Sashe 40
Tmw Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Umma tafi kowa Farinciki da dawowar Sadiq gida ya ji sauki gida haka ya ke cika da yan'uwansa duk kuma a bangarensa ake zama Har Innani ta koma yini a bangarensa.
Shi dai baya mgana Sosai sai dai ya bisu da ido kawai kuma sai ma da ya dawo gida ya kara tabbatar da zarginsa.
Siya suka dorama alhakin duk abunda ya sameshi.
Abba ne ma daya dawo hayyacinsa a kwanakin baya ya yi ma Surayya mganar Hasiya ita kuma ba kwana kwana ta sanar da shi abunda Umma ta aikata da taimakon ya'yanta.
Abba ya shiga tashin hankali yace maza maza ta sake komawa Zariya ta tabbatar ta samu Hasiya domin taga Halin da ta ke ciki.
Ita kuma a ranar data shirya zata koma Zariya uwar mijinta ta rasu ba Halin tafiya kuma sai abun ya shafe a ranta gabadaya.
Shi Uban gayyar bai manta ba sai da ya yi kwana hud'u da dawowa gida sannan Tahir ya zo dubashi, kuma akaci sa'a Tahir yazo da mota kirar Camry, Motar uban gidansa ba ya kasar shine ya ke zirga zirgan shi da ita.
Yana zuwa Sadiq yace zai kai sa wani waje a motar don Allah, shi a tunanin Tahir nan kusa ne shiyasa bai ce a'a ba, Sadiq ya shirya cikin riga da wando na wani farin yadi, sai ya nannad'e kasan wando, saboda Kafarsa ta dama kuma Tahir yaga harda Hula ya saka baki sake yace"Wai ina zaka je ne?
Kai Tsaye Sadiq yace"Kai dai muje zaka ganin ma idanuwan ka"
Ba musu Tahir ya tashi suka tafi, kuma abunda Sadiq ya shirya ba wanda yasan ya fita ya riga ya gayama Auwalu duk wanda yazo dubashi yace yana ciki ya kwanta Malam Taju megadi Sadiq ya fad'a masa ko Abba kada yasan ya fita.
Sai da suka dauki hanya ne Tahir yace ina zamu je?
Sadiq yace"Zariya."
Tahir ya saki baki kafin yace"Ka yi me a Zariyan?
Kai Tsaye Sadiq yace"In yi me kuma? Ai kasan dai ina da wata matar acan."
Tahir sai ya kasa mgana duk da Big sis bata gayamasa komai ba ammh yasan akwai matsala kuma dai maganar gaskiya shi bai ganta ba, a ransa yace to Allah yasa ba rasuwa ta yi wajen haihuwa ba sai yaji a ransa yana fata da addu'an komai lafiya saboda yasan yadda Sadiq ke girmama waannan zabiyar matar tashi.
Sai ga su a Zariya har kofar gidan da Hasiya ke zaune cikin kuma sa'a suka ga Maman suhailat a waje an kawo mata sakon kaya daga kano.
Tana ganin Sadiq ta iso wajensu bakinta har kunne ta na Fad'in"Barka da arziki Abubakar Allah sarki daman nace in dai kana raye zaka tako kafarka wajen Hasiya."
Mirmishi kawai ya yi mata sai barka da arziki ta ke yi masa ganinsa da Sanda har tana kwallah.
Tun kafin ma ya yi mganar Hasiya maman suhailt na sharan kwallah ta kwashe duk abunda ya faru ta gayamasaa.
Cikin tashin hankali yace"Yanzu ina Siya ta ke?
Maman suhailat tace"Ta na gidan yayarta din nan fati, ba ta ma jima da dawowa ba da farko ta na wajen mahaifiyar tasu ne kasan yayar mahaifiyar ta su ce ta rasu kwanakin baya."
Har tana gayamai itama daga baya ta koma sai ta samu Hasiyar ta dawo nan cikin Tausayi tace"Abunda zai baka sha'awa da yarinyar nan duk abunda ya faru bata gayama yan'uwanta komai ba, cewa ta yi kayi tafiya baka gari ita kad'ai ce ta kunshi wannan bakincikin baiwar Allah.
Ai Sadiq bai gama sauraranta ba ya fad'a mota saboda bacin rai baya ma gani sosai.
Huci kawai ya ke yi, Tahir ma ya shiga ya tada motar Sadiq na nuna masa hanyar gidan, Tahir ganin yadda Sadiq ke huci yasa ya kallesa yana fad'in"Ka bi a sannu Sadiq ka san dai baka da lafiya ko?
Sadiq kamar ya yi kuka yace"Tahir wannan wani irin tozarci ne? Ni ne basa son ganin farincikina ai shikenan dama a hatsarin da na yi mutuwa na yi da kowa sai ya duka ya Dauka."
Da Sauri Tahir yace"Subhanallah kada Bacin rai yasa ka yi Sabo mana."
Sadiq bacin ransa da Maman Suhailat tace har Surayya ta zo kuma ta gayamata ammh shine ta yi masa karya.
