← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 83

Sashe 39

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har Hajja kakar Tahir sai da tazo ta Dubashi tare suka zo da Tahir sai yayansa Kasim, nan suka barshi ya kwana su kuma suka koma aranar, Sultana ma wajen sau uku ta zo ta dubashi itama sun fara Jarabawar Neco shiyasa Abba yace ta zauna a gida ta natsu kan jarabawarta.
Da Farko nan aka so a barta wajen Salima tunda mijinta ne ranar da Sadiq ya farfado yaji labari yace ta koma gida shi baya bukatar ta.
Shikenan ta shiga damuwa tana ganin kamar ko tun abunda ya faru ne bai manta ba, shi kuma gani ya yi ina ita ina Jinyarsa ta na mace sannan shi bayason rashin kunya tunda kuma ya lura shi ta koya yanzu.
Har abokansu Jb da Mb sun zo sun Dubashi suka yini kafin su tafi shi dai Shuru kawai ya ke yi baya mgana yana kwance kafafunsa sagale a sama hannanunsa ma yana Sagale sai inda aka juyasa ko wanka ba'a yi masa sai dai ana goge masa jiki bayan kowani kwanaki Biyu.
Yaga kowa ammh bai ga Siya ba, tun washegarin ranar da ya Farfad'o sai da ya yi ma Big sis mganar ina Siya? Saboda lokacin da ya ke kwance yana fama da kansa ita kawai ya ke tunawa har Mafarkin ta haihu ya yi, saboda sanin Halin data ke ciki.
Ita kuma Surayya ta yi ta kiran wayar Hasiya a kashe, kuma ta yi hausan karisawa zariya ta duba ta bai zo mata ba sai da Sadiq ya yi tambayar, tunanin haka ya zo mata alokacin sai aka yi baki abokan Alhaji Jibril tare da su Abba suka shigo tunda ita ta na yawan zuwa duba Sadiq din.
Fitan ta yasa tace ma Auwalu bari taje ta dawo  daga nan ta hau motar Zariya sai gidan Hasiya.
Sai dai Labarin da taje ta iske ya tada mata Hankali bata tab'a tunanin Umma zata iya sa su sajida su zo su aikata irin wannan aikin ba.
Maman suhailat ta samu, abunda yasa ma ta gayamata cewar da tayi ita yayar mijin Hasiya ce, shine Dalilin da yasa Maman suhailat ta kai ta dakinta ta zayyana mata komai.
Da Surayya ta tambayeta yanzu Hasiyar ta na ina? Maman suhailat tace washegarin tafiyata taje gidan yayata ta iske mijinta shi ya gayamata yayar mahaifiyarmu ta rasu mun tafi can garin inda mahaifiyar mu ke zaune.
Kuma yace mata sai bayan an yi kwana bakwai zamu dawo, Hankalin Surayya ya gama tashi ta rasa wata amsa kuma zata baiwa Sadiq in ya kara tambayata Hasiya? Ba ta baro gidan ba sai da ta Rubuta ma maman suhailat lambarta tace da zarar taji Labarin dawowarmu ta kirata ta sanar da ita.
Sai da surayya ta fito zata tafi ne Maman suhailat ta Biyo ta tana tambayata  jikin Abubakar din? Ita kuma tace mata yana ta samun sauki sai hamdala.
Surayya ta koma asibiti cikin Tsananin Damuwa, Allah yasa lokacin da zata yi ma Sadiq sallama su Abba na wajen tare da shi ma za su koma Shiyasa ta samu ta sulale a lokacin har suka isa Gusau ta na mamakin abunda ta aikata ashe kenan Fad'an da akace mallam ya zo ya yi mata bata ji ba tunda tasa a yi ma Hasiya wannan Tozarcin.
Kuma ta yi alkwarin ko a Fuska bazata nuna musu tasan abunda suka aikata ba zata bisu a haka ita damuwar d'aya Sadiq.
Shi kawai take Tunanin hanyar da zata sama masa mafitan da bazai san me ya ke faruwa ba.
Ta kara komawa ganinsa a lokacin ne da ya kara tambayarta ta yi masa karyan ai tazo ta gansa lokacin yana barci saboda nauyin jikinta yasa Abba yace tayi zamanta a gida.
Kallonta kawai ya yi tunda bai cika mgana ba Sosai ammh ta san bai yarda da ita ba, saboda tsaro yasa har Auwalu ta shiryama ko Sadiq ya Tambayesa Wata siya tazo? Yace eh tazo yana barci har Tahir ta gayamawa.
Tahir yace"To tazo din ne? Nima fa ya yi ta tambayana nace ban sani ba."
Surayya sai ta kasa mgana, kawai dai tace su gayamasa tazo ma wajen sau biyu yana barci saboda nauyin jikinta yasa Abba yace ta yi zamanta a gida.
Kamar ta sani dukkansu sai da ya tambayesu suka gayamasa yadda Surayya ta gayamusu.

