← Book details Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 54

Sashe 11

Al'adarmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirun ta yayi yawa, ta wuce
aki kai tsaye sai da ta sha paracetamol sannan ta samu waje ta zauna ta lumshe idanuwan ta tana nazari....a hankali na zo ina matsa mata hannayen ta, na kwanta saman kafa
ar ta nayi shiru.
*Anam*
Ta kirawo sunana, na amsa a hankali ta ce,"Bana son kiga kaman ina tauye miki hakkin ki, Anam na amince da bukatar su ne saboda ina so mu zauna cikin
an uwan Abhi
inki, Kinfi kowa sanin cewa na jima ina so muzo Nigeria, sai gashi a cikin kankanin lokaci munzo kuma bamu isa muce zuwan namu ba alkhairi bane Anam, tun da yanzu muka fara zaman"
Ta tsagaita ta sha ruwa, kafin ta cigaba da cewa, "Na sani idan muka koma Turkiyyah hankalin mu zai kwanta saboda babu hayaniya amma bamu san wani hali Abhi yake ciki ba, kar mu guji zuri'ar sa don baya nan, gwara mu so su tun bamu san ko yana raye ko baya raye ba, Anam zama da su shine zai sa mu koyi juriya da jajircewa akan rayuwa, ba komai bane kake so Allah yake baka, muna da ku
i muna da power ba shi zai sa mu tafi mu bar su ba, Anam muna da ilimi mun san abin da muke yi, tsangwama ba shi zai sa mu koma turkey ba.......... ina so muyi hakuri mu zauna da su da
i ko wuya Allah na tare damu kinji Anam
ina"
Na gya
a kai sannan nace,"Amma ba shi zai sa suce zasu aura min wanda bana so ba Ammi"....."Shishhhhhhhh"Ammi ta toshe min baki tana cewa ,"Bana son na kara jin wani magana kuma Anam, wai ma yaushe kika girma ne har kikasan wanda zaki aura"
Na zum
ure baki ina buga kafafu, na ce,"Ammi ni babu wanda nake so, kawai ni wannan Al'adar tasu tana bani haushi, wallahi na tsani Al'adar tun da sanadin da ya sanaya Abhi har yayi aure babu wani nashi da yasan da zaman mu sai yanzu.....Ammi ni gwara fa mu koma Turkey saboda muyi rayuwar mu babu takura balle tsangwama.

Ammi ta girgiza kai tana cewa,"Mu zauna for a main time Anam saboda ko zamu ji wani news akan Abhi kinji"
Tashi nayi na koma saman gado ina cewa,"Shikenan sai musa kan mu acikin damuwa da wahalar rayuwa bayan muna da yanda zamuyi maganin abin, zaman mu dasu yana nuna cewa mun amince da duk wata bukata tasu"
Kamar yadda tafiyar mu yana nuna cewa," Munyi give up dasu, ba za mu iya rayuwa tare da su ba, then what if Abhi come back to us, and ya ce mu zo ya kawo mu wajan su"cewar Ammi tana tambayar Anam
Ammi ta cigaba da cewa,"Sai mu sake biyo Abhi kenan mu dawo cikin zuri'ar babu kunya babu tsoro Allah"
Ammi ta cigaba da cewa kuma,"Ni anawa tunanin tun da mun kawo kan mu, to muyi zaman mu har zuwa sanda za a samu labarin Abhi"
ure bakin na kuma yi na kwanta ina mai juya ma Ammi baya, don har ga Allah naji na tsani halayen mutanen gidan.

ZARIA
2 month later
Sunday 2:00pm
Zaune suke saman tabarma, Umma da Aiman suna cin abinci a plate
aya shinkafa da wake mai da yaji da latas, gefe
aya kuma Abhi ne kwance ya jingina kan sa da pillow yana kallon su cikin anashuwa.

Inna kuma ta tisa shi gaba tana ta masa hiran irin tsangwamar da tayi tayi ma Asma'u wato Umma, wai saboda bata da dangi ashe dai
ar dangi ce alokacin Inna na ji da kan ta a matsayin uwar miji fitinanniya.

Abhi tun yana dariyar labaran Inna har Bacci ya
auke sa, Umma ta gyara masa kwanciyar sa, tana masa fiffita saboda kwana biyun nan ana zafi sosai damuna ya fara tafiya.

Aiman ya ce,"Umma kince zaki bani labarin kuma kinyi shiru"
Umma tayi murmushi ta kalli Abhi sai ta tuna da tsohuwar zuma, ta ce "Allah sarki rayuwa kenan"
Shekarun baya.

Mahaifiyar mu ita ce Baba Huraira a cikin zuri'ar Gidan daura, Mahaifina ya rasu tun ina da junior secondary school, Allah ya azurta iyaye na da
a goma, Maza Shidda Mata hu
Nice autan mata, kuma ta tsakiya da haihuwa,yayye na mata duk sun yi aure,ni ka
ai ce nace sai nayi boko,
na kammala secondary school in da nayi boarding school, Dutsinma.....Na dawo gida da niyar zan koma kastina Jami'ar umaru musa
ar adua, nayi karatun Law, sai Allah bai kaddara ba,.

