← Book details Tmw Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 83

Sashe 41

Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi bai yi ta yaran ba sai da ya tambayi likita yanayin jikin matarsa ya tabbatar masa zuwa dare Hasiya zata Farfad'o cikin koshin lafiya.
Sannan ya karbi yaran hannun Tahir sun ci Kayan sanyi na yara masu kyau, Allah yasa Hasiya ta kwashi wasu daga cikin kayan haihuwanta ranar da su Sajida suka koreta suka karbe key din dakin.
Kuma daman wasu kayan akwai biyu biyu wasu kuma daman Both sawar maza daa mata ne.
Tahir na gefe na daukansu Hoto cikin murna yace"Abokina ga jinjina."
Ya fad'a yana sara ma Sadiq shi kuma yana mirmishi tunda bashi da kafa, sai da ya zauna Tahir ya Dora masa yaran a jikinsa.
Kallonsu kawai ya ke yi yana jin wani Farinciki daman haka ake jin in mutun ya zama Uba.
Addu'a ya ke ta tofa musu sannan Tahir ya kama masa dayan ya rike dayan ya yi musu kiran salla duka kunnuwansu kuma ya sanya musu suna batare da ya Furta ma kowa ba.
Aka bar Tahir da fadin"Ashe ashe shiyasa ka dage, ashe akwai rabon yan Biyu zarata kai da yar Zabiyar ka."
Hararansa Sadiq ya yi kafin yace" Sunanta Asiya mallam ba zabiya ba."
Tahir ya kwashe da Dariya yana fadin"To yau kuma sai ta koma Asiya ba Hasiya ba."
Yana jinsa ya yi masa banza, yaran nan sai da Nurses suka zo suka Daukesu suka maida su ciki sannan suka bar hannun Sadiq.
Adda Fati kuma taje gida ta kawo ma Hasiya wasu kaya tare da Ruwan zafi.
Su kuma su Sadiq suka tafi salla domin ba su yi azahar da la'asar ba har Biyar na yammah ya wuce
Sun idar da sallar kenan Abba ya kira wayar Tahir.
Tahir na gani yace"To an fa gane baka gida."
Sadiq ya karb'i wayar yana fad'in"Ba ni zan dauka."
Ba musu ya mika masa shi ya amsa kiran.

Abba daman suna shashen Sadiq ne an turke Auwalu dole ya fadi gaskiya Umma ta kasa zaune tsaye itace daman ta fahimci Sadiq baya gidan tunda har ciki ta shiga bata gansa ba.
Daga karshe da Tambayoyi suka tashi kan Auwalu yace sun fita a mota tare da Tahir shine Abba ya kira Tahir shi daman su suka kirasa suka tadamai Hankali kada Innani da Umma su ji Labari.
Abba na jin an dauka yace"Attahiru kuna ina ne kai da Abubukar?
Sadiq yace"Ba shi ba ne, ni ne Abba."
Abba yace"Magajin gida lafiya? Ina kuka je?
Sadiq yace"Zariya Abba."
Abba ya maimaita"Zariya?
Da yasa gabadaya su Umma suka mike suna kallonsa gaban Umma na fad'i.

Dagacan bangaren Sadiq yace"Eh nazo na iske Hasiya na asibiti zata haihu, sai dai Mungode ma Allah tunda an yi mata C.s an ciro mata mazaje guda Biyu."
Abba ya washe baki cikin Fara'a yana fadin"Alhamdulillah masha Allah, ina ita uwar fata ta na lafiya?
Sadiq yace"Eh bata dai Farfado ba dai har yanzu muna asibitin tare da yan'uwanta."
Abba ya Shiga addu'ar Allah ya bata lafiya ya yara abunda aka samu.
Sannan suka yi sallama.
Abba na sauke wayar a kunnensa mama ta ce"wa ye kuma ya haihu Abban siyama?
Cikin Tsananin Farinciki yace"Matar Magajin gida ce ta sauka, aiki aka yi mata an ciro abokaina har guda Biyu."
Umma sai ta zaro ido, Mama kuma sai tace"Allah sarki.!
Innani kam sai kabbara cikin Dariya tace"Ni"imar Ubangiji da rahmarsa ya sauka a gidan magajin gida Allahu akbar"
Sai kuma ta kasa kuka tana fadin ashe tana raye zata gani. ita innani abunta kamar na yan juju ne nan Umma ta gayamata ta saka an koreta tace gwara da akayi haka ammh yanzu ance an sauka tace Rahma ta sauka a gidan magajin gida.
Umma mamaki ya hanata kara mgana kenan yarinyar nan sai da ta kara kusantar rayuwar Sadiq ita tana Tunanin ta rabasu ashe hakan ta bai cimma ruwa ba..kafin kace kwabo kowa yaji Sadiq ya samu karuwar yan Biyu.

