← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 83

Sashe 9

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta na Bude data sakonni suka yi ta Tururuwan shigowa, Sai da ta bari suka gama shigowa sannan sai taga ma agent din yaron shagon ma ya yi mata mgana sai ta Bude ta na gani.
Vioce ta yi masa bayan ta ga hoton kayan da daukan mata, akwai sauran kudin da zata tura musu, sai da ta gama duba komai taga sun yi, sannan ta sauka ta tura musu Ragowan kudin, ta dauki Trancsation din ta Tura masa tare da lambar wacce za'a aika ma kayan Tunda su za su ba da akai tasha a saka a motar jigawa.

Ta na ganin ta gama da wannan bangaran, sai ta fara duba Sakonin mutane ta na ba su amsa bata ma gama ba, ta tafi kallon Status din Sauran mutanenta.
Har ta wuce Status din Khairiya Ahmad, sai ta dawo saboda ta na saida y'an kunnaye ma su kyau ta na so ta siyan ma yara, sai ta shiga ta fara Dubawa, ta santa tunda suna harkan kasuwanci tare ba su dai tab'a ganin juna ido da ido ba sai a hoto.
Ta dai san kamar Khairiya ta tab'a Fad'a mata ita yar zariya ce.
Kamar wasa ta na gama ganin Hotunan y'an kunnen sai tayi Tagging din na karshen ta yi mgana.

"Salam Khairiya wannan akwai na yara irin shi?

Sai kuma ta kara da cewa"Au bamu gaisa ba ina kwana ya kasuwa?

Sai ta fita ganin kamar ta na Online ammh kuma kamar ba ta kusa da wayar.

Ijiye wayar ta yi itama ta je kitchen domin ta saka ruwan zafi ta na dafa Indomie ne, yau yaran da megidan Plantai suka ci da Tea ita kuma ba ta cika son plantain ba.
Sai da ta gama Dahuwarta ta dafa kwai sannan ta Zubo a filet ta fito da shi falo ta ijiye saman Center table din da ke falon.
Wayarta ta dauka sannan ta fara cin abinci, ta na ci ta na duba wayarta, Khairiya ba ta duba sakonta ba sai tayi tunanin kila har yanzu ba ta zo kusa da wayar ba.
Sai ta koma Bangaran Status sai kuma taga sunan khairiya alamun ta kara saka wani Status  har ta wuceta sai kuma ta dawo ganin kamar Hoto taga ta saka, sai ta dawo ta Bud'e.
Abunda ta gani ne yasa sai da  cokalin hannunta ya subuce ya fad'i kasa.
Da sauri ta mike jikinta na rawa har ta barin Ruwan da ke karamin kofin Tangaran a gefenta.
Cikin Firgici da rawan baki tace

"SADIQ."

Hannunta na rawa ta kara Zooming din Hoton domin ta kara tabbatar ma da Idanuwanta shin abunda ta gani gaskiya ne?
Sadiq ne ta ke gani tare da wata mace da ciki, sannan a yanayin Hoton cikin Halin da mata miji ko farka kan kasance ne a ciki.
Saboda Tsabar Rud'ewa ta manta da Duba abunda Khairiya ta saka a kasan Hoton sai da ta dauki Hoton ta koma kan wayarta ta kara Duba shi da kyau.
Tabbas wannan Sadiq ne to Sadiq din ne bata sani ba Allah na Tuba ko cikin Duba sai ta iya Cire kanin na su.
Zama ta koma ta yi Saboda jin wani jiri na Dibanta.
Da Rawam jiki ta kara komawa ta Duba Status din khairiya sai alokacin taga abunda ta saka a kasan Hoton.

"Jama'a See Love don Allah? Mu ma Allah ya aurar da mu"

Tare da saka Emojin kunya da Love.
Saddiqa sai ta kasa ma wani Tunani, kada ta ce ba ta da tabbacin ba Sadiq ta gani ba domin shi ne ta gani a wannan Hoton tare da wata?
To in shi ne ta jikin Hoton wacece?
Sai ta kasa ba ma kanta amsa lokacin da wani shashe na zuciyarsa yace"Karuwar sa mana."

Tunda dai mace daya garesa itace Sultana to in dai ba Sultana bace wacece? Kuma a yanayin da suke a tare tabbas in ba mata da miji ba to su farkan juna ne.
Hankali tashe Saddiqa ta lalubo lambar Surayya ta doka mata kira ammh har ta gama ringing bata dauka ba, Sai zuba Zufa ta ke yi lokaci d'aya ta na fad'in"Ki daga mana, ki daga mana Big sis."
Ta ke fad'a ta na faman zagayen falon cikin tashin Hankali.
Kiran da ta yi ma surayya yafi goma ammh bata daga ba, sai ta yi tunanin Tabbas bata kusa da wayar.
Ta rasa wa zata kira, Surayya ce babba kuma kafin umma taji wasu matsalansu ita ke fara ji, kuma ta tayasu warware shi cikin sauki.