Soyayyah
Tun ina karama Allah ya
aura min son Yaya na wato Sulaiman, Shima kuma yana nuna min kulawa kwatan kwacin yanda nake mishi soyayyah, amma da muka taso muka yi wayo muka girma sai na fahimci AL'ADAR Gidan Daura basa son auran bare, kuma sannan alokacin Yaya Sulaiman zai tafi karatu Turkiyyah, bayan tafiyar sa, na fara karatu a jami'ar katsina Allah cikin ikon sa, sai na ha
u da Baban ka *Yusuf* Prof Yusuf
an asalin Kaduna ne, cikin Garin Zaria, ya jima baiyi aure ba, sai da ya ha
u da ni kuma na amince da soyayyar sa, cikin rashin nuna tsoro na gabatar da shi wa magabata na.

Sai dai kuma abin ya girgiza kowa jin wai na kawo bare a matsayin mijin aure, babu wanda yayi yunkurin hanani auran *Prof Yusuf Zaria* a lokacin, Magabata na sun yadda sun
aura min aure dashi babu abin da ba a mun ba amatsayi na na tsatson Daurawa, sai dai ranar biki, kowa ya watse manya suka taramu ni da Prof Yusuf, suka shaida masa cewa sun cire ni daga cikin zuri'ar su, kar na sake na tako kafata nace nazo ganin gida, ko fuska ko mai kama dani basa son su kara gani balle ma suji labari na.

Hakika na razana, saboda ban ta
a ganin
anyen hukunci irin wannan ba kuma babu wanda aka fara yi ma irin wannan hukuncin sai ni ka
ai... shiyasa na razana matuka, Yaya Sulaiman yana Turkey na kira sa na sanar da shi duk abin da ya faru, wauta ta daya gani ban sanar da shi ba sai da komai ya ta
are, shima kuma a wannan lokacin yace min yana shirin yin aure ne amma baya son kowa ya sani na rike masa sirrin sa, sannan kar na damu nabi mijina In Sha Allah ko bajima ko ba da
i watarana sai ya nemo ni ya dawi dani cikin zuri'ar mu.

Katsina muka fara zama wata na
aya na samu cikin ka, na sha wahala ba uwa, ba
an uwa sai Inna da da
i da ba da
i haka ta zauna min dana haihu har nayi arba'in, daga baya muka koma Zamfara, mun
au shekaru da yawa a Zamfara kafin muka dawo Zaria... daga nan kuma Allah ya
au ran mahaifin ka ya tafi ya bar mu cikin duniyar da babu komai cikin ta sai tashin hankali.....Aiman kasan irin wahalan da muka sha ai a rayuwa bayan rasuwan mahaifinka wanda har yanzu muna cikin ta ma.

"Uhmmmm kuma In Sha Allah, Allah zai yaye muku wahalhalun naku" Cewar Abhi daya farka yana musu murmushi yace ,"Wai nikam baki cigaba da karatun bane?

"Umma ta ce, ai dama Baban kowa ne ya nema min admission
in, to bayan nayi aure sai suka kore ni daga zuri'ar sannan suka sa Jami'ar tayi withdrawing
ina....kaji silar lalacewar karatu na.

Abhi ya girgiza kai ya matukar tausaya ma halin da Umma ta shiga.

Umma ta ce,"Ina iyalan ka Yaya"
Abhi ya ce,"Suna Turkey Umma, idan na warke zan koma turkey na taho da su nan, sannan sai mu ha
u gaba
ayan mu har da ku mu koma Daura, wannan karan ko suna so ko basa so, sai sun sassauta mana hukuncin da suka
auka akan riko da AL'ADUN MU na Gidan Daura.

Wato AL'ADAR Gidan Daura na rashin auran bare yana bai mamaki, wannan al'ada asalin ta mutanen Fulfu
e wato fulani su aka sani da auran dangi, na rasa ta yaya akayi Gidan Daura suka ara suka yafa wannan AL'ADA kuma ta zauna daram a cikin zuciyoyin mu......wanda har gobe da ita ake koyi" Abhi ya cigaba da cewa "Hakika zan so a ce na rushe duk wata Al'ada ta rashin auren bare a zuri'ar mu, kuma ina gab da aiwatar da hakan matukar Allah mai kowa da komai ya bani nisan rai da aran lokaci to babu abin da zai hanani aiwatar da hakan"
Umma ta ce,"Wannan yakin daka
auko yaya ba karamin yaki bane, wato har na fara jin tsoron tunkarar Daura, saboda na sani ba lallai su amince da sabon AL'ADAR da zamu zo musu da ita ba"
"Ko su amince ko kar su amince zamu koma cikin zuri'ar mu kuma basu isa su kore mu ba, don ko sun kore mu ma, babu in da zamu je" Allah dai ya bani lafiya"
"Ameen ya rabbi" Aiman ya amsa.

Inna kam tana cen gefen bishiya tana matsar daddawar ta, ran ta wasai babu abin da ya shafe ta.

DAURA
9:00am
Na fito cikin shirina tsab cikin shiga ta ta ainahin mutanen kasar waje idan sanyi ya zo da snow sai su sanya jeans, doguwar rigar sanyi iya gwiwa, na sanya hulan sanyi na rufe gashi na, sannan na sanya white boot
ina mai sheki da adon barbie a jiki...na yi rolling da wani pink veil.

Khausar na gani na ta zare idanu tana cewa,"Wannan shigar fa Anam?
Chapter 11 · 0% Book details