← Book details Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 54

Sashe 33

Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ok Sir"
Ya matso daf da ita a hankali ya ce,"Anam bu
e idanuwan ki ganni zanyi tafiya ne and ban san ranar da zan dawo ba"
Numfashin sane yake gogan numfashi na,da sauri na bu
e ido na, na ce,"To sai me idan za kayi tafiya ne, bayan ko kana garin ma you don't border to see me"....na fa
a ina folding hannaye na na juya gefe guda, ya sake dawowa ta ina da nake ya ce,"Am sorry for every mistake Gimbiya ta" ya fa
a yana kama kunnen sa
aya. ya cigaba da cewa "Idan fa baki saki ranki ba, zan dasa tafiyar nan Anam, haka zan yini ina bauta miki duk in da zaki ina biye da ke har da ma bayan gida"
Kalmar karshe ce ta sanya ni dariya wai har da bayan gida, wanda nayi dariyar har na gode Allah....daga bisani na tokare shi da kafa wanda shatin takalmi na sai da ya fito a kadin gugan bakin wandon sa, Na ce,"Look it's a stain" na fa
a fuska ta da walwala, sai nace,"Duk sanda ka kalli shatin takalmi na na san zaka tuna silly things
ina" na fa
a ina hura baki nayi gaba ina masa dariya.

Biyo ni yayi yana baya na, ban juya ba naji ya ce,"Anam ina sonki so mara misaltuwa" Dakatawa nayi jin kakmar da na jima ina muradin ta fito daga bakin sa, amma sai dai kuma na gagara juyawa balle ma na kalle sa, karar motar da naji sai nayi saurin juyawa, tuni ya bar ni a tsaye ya koma cikin mota ya kunna horn yayi min ha
e da dallaro min hasken fitilar motar duk da gari yayi haske amma na san da ni yake, murmushi na saki ina kallon sa yazo daf in da nake ya bu
e motar ya ce,"Shigo na kai ki kofar gida mana"
Ba musu na shiga saboda kalmar so daya fa
a ta sanya jijiyoyin jiki na sun mutu murus, ina bukatar na kulle kai na a
aki nayi ta murna, farin cikin da zuciya ta take ciki yafi na kowani lokaci dana kasance a raye tun haihuwa ta.....Wakar Arash feat helena mai taken:
*Don't, don't be afraid
I'll be by your side leading the way
I'm so lonely broken angel
I'm so lonely listen to my heart
One and only broken angel
Come and save me before i fall apart*
Tafiyar ba mai tsayi bace daga wajan zuwa ainahin gidan Abhi amma silent
in cikin motar da kuma yadda muka natsu muna sauraron taken tafiyar wakar cike da salo mai shauki da da
in sauraro, sai ya kasance har bamu so mu rabu da juna, kamar an zare rai a jikin mu haka muka daskare a lokacin da yayi parking a daidai kofar gidan namu, tsahon mintuna biyar kafin na yunkura na bu
e kofar a hankali na furta,"*Allah ya tsare hanya Yaya Ayman*
Wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar shi ya kura mata idanuwan sa adai dai lokacin da ta fita tana tsaye bakin kofa, ji yake kamar ya fita ya zagaya ya rungumota......amma ya daure ya ha
iye komai, yana jin kiran Abhi na shigowa amma sai da su kayi sallama sannan ya
aga bayan ta rufe kofar ya ce,"Abhi gani fa a kofar gida"
Sannan ya kashe wayar, tuni ta shige gida abin ta don tana son ta gana da Abhi
in ta kafin shima yayi tafiya.....don bata san ona zai je ba.

ZARIA, KADUNA.

Tun safe take zagaye a unguwar da aka kwatan ta mata amma sam bata gane gidan ba.....Tana zaune ne dakalin wani gida wanda yake da kofar buhu, ta buga uban tsaki tana cewa,"Tun safe mutum yana abu
aya kam, to wai kaf layin nan banga gidan daya kamata ace nan cibiyar Gifted ba, layi gidajen laka, babu tsayayyen kofa habaaaaaa ina ga
atan kai nayi bari dai na sake tambaya na karshe kafin na bar layin" maganar ta a fili take yi ita ka
ai abin ta.

Tan hango wani yaro n tafiya a galabaice ta
aga hannu tana kiran yaron don gaba
aya ta gaji, "Yaro don Allah ya ka nan"
"Gani" cewar yaron, ta gya
a kai tana da
a tambayar yaron same question da ake bata amsa
aya amma ta gaza kar
ar amsar ta ce,"Yaro ka san wani saurayi anan layin mai suna SULAIMAN, Baki ne baya da haske sosai, kuma yayi makarantar ABU..........

"Kwarai ma kuwa Aiman kike nufi, Sunan Babar sa Umma mai
anwake ko ai ga ki a kofar gidan nasu"
Zuciyar ta ta soma lugude tana sake duba gidan tana da
a tambayar yaron , "Anya nan ne gidan?

"Nan ne mana, kina ta wani tambaya ta, na tafi aika wa Baba ta",Ya tafi ya barta da jimamin, Khausar ta kura wa kofar katakon da taga an rufe tokare kofar da shi, ta bu
e ta shiga, komai na tsakar gidan yana zaune a muhallinsa an share gida tas kamar da mutum a cikin gidan amma sallamar duniya tayi shi shiru da alama babu kowa a ciki.