Ta yi Tunanin ko kiran Sa'ima ammh kuma sai ta fasa, in kuma ba shi ba ne fa? In har maganar ta fita Sun zubar ma kaninsu kima da Darajarshi da sauran suke gani.
Rashin Daukan wayan Surayya yasa ta kara komawa ta na ta duba Hotunan nan, ta na kara Zooming tuni idanuwanta har sun ciko da kwallah, sai a lokacin ma taga kamar tasan yarinyar jikin Hoton ammh ta rasa inda ta santa.
Sake komawa Chart din ta yi sai taga Khairiya ta sauka daga online da gaggawa ta kirata, kuma ba sa ma kiran juna in ba kasuwanci siyan wani abu ya had'a su ba.
Itama sai da wayar ta kusa katsewa sannan ta dauka.
Bayan sun gaisa Saddiqa tace"Khair na yi miki mgana ta chart baki Duba ba."
Dagachan Bangaren khairiya tace"Sorry na ijiye wayar ne muna mgana da Mama? Lafiya ko wani abu ki ke so ne?
Saddiqa tace"Eh na yi miki mganar wasu y'an kunne ne ko akwai na yaran su?
Khairiya tace"Ok in na duba zan miki mgana, Nagode"
Har khairiya zata sauke Wayar Saddiqa tace"Amh Khairiya ni ko nace ba, hoton da naga kin saka dazu amaren sun yi kyau, sai naga kamar kuna kama ko kanwarki ce? Mijinta ne?
Khairiya tace"Wacce? Wai HASIYA?
ba kanwata ba ce kawar kanwata ce Safiya a wayarta nima naga Hoton sun yi min kyau sai na Tura shi a wayata shine har na yi status da shi Eh mijinta ne."

Saddiqa cikin mamaki tace"Allah sarki! A nan zariyan su ke kenan?
Khairiya tace"Eh anan zariya su ke"
Saddiqa sai ta rasa kuma abunda zata ce, kiran wayarta taji ana yi, ta na Dubawa sai taga Surayya ce kiranta da Sauri ta yi ma khairiya sallama.
Ta daga kiran Kiran Surayya.
Wacce ta na dagawa tace"Ke lafiya naga uban kira Rututu?
Saddiqa ta sauke Numfashi kafin tace"Big sis ki zo online zan tura miki wani abu yanzu nan."
Dagachan Bangaran Surayya tace"Miye? Lafiya ki ke kuwa? naji muryanki ta yi kasa ne."
Saddiqa tace"Big sis ki je ki ga abunda ya sakani firgici don Allah"
Jin haka yasa Surayya tace shikenan Hankalinta ya tashi ganin kiran Saddiqan ba adadi.

Da sauri ta Bude data, Daman dazu wayar na daki ne ita kuma suna falo megidanta na karyawa sai da ya gama ta rakasa ya fita aiki shine da ta dawo dakin taga kiran Saddiqa ba adadi.
Ta na bude data ba ta tsaya sauraran kowa ba sai sakon Saddiqa da ta jira ya shigo ta na shiga sai taga Hoto ne.
A kasan Hoton Saddiqa tace"Don Allah Big sis wa ki ka gani cikin Hoton ga?
Sai da ta Bude hoton, irin razanar da Saddiqa ta yi, Surayya ta fita shiga tashin Hankali domin sai da wayar ta subuce daga hannunta ta fad'i saman Cafet Saboda gigita da Dimauta.
Sai da ta kara Dauko wayar ta sake bin Hotin da kallo, ai ba ta bukatar ta yi zooming ko mutuwa ta yi ta dawo zata iya shaida kaninta a cikin Dubban Mutane.
Wannan ai Sadiq ne! Sadiq shinkafi ne kaninsu to shi da waye?
Ita yarinyar ta rika kallo ma, sai ta ke ganin kamar tasan fuskarta cikin jikin yarinyar shi yafi komai jan Hankalinta
Saddiqa na ta turo mata mgana ba ta Dubawa.

"Big sis Sadiq ko? Ko ba shi ba ne?

"In da naga Hoton, tace wai mata da miji ne?
Sadiq na da wata mata ne bayan Sultana?

"Kin yi shuru?

'"ni macen Hoton ne na ke ganin kamar na santa."

Sakon Saddiqa na karshe yasa Surayya ta kara Duba Hoton macen da kyau, Tabbas tasan wannan Fuskar, kuma kamar a gidansu ta taba ganinta, zama ta yi ta na kallon Hoton ta na so ta tuna inda ta taba ganinta Momorig lokacin na Shiga kanta.
Kamar an Tuna mata sai taji ta tuna a da inda ta tab'a ganinta kawar Saliha da ta zo bikin Sultana.

Da Sauri ta kira Saliha tace ta Hau chart zata Tura mata wani Hoto.
Gudun abunda zai je ya dawo sai ta yanke Hoton Sadiq ta Tura mata na Hasiya sai da ta tabbatar ta gani sannan ta  kara kiranta
Ta na Dauka Surayya tace"Saliha kamar kawar nan ta ki ko?
Saliha tace"Kwarai HASIYA ce. Ba ta zo min bikin Sadiq ba? Kin manta wacce na ce muku a kaduna muka had'u yar'uwan mijin Salima ce fa."
Surayya sai jinjina kai ta ke yi cikin Tsananin mamaki kafin tace"Na tuna ta wata tfara haka  har ma kika bani wayarki na yi muku Hoto ko?
Saliha tace"Kwarai ashe baki manta ba, bari na tura miki hoton ki kara gani, anan ta yi kiban fuska ne kila Saboda cikin jikinta ne, ni ban ma san ta na da ciki ba, kwanaki dai da muka yi waya tace min ta yi ta fama da Zazzabi."
Surayya sai ta kasa mgana ji ta yi zufa na keto mata ta saman goshinta, duk da AC Din da ke falon.
Cikin wani yanayi Surayya tace"Da bikin sun had'u da Sadiq ne?
Saliha ta yi shuru kafin tace"Gaskiya bazan iya tunawa ba? Hala me ya faru?
Da Surayya tace"A'a bakomai, wata kawatace naga ta  saka a status sai na ke tunanin inda na taba ganinta."
Da haka ta shanshantar da mganar Saboda kada Saliha ta fahimci wani abu.
Chapter 9 · 0% Book details