci domin zuwa cikin gari don aiwatar da Sallar idi a cikin al'umma.

Dr.SM DAURAWA ne zaune saman kujerar mai zaman banza, cikin motar sa yayin da iyayen sa biyu suna kujerar baya, sai Ado driver yan tuka su,
Sautin kira'a ne ke ta faman tashi a cikin motar na *Suratul Mu'uminoon*
sai kuma kamshin turarukan da ya gauraye dana kowannen su.....ringing
in wayar sa ita ta sanya hankalin su ko mawa kan
an nasu wanda duk da bai dame su su san wanda ke kira ba amma ya kamata ya sanya wayar sa a silent saboda su ba mutane bane masu son hayaniya.

Sunan ta ne ya bayyana a kan screen
in wayar tasa *My Anam*, kasa
aukar wayar yayi saboda yana gaban
iyayen sa....har wayar ta tsinke, kafin a sake bugowa sai ya sanya wayar a flight mood daga nan kuma ya fa
a dogon tunani...tun da yake sallah bai ta
a fashin zuwa turkiyyah ba sai wannan karan, ko wacce sallah a cen yake yi sai dai da anyi sallah da kwana
aya yake dawowa Nigeria don yaba ma iyayen sa hakkin su suma....batare da sanin kowa hakan na faruwa ba....amma all of the sudden wannan shekarar abubuwa suna son ta
are masa, duk wani plan da ya ke shiryawa sai yaga baya working, to the extend that abin har yana sasu samun sa
ani da iyalin sa Ammi.....ga iyayen sa sun
age masa ya fito da mata a cikin dangi ya aura if not zasu masa auran dole.
Chapter 3 · 0% Book details