Ta jima cikin tunani kala kala, taji tsayuwar mota a waje, jim ka
an ta ji hanyaniyar mutane tana tsaye aka shigo gidan ta gansu su biyu suna mamakin yadda suka samu gidan a bu
e, a hankali ta bu
e baki ta ce,"Abhi", "Gifted"
Ai suma mamakin ganin ta su kayi a cikin gidan, su kuma sun biya ta Zaria ne don su
auki muhimmin abu a
akin Aiman wanda ya manta da shi shaf...Sarai Aiman ya gane ta, dakewa yayi ya
aure fuska ya wuce ciki ya bar Khausar da Abhi, Abhi yana ta mamakin abin da take yi a cikin gidan su Umma.

Abhi dama ka san Aiman ne?

Abhi ya gya
a kai yana cewa na sanshi farin sani mana, Aiman ai
an Umma Asma'u ne" abokin aiki nane shiyasa kika ganni cikin gidan su" Khausar ta gya
a kai jin wani ha
i wanda yayi bala'in burge ta, wato ko shiyasa take jin sa a cikin zuciyar ta, ko shiyasa soyayyar shi tayi karfi a cikin jinin jikin ta, lallai kuwa babu abin da zai raba ta da Aiman......ta zurfafa sosai cikin kogin tunani wanda Aiman har ya fito zasu tafi da Abhi, Abhi ya ce," Khausar mutanen gidan basu nan, wa kika zo nema?

Khausar ta rinka washe baki tana nuna Aiman da hannu tana cewa, Abhi ai saurayi na ne fa, na jima bangan shi bane shine na biyo shi gida inga ko yana lafiya"
Aiman ya zare bakin gilashin dake fuskar shi, ya ce,"What!!!!!!!!!!

Kina da hankali kuwa"
Abhi ya ce,"Ya isa hakanan, yanzu kije gida" Khausar ta ce,"Ina bakin aiki ne, zan koma kaduna ne, zaku rage min hanya don dama ban zo da mota ba"
Aiman ya galla mata harara yayi gaba abin sa, yana jin tsanar halayen da khausar
in take dashi na rashin kunya da fitsara......a mota haka ta ringa fa
a ma Abhi yadda ta zo neman sa duk ta fayyace wa ABHI itin son da take ma Aiman....Aiman kuwa gudu ya rinka yi har suka isa Kaduna ya ajiye ta a kawo, duk da Abhi yaso su kara sa da ita magajin gari amma yaki yace akwai cunkoson motoci a gaba zasu canja hanya ne.

Abhi bai ta
a tsintar kansa cikin halin da ya shiga ba, hakika ta yaya zai bawa Anam Aiman, ga kuma Khausar na matukar mura
in auran Aiman
in...da wannan tunanin suka karasa Abuja.

FADILA IBRAHIM
AL'ADARMU
Page 25
Fadila Ibrahim
ABUJA
Da yamma ne misalin karfe hu
u da kwata sun iso tun da rana amma sun wuce wajan masu shedu guda biyu,
ayar kuma mara lafiya ce sai antura musu addereshin asibitin da sunan patient
in.

Suna hanyar dawowa cikin garin Abuja aka tsuge da ruwan sama,kamar da bakin kwarya haka yake sauka a tsakiyar garin Abuja, garin baya rabo da ruwa a
an kwanakin nan, cikin ruwan suka fito suka shiga gidan da Ayman yake, babban gidane mai
auke da flat akallah takwas kowa yana damuwan sa, apartment
in Ayman suka shiga da sauri suna karka
e jikin su duk wani muhimmin takaddu sun aje shi
cikin mota.

Cike da ladabi da girmamawa ya ce,"Abhi ka shiga ka sauya kaya", Abhi ya ce,"No shiga ka gama kawai bari nayi waya da Ammi tukun"
Siririyar sallama ce a bakin sa, ya shiga
akin kai tsaye akwatin sa ya bu
e ya
auko farar jallabiya, bayan ya sauya kayan ne kafin ya cire wando sai ya hango shatin takalmin Anam sai yayi murmushi ya bar wandon bai cire ba, Alwala yayi ya feshe jikin sa da turaren *Black Oud* Ya fito.

Sannan Abhi ya shiga ya sauya shima ya fito su kayi sallah, daga bisani Ayman ya nufi min kitchen
in da yake apartment
in, ba wani jimawa yayi ba cen sai gashi ya fito
auke da transparent mug a hannun sa, kamshin citta da kannunfari ne suke tashi daga cikin kofin hot tea
in, ya mika wa Abhi na sa.

"Thank you Ayman" cewar Abhi, Ayman yayi murmushi ya zauna yana sake kallon shatin takalmin Anam kwance a karin gugan bakin wandon sa,, ya rasa dalilin da yasa ya kasa mantawa da moments
in su na yau, ya kunna tv yana saka news channel daga bisani hira ta
arke tsakanin sa da Abhi kamar uba da
a haka suka koma.

A daren wani abokin aikin sa ya kira sa yana cewa,"Ayman kai fa sai a hankali ka bule whatsapp
inka zaka ga na turo maka hotuna da addireshin asibintin da matar take, har da lambar wayar likitan ma....su kabilar tibi ne kuma dole kuyi taka tsantsan da su, ku san irin yadda zaku yi musu magana, saboda Al'adun su sun ban banta dana hausawa.

Ayman ya gya
a kai ya na cewa,"Thank you Br.Aminu, gobe zan shigo office In Sha Allah"
Daga cikin wayar aka ce,"Okay Allah ya kai mu" suka kashe wayar.

Ayman ya kunna data yana waigawa zai nuna wa Abhi dake aiki a system nasa, ashe har yayi bacci.
Chapter 33 · 0% Book details