Ba dad'ewa sai ga su a kofar gidan Adda Fati Tahir ne ya buga sallama shi kuma Sadiq na gefe rike da sanduna zuciyarsa na faman Bugawa.
Mijin Adda Fati ne ya fito ganin Mijin Hasiya yasa ya fito da sauri sun gaisa sama sama shi da tambayan garin yaya ya samu rauni a bakinsa shima Sadiq a bakinsa da tambayar ina Hasiya?
Mijin Adda Fati ya yi ajiyar rai kafin yace"Suna asibiti da Hasiyar tun safe ta fara zubar da jini, ammh yanzu Yayarta ta kirani tace C.s Za su yi mata yanzu nan."
Sadiq ya ji kamar ya zura a guje saboda Tashin hankali cikin Sauri da rawan baki yace"Wani asibiti ne?
Yace"Kamar inda ta ke awo tace na manta sunan asibitin."
Sadiq ya juya da sauri yana ce ma tahir yasan asibitin su tafi kawai.
Sai mijin Adda Fati yace shima daman can zai je, kawai sai suka rankaya gabadaya.
Suna tafe Habibu mijin Adda na basu Labarin irin wahalar da Hasiya ta sha, tafi sati daya ta na nakudar tsaye sai yau da safe ne ta fara zubar da jini yasa suka tafi asibiti da Sauri ashe ma haihuwar ta ki Sai an yi mata aiki.
Asibitin musulmi ne, suna zuwa Habibu ya kira Adda Fati sai gashi ta fito Yarkace yarkace fuska duk ta kod'e Saboda kuka da Damuwa.
Itama sai da ta bude baki ganin Sadiq cikin damuwa tace"Abubakar ashe ka dawo? Subhanallah ba dai a wajen aikin ne ka samu raunika haka ba?
Sai ya ma kasa yi mata mgana yana jin wani abu na shiga ransa.
Ya kalli Tahir shima ya kallesa karshe dai Tahir aka bari da fadin"Eh a can ne ya samu d'an hatsari kad'an".
Ta bishi da Allah ya kara lafiya suna tafe ta na fad'amai daman saka hannun mijinta ake jira ko na wani makusancinta zasu shiga da ita tiyata sun ce yan Biyu ne acikinta.
Akwai bukatar gaggawa ceto Rayuwarta da na abunda ke Cikinta.
Shiyasa bata lokaci suna zuwa Adda Fati tace ga mijinta nan Sadiq ya Rattafa hannu aka shiga da Hasiya Tiyata, Sannan kudin Tiyatar ma shi ya Biya bai zo da ko Atm dinsa ba tunda shi babu komai ma a hannunsa Tahir ya ara masa kudin hannunsa ya Biya da shi.
Tare suka yi zaman jugum jugum a asibitin nan shi da Tahir da Adda Fati tare da Adda Rukayya, sai Habiba da Ramatu mijin Adda Fati Shi kuma ya tafi daga baya, sannan Safiya tazo daga baya sai kuma yar'uwata Sister Zainab da ke aiki a asibitin.
Sadiq ya yi kwallar Tausayin Hasiya ciki har wajen wata sha daya yana jikinta bata haifeshi ba sai yanzu ga nauyin jiki ga na zuciya ga na lulura ga tashin hankali ammh ko alama bata zaunar da wani cikin yan'uwanta ta b'ata shi ko danginsa a wajensu ba, sai yaji matsayin da Siya ke da shi a baya yanzu ta na Hau hau sama da matsayinta na baya acikin zuciyarsa.
Kimanin awa uku sannan aka Samu nasaran fito da Ya'ya biyu duka maza acikin Hasiya yan biyu kosassu masu lafiya wad'anda ke kama sak da mahaifinsu sai dai Farar Fatar Hasiya kad'ai suka dauko.
Ita kuma ba ta farfado ba an kaita dakin Hutu.
Sadiq na gefe yana yi ma Allah kirari da godiya.
Tahir ya amshi yaron bayan su Adda sun gama ganinsu suna hamdala.
Adda Fati ta yi gefe ta kira Amma tana gayamata an yi ma Hasiya aiki an ciro mata yara maza guda biyu.
Amma sai farinciki da hamdala kuma daman ba su gayamata Hasiyar na naguda ba, kada su tada mata hankali.
Kamar Amma na wajen tace"Allah Sarki Ina shi megidan nata ya dawo kuwa?
Adda Fati tace"Ya zo a kan gaba Amma, shima ashe achan in da suke aiki hatsari ya samu."
Amma ta yi ta salati nan tace a bashi wayar shi kuma Lokacun yana gefen Tahir da ke nuna masa yaran shima bakinsa har kunne.
Adda ta mika masa waya tace ga Amma cikin ladabi ya karb'a ya gaisheta lokaci d'aya yana yi mata gaisuwan Adda Tunda Maman suhailat tace yayar mahaifiyarsu yasan Adda ce tunda shi dai ita kad'ai ya sani."
Amma ta amsa masa, itama ta yi masa jaje tare da barka da arziki sannan suka yi sallama ya mikama Adda Fati wayar.