Tun daganan yasan akwai wani abu, ta yaya yaga kowa sai itace bai gani ba sai ace wai tazo yana barci kaji mganar da Hankali bazai Dauka ba.
A jikinsa yasan akwai abunda ya kamata ya sani bai sani ba, shi damuwarsa d'aya tsohon ciki gareta babu wanda ke tare da ita balle ya taimaketa kuma ba ta da kowa sai shi, hankalinsa ya kan kwanta in ya Tuna tana da yan'uwa a Zariya yasan baza su barta ita kadai ba sai dai kulawarsa ne a matsayinsa na Uban cikin bazata samu ba.
Sai ya rage mgana kwata kwata daga sannu ya jiki shikenan ko Tahir sai ya yini mganarsu bata wuce goma ba.
Kuma abunda ya Fahimta shine ba mai yi masa mganar siya, sannan zuwan Innani ta gayamassa wani kalma in da tace wai bala'i da Annoba ya sauka a gidansa jinin wannan yarinya ba alheri ba ne.
A lokacin bai damu da mganarta ba sai yanzu ya ke auna mgamganunta.
A ransa yasan daman haka zai faru suna zargin duk abunda ya faru da shi Siya itace sila, kuma yana da tabbacin wani abu ya faru wanda ba'a so ya sani to bazai matsa ma kansa sai ya sani ba ammh in ya samu kansa shi zai mike yaje ya gannin ma idanuwansa komai sannan yaji duk abunda ya faru.
Shiyasa ya yi bakam bai kara yi ma kowa mganar Siya ba hankalin Surayya sai ya kwanta a tunaninta in ya samu lafiya sai ta gayamasa ita kuma Umma ta samu natsuwa Tunaninta ya ma manta da ita tunda bata ya yi mganarta ba, ta manta fa matarsa ce dauke da ciki ta ya ya zai manta da ita sai kace wanda ya samu makuwa?
Haka Sadiq ya cigaba da jinya a asibiti har daga ma'aikatansu daga Abuja sun zo dubashi, kuma sun ji dadin ganinsa har yana samun sauki.
Yana da wata d'aya a asibitin aka duba Dorin kuma Alhandulillah duka sun yi kyau, sai aka fara bashi Sanduna guda biyu yana tafiya da su a haraban asibitin Saboda warware kasusuwansa da suka gaji da kwanciya sannan Tuni Rauninka sun fara baki sun dauko warkewa.
Kansa ma an cire bandage ya sabe kumburin gabadaya.

Hannunsa kuma sai dai aka sakamai jakar sagala hannu aciki, kullum yana sanye da gajerun wando saboda Kafarsa, kuma Alhamdulillah kowa yazo yaga Sadiq sai yace ba shi da kyamar jiki ganin cikin Lokaci har ya fara tafiya da taimakon sandunan asibiti. Kuma su kansu likitocin sun ce sun yi mamakin saurin mikewarsa suka yi musu albishir di'n Cewa bazai jima za su sallameshi ya koma gida ya cigaba da kula da kansa.

Auwalu ke Daukan Hotonsa yana Turama yan'uwansa mata suna gani suna jin dadi, Sultana kuma koda yaushe cikin kira waya ta ke yi, in aka basa daga gaisuwa da tambayan ya jiki shikenan ya ke yi mata shuru itama sai ta rasa me zata ce ganin yadda ya yi mata gim da shi, har Umma ta gayamawa ita kuma tace ta yi masa uzuri saboda halin ciwo, ita kuma tana son shi, shiyasa har aranta taji ta tsani Hasiya umma kuma ta bata tabbacin da ita kad'ai Sadiq zai cigaba da zama a matsayin matarsa.
Hatsarin nan da Sadiq ya yi sai ya rage magana kamar ba shi ba, ya koma wani shuru shuru mgana sai in ta zama dole.
Fatansa kawai ya samu saukin da zai iya tafiya yaje ya duba Siya yaga Halin da ta ke ciki, in ya lissafa dai dai cikinta ya fita wata na tara ya shiga goma kuma yasan Edd dinta tun 19 ga watan jiya ne.
Ga shi ba waya a hannunsa da ya yi mganar wayarsa sai aka gayamasa ta lalace ta fashe a had'arin da ya yi, tare da motarsa da bazata gyaru ba saboda yadda in jin Motar ya tashi aiki Abba yace a saidata kawai tunda bazata gyaru ba.
Shi dai bashi da tacewa sai shuru, tunda ana ganin yana kwance ba shi da lafiya in ya matsa da mgana sai kuma ace shi da ba shi da lafiya.
Ammh ya shirya yin abunda rai bazai so ba, matukar ya warke yaga abunda bashi ne ba.
Jinya dai ta yi tsawo kad'an ba da yawa ba, tunda har kusan wata Biyu Sadiq yana asibiti sannan aka sallameshi lokacin yana da wajen kwana sittin da wani abu a gadon asibiti yana jinya.
Direct daga nan sai Gusau gida aka wuce da shi, a kuma bangarensa yace a kaisa tunda Abba ya basa zabin cewa ko gidansa za'a wuce da shi yace a'a a wuce dashi gida.
Kafar ne kawai ta rage hannu kuma ya warke shima sai kad'an da ba'a rasa ba kuma an cire masa wannan Jakar kafar ne ya ke tafiya da taimakon sanda har a lokacin.
Dayake tun a asibitin ana yi masa aski, da ya dawo gida wanka kawai ya yi, sai kuma aske gashi nan da suka taru a jikinsa har kuma Lokacin Auwalu na tare da shi duk Sadiq din yace ya koma gida zai iya kula da kansa ammh yaki yace yana tare dashi har sai ya warke gabadaya.
Chapter 39 · 0% Book details