Sultana da siyama da suka Dawo daga Jarabawa suka samu Labari. sai kishi da bakinciki ya turkuketa har da kuka Siyama kuma sai ta kama Murna tana son ganin yaran kuma ma yan Biyu masu ban sha'awa.
Surayya da ta samu Labari ta fi kowa murna daman kuma tasan girman cikin nan na Hasiya yafi guda d'aya.
Bata yi mamakin jin cewa Sadiq yana zariya ba, daman tasan matukar yana iya tafiya sai ya nemo Hasiya zuwa kuma wannan lokacin tasan yasan komai da ya faru.
Da wayar Tahir ta kirashi suka yi mgana da shi ta yi masa barka, bai yi mata wata mgana ba itama bata yi masa ba sun Rabu akan gobe zata zo in sha Allahu..shi kuma yace zasu kwana a Hotel zuwa da Safe tunda Hasiyar ta Farfado dazu bayan mangariba.
Ni dai kawai farkawa na yi na ganin a gadon asibiti acikin daki na musamman.
Nurse din da ke kaina ta shaidamin aiki aka yi min an ciromin yara Biyu duka maza.
Ba farincikina Haihuwanta na rika yi ba sai na ganin Assadiq a kaina yana rike da Hannuna.
Sai gashi ina hawaye ina fadin"Assadiq daman zan kara ganin ka?
Cikin mirmishi yace"Gashi kin gani, ai na taba fad'a miki ni da ke har Abada ne Siya."
Duk da dinkin jikina sai da na Rumgumesa ina kukan Farincikin sake ganinsa a Lokacin da na Fidda rai.
Ban taba ganin Tahir ya yi min Fara'a irin na yau ba, shi ya mikama min yaron d'aya Assadiq ya kwantar da daya a saman jikina.
Su Adda na gefe suna ta min mirmishi da barka da arziki.
Bansan Sadiq na tafiya da Sanda ba sai da ya mike cikin damuwa na kallesa ina fadin"Assadiq me ya samu kafar ? ita bata warke ba?.
Domin duk naga Tabon ciwukan kansa cikin mirmishi yace"Karayace a kafar ita bata karisa warkewa ba."
Sai gani hawayena na diga saman ya'yan dake zube a jikina.
Mirmishi ya yi min kafin ya Furta"Nagode Nagode sosai Siya, na yaba kuma ina Fatan Ubangiji kema ya yaba miki fiye da yadda ni na yaba miki."
Na kalli yan'uwana a zagaye dani abun Farincikina ganin Assadiq a kusa dani, na tuna a baya sanda na shiga cikin kunci saboda rashinsa.
Har nagama zamana a wajen Amma bata san abunda ya faru ba, saboda kada ta Fahimci wani abu yasa nace zan dawo wajen Adda kafin Assadiq ya Dawo.
Itama da na dawo ban gayamata komai ba, har kuma zuwan Maman suhailat ni nace kada ta sanar da su, hatta kawata Ramatu na Boye mata wannan sirrin Saboda ba na so su rika kallon Assadiq da wani Duba na Dabam.

Safiya kawar Amana ce bata tafi gida ba sai da taga farfad'owata na Tuna gajiya ta yi da kiran wayata a kashe taje gidana maman suhailat tace ina gidan yayata daman kuma mun taba zuwa tare sai gata tazo ganina, da ya ke mun koma makaranta a halin nauyin cikin nan da na ke ciki tara kani makaranta naje na karbo T.P LETTER d'ina ban dai samu na kai makarantar da zan yi Teaching pratice din ba Nagudan Tsaye Tsaye ya kamani, daman kowa na mamakin girman cikina sannan kuma ya wuce wattanin haihuwansa.
Kuma da na dawo naje asibiti suka Dubani sukace lolacin haihuwata bai yi ba, duk da cikin ya wuce wattaninsa ba su ga alamun mahaifa zata Bude ba.
Yadda gabadayansu suka zagaye gadon da ni ke kwance ne ya sakani kwalla, naji a raina ni Ubangiji ya gama mini komai tunda ya barni da Soyayyar yan'uwana tare da gwarzon miji irin Assadiq
Daman na sani ko  a jima ko a dad'e Assadiq zai zo ya neme ni shiyasa nima na kasa mantawa da shi acikin zuciyata.

*Janafty*
*TMWB3K012*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/K3rO5UonX4GDVxtQbA5mZl
PAID ADVERT✅

Assalamualaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu!!! Wannan group din dai na komai da komai ne. A taiqaice
*Farashin mu na daban ne compared to sauran Yan kasuwa
*Kaya masu kyau da quality. Abinda kika zaba shi za a Baki
* Swift delivery.watau waybill a sauqaqe da Yardar Allah
* Muna sake New Arrivals ka fin su cika Gari
* Muna iya duba maku kaya a good price ko da ba namu ba ne idan kuka Aiko da hoton kayan
Allah sa mu qaru da juna Ameen

Washegari Surayya da ta shirya tafiya Zariya sai da ta biya ta gida ta sanar da Abba zata je ta duba mejego da yara.
Jin haka yasa Abba yace Mama ta shirya sai su tafi tare da Surayya sannan yace nawa suke bukata wanda zasu iya rike ma maijegon wani abu?
Ita daman Surayya ta zo da kaya cike da leda su pamper din yara ne, sai Kayan sanyi masu kyau da mayukan setin na yara.
Sai sauran tarkace irin na kayan yara dai jariri, Jin Abunda Abba yace ne yasa tace ya bari wannan sai sun je sun dawo tukunnah.
Siyama ma jin da Mama Za'a tafi ganin Twins itama ta dauki damara tace sai taje daman da Tunanin yaran ta kwana a ranta, Innani kuma damam Tun jiya ta had'a kayanta tace ai magajin gida ya yi mata alkwarin ita zata yi ma Hasiya wankan jego saboda haka rana fa bata karya sai dai uwar diya taji kunya.
Shi kuma Abba yace a tafi da ita taga ya'yan magajin gida Umma kuma sai ta zama yar kallo Sajida ma tazo gidan gulma taga ko Surayya ba ta tsaya cewa tazo su tafi ba, ballatana Abba da ga ita har Umma sai ya yi kamar bai ma gansu ba, harda Sultana da ta damu kanta da bakin kishi Saboda Haihuwar Hasiyan.
Chapter 41 · 0